Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-10-29 10:38:36    
Bayani kan taron ministoci na karo na farko da na biyu na dandalin tattaunawa kan hadin gwiwa a tsakanin Sin da Afrika

cri
Sakamakon kokarin aiki da Sin da Afrika suka yi, ya zuwa yanzu, an riga an yi taron ministoci sau uku na dandalin tattaunawa kan hadin gwiwa a tsakanin Sin da Afrika.

Daga ran 10 zuwa ran 12 ga watan Oktoba na shekarar 2000, a birnin Beijing, an yi taron ministoci karo na farko na dandalin tattaunawa kan hadin gwiwa a tsakanin Sin da Afrika. Bisa manufar yin shawarwari cikin daidaito, da kara samun ra'ayin daya, da kara fahimtar juna, da kuma karfafa zumunci, kana da ingiza hadin gwiwa a tsakaninsu, an yi tattaunawa kan batutuwa biyu wato yadda za a sa kaimi kan kafa sabuwar odar siyasa da tattalin arziki ta duniya a karni 21, ta yadda za a karfafa hadin kan tattalin arziki da ciniki a tsakanin Sin da Afrika yayin da ake cikin sabon hali. Kuma a yayin taron, an zartas da "sanarwar Beijing ta dandalin tattaunawa kan hadin gwiwa a tsakanin Sin da Afrika" da "tsarin ka'idoji na yin hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka wajen bunkasuwar tattalin arziki da zaman al'ummar kasa" wadanda suka tabbatar da alkibla wajen bunkasa dangantakar abokantaka ta sabon salo cikin dogon lokaci kuma cikin daidaito da kawo moriyar juna dake tsakanin Sin da Afrika. Ban da haka kuma, yayin da aka yi taron ministoci na wannan karo, an yi taron nazari har sau hudu, wadanda suka shafi batun zuba jari da yin cinikayya a Sin da Afrika, da yin musanyar ra'ayoyi kan babban ci gaba da aka samu a Sin da kasashen Afrika wajen yin kwaskwarima, da kuma kawar da talauci da samun dauwamamman ci gaba a fannin noma, kana da yin hadin gwiwa a fannonin ba da ilimi da kimiyya da fasaha da kuma kiwon lafiya da dai sauransu.

Bisa "tsarin ka'idoji na yin hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka wajen bunkasuwar tattalin arziki da zaman al'ummar kasa", bangarorin biyu sun amince da kafa tsarin gudanar da ayyuka bayan dandalin tattaunawar a mataki daban daban na bangarorin biyu.

Bisa tsarin gudanar da ayyuka bayan dandalin tattaunawar, daga ran 15 zuwa ran 16 ga watan Disamba na shekarar 2003, a Addis Ababa, babban birnin kasar Habasha, an yi taron ministoci karo na biyu na dandalin tattaunawa kan hadin gwiwa a tsakanin Sin da Afrika. Jigon taron shi ne "Yin kokarin hadin gwiwa", kuma a gun taron, an yi tattaunawa kan sabuwar hanya da sabon matakin da za a dauka a nan gaba wajen zurfafa hadin gwiwa a tsakanin Sin da Afrika a muhimman fannoni kamar su horar da gwanaye, da aikin noma, da gina manyan ayyuka, da kuma zuba jari da yin ciniki da dai sauransu. Wakilan da suka halarci taron sun waiwayi aikin gudanarwar "sanarwar Beijing ta dandalin tattaunawa kan hadin gwiwa a tsakanin Sin da Afrika" da "tsarin ka'idoji na yin hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka wajen bunkasuwar tattalin arziki da zaman al'ummar kasa" da aka zartas a gun taron ministoci karo na farko na dandalin tattaunawa kan hadin gwiwa a tsakanin Sin da Afrika a shekarar 2000. Kuma a gun taron, an zartas da shirin aikatawa na Addis Ababa na dandalin tattaunawa kan hadin gwiwa dake tsakanin Sin da Afrika (daga shekarar 2004 zuwa ta 2006) wanda ya tsara shirin yin hadin gwiwa a tsakanin Sin da Afrika a cikin shekaru uku masu zuwa. Ban da wannan kuma, a yayin taron, an yi taron masu masana'antun kasashen Sin da Afrika a karo na farko, inda masu masana'antu fiye da dari biyar suka halarta kuma suka yi shawarwari kan harkokin kasuwanci, kana suka kulla yarjejeniyar hadin gwiwa guda 21 wadda kudin da aka tanada ya kai dala biliyan daya.(Asabe)