Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-10-30 11:03:13    
Taron koli na birnin Beijing kuma taron ministoci a karo na 3 na dandalin tattaunawa kan hadin gwiwa tsakanin Sin da kasashen Afirka

cri

An gudanar da taron koli na birnin Beijing kuma taron ministoci a karo na 3 na dandalin tattaunawa kan hadin gwiwa tsakanin Sin da kasashen Afirka daga ranar 3 zuwa 5 ga watan Nuwamba na shekarar 2006 a birnin Beijing. Wannan taron koli shi ne irinsa mafi girma da shugabannin kasashen Afirka mafi yawa suka halarta a cikin tarihin dangantakar diplomasiyya tsakanin Sin da kasashen Afirka, wanda ya kai sabon matsayi a fannin dangantakarsu.

Shugaban kasar Sin Hu Jintao, da shugabanni da kusoshin gwamnatocin kasashen Afirka 48 ciki har da firayin ministan kasar Habasha dake jagorancin dandanlin Meles Zenawi, da kuma wakilan kungiyoyin duniya sun halarci taron kolin, inda aka zartas da shirin aikin Beijing daga shekarar 2007 zuwa 2009 na dandalin, kuma shirin ya bayyana abubuwan da aka tanada a cikin aikin hadin gwiwa tsakanin Sin da kasashen Afirka a fannonin siyasa da tattalin arziki da zamantakewar al'umma a shekaru 3 masu zuwa, wanda ya bayyana tunanin yin hadin gwiwa tsakanin bangarorin biyu don samun moriyar juna da bunkasuwa tare. A yayin taron kolin, an zartas da sanarwar taron kolin Beijing na dandalin tattaunawa kan hadin gwiwa tsakanin Sin da kasashen Afirka, wannan ya bayyana cewa, an kafa sabuwar dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare tsakanin su ta hanyar fitar da takardun siyasa.

A gun taron kolin, shugabannin Sin da kasashen Afirka sun waiwayi hadin gwiwar abokantaka tsakaninsu a cikin shekaru 50 da suka wuce, da nasarorin da aka samu bayan shekaru 6 da aka kafa dandalin tattaunawar a karkashin taken "zumunci da zaman lafiya da hadin gwiwa da kuma bunkasuwa", kana sun yi shawarwari kan yadda za a raya dangantakarsu da inganta hadin gwiwa tsakanin kasashe masu tasowa da kuma kafa sabon tsarin harkokin siyasa da tattalin arziki na duniya da dai sauran batutuwa, kuma sun cimma daidaito game da wadannan batutuwa, da tabbatar da raya sabuwar dangantakar abokantaka tsakaninsu ta samun fahimtar juna a fannin siyasa, da samun moriyar juna a tsarin tattalin arziki, da kuma yin mu'amala a fannin al'adu.

Don raya sabuwar dangantakar abokantaka tsakanin Sin da kasashen Afirka, da kara hadin gwiwa tsakaninsu a dukkan fannoni, shugaban kasar Sin Hu Jintao ya sanar da matakai 8 a gun taron kolin, ciki har da yawan gudummawar da Sin ta baiwa kasashen Afirka a shekarar 2009 ya ninka sau daya idan aka kwatanta shi da shekarar 2006, da soke basussukan da kasar Sin take bin kasashen Afirka wadanda suke da dangantakar diplomasiyya da Sin da suke cin basussuka masu tarin yawa, da suke fama da talauci kwarai, da kafa asusun raya kasar Sin da kasashen Afirka, da kuma horar da gwanaye da dai sauransu.

Ban da wannan, a yayin taron kolin, gwamnatoci da masana'antun kasashen Afirka da kamfanonin Sin 11 sun daddale yarjeniyoyi 14 a fannonin aikin gona da ma'adinai da makamashi da ruwa da gine-gine da zirga-zirga da dai sauransu, wadanda yawansu ya kai dala biliyan 1.9, kana an sanar da kafa kungiyar hadin gwiwa kan masana'antu da harkokin ciniki tsakanin Sin da kasashen Afirka.(Zainab)