Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-10-29 15:01:23    
Dandalin tattaunawa kan hadin kai a tsakanin Sin da Afirka

cri

Bayan an shiga karni na 21, batutuwan kiyaye zaman lafiya da neman samun zaman karko da sa kaimi ga bunkasuwa sun zama burorin jama'ar kasashen duniya. Domin ci gaba da inganta hadin gwiwa a tsakanin Sin da Afirka, da tinkarar kalubale da tsarin raya tattalin arzikin duniya bai daya ya kawo, da sa kaimi ga bunkasuwa tare, bisa shawarar da wasu kasashen Afirka suka bayar, a watan Oktoba na shekarar 1999, gwamnatin kasar Sin ta gabatar da shawara kan gudanar da taron ministoci na dandalin tattaunawa kan hadin kai a tsakanin Sin da Afirka da aka shirya a birnin Beijing a shekarar 2000. Kuma wannan shawara ta samu goyon baya da kasashen Afirka suka bayar.

Bisa kokarin da Sin da kasashen Afirka suka yi, a watan Oktoba na shekarar 2000, a birnin Beijing, an yi taron ministoci na dandalin tattaunawa kan hadin kai a karo na farko a tsakanin Sin da Afirka, a wajen taron, an zartas da "sanarwar Beijing ta dandalin tattaunawa kan hadin kai a tsakanin Sin da Afirka" da "tsarin yin hadin gwiwa wajen bunkasuwar tattalin arziki na Sin da Afirka". Bisa tsarin da aka zartas, bangarori biyu sun yarda da kafa tsarin yin mu'amala a tsakanin matakai daban daban. A watan Yuli na shekarar 2001, a babban birnin kasar Zambia wato Lusaka an gudanar da taron shawarwari bayan dadalin tattaunawa kan hadin kai a tsakanin Sin da Afirka. Inda aka zartas da "shirin tsarin gudanar da ayyukan bayan dandalin tattaunawa kan hadin kai a tsakanin Sin da Afirka", a cikin shirin, an yanke shawarar kafa tsarin gudanar da ayyukan bayan dandalin tattaunawa kan hadin kai a tsakanin Sin da Afirka a kan matakai 3, wato za a gudanar da taron ministoci sau daya bayan shekaru 3, kuma za a yi taron manyan jami'an kasashen Afirka da Sin sau biyu wato kafin shekara daya da kuma kafin 'yan kwanakin da aka gudanar da taron ministoci, don yin sharen fage ga taron ministoci, kuma jakadun kasashen Afirka da ke kasar Sin da sashen sakatariya na kwamitin gudanar da ayyukan bayan dandalin tattaunawa kan hadin kai a tsakanin Sin da Afirka za su gudanar da taro bisa kayadadden lokaci. Kuma za a gudanar da taron minitoci da taron jami'ai a Sin da kasashen Afirka bi da bi.

Dandalin tattaunawa kan hadin kai a tsakanin Sin da Afirka shi ne dandalin yin shawarwari a tsakanin Sin da kasashen Afirka, kuma shi ne tsarin yin hadin gwiwa a tsakanin kasashe masu tasowa. Halin musamman na dandalin tattaunawa kan hadin kai a tsakanin Sin da Afirka shi ne kara yin takamammen hadin gwiwa bisa manufar kara yin shawarwari da hadin gwiwa, da yin zama daidai wa daida domin cin moriyar juna, wato yin shawarwarin siyasa da hadin gwiwar tattalin arziki da ciniki tare bisa manufar sa kaimi ga bunkasuwar juna.(Abubakar)