Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-10-21 21:48:10    
Shugabannin Sin da Amurka sun sake nuna ra'ayi daya kan matsalar sauyawar yanayi tsakaninsu

cri
A ranar 21 ga wata, shugaban kasar Sin Mr. Hu Jintao ya buga waya ga takwaransa na kasar Amurka Barack Obama, inda suka yi musayar ra'ayi kan dangantakar bangarorin biyu da matsalar sauyawar yanayi tsakaninsu. Wannan shi ne karo na farko da shugabannin kasashen biyu suka sake samun ra'ayi iri daya tsakaninsu, bayan taron koli na M.D.D da aka yi kan matsalar sauyawar yanayi ta duniya a watan jiya.

Mr. Hu ya bayyana cewa, taron da za a yi a watan Disamba na bana a birnin Copenhagen zai kasance wani muhimmin taro ne da kasashen duniya za su yi game da matsalar sauyawar yanayi ta duniya. Ko da yake yanzu, akwai matsaloli da dama da ya kamata a yi kokarin warware su ta hanyar yin shawarwari, amma idan bangarorin da abin ya shafa suka iya hadin gwiwa tare, za a iya samun sakamako mai kyau a gun taron, amma kamata ya yi a yi taron bisa yarjejeniya kan matsalar sauyawar yanayi ta M.D.D da yarjejeniyar Kyoto, da kiyaye sakamakon da aka samu a yayin shawarwarin Bali.

Hu Jintao ya jaddada cewa, kasashen Sin da Amurka na fuskanatar matsaloli tare a kan matsalar sauyawar yanayi, kuma bangarorin biyu na samun moriyar juna. Sin na fatan inganta mu'amala da shawarwari da yin hadin gwiwa, da ci gaba da daukar kwararran matakai tare da bangarorin da abin ya shafa ciki har da Amurka don kokarta samun sakamako mai kyau a yayin taron Copenhagen, da warware matsalar sauyawar yanayi tare, don kara ba da gudummawa wajen sa kaimi ga samun bunkasuwar duniya cikin dogon lokaci.

Obama ya ce, game da taron Copenhagen da za a yi nan ba da dadewa ba, Amurka tana fatan hada kai tare da bangarorin da abin ya shafa don tabbatar da samun sakamako mai kyau a yayin taron. Kasashen Amurka da Sin sun dauki kwararran matakai don warware rikicin kudi na duniya. Ya kamata bangarorin biyu su hada kai tare, don tabbatar da yiwuwar taron Copenhagen da ganin an fitar da matakai masu ma'ana wajen warware kalubalen da za a iya fuskanta game da matsalar sauyawar yanayi, don cimma nasara a taron.(Bako)