Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-10-21 20:43:37    
Bunkasuwar tattalin arziki da zaman al'ummar kasar Sin sun shiga yanayi na fara murmurewa, in ji Wen Jiabao

cri

Firayin ministan kasar Sin Mr. Wen Jiabao ya shugabanci wani taro na majalisar gudanarwa ta kasar Sin a ran 21 ga wata a birnin Beijing, domin tattaunawa kan yanayin tattalin arziki da ake ciki, inda ya jaddada cewa, bunkasuwar tattalin arziki da zaman al'ummar kasar Sin tana cikin wani muhimmin yanayi na fara murmurewa a halin yanzu.

Taron ya ce, a cikin farkon watanni 9 na shekarar da muke ciki, bunkasuwar tattalin arziki da zaman al'umma ta kasar Sin ta fi kyau fiye da yadda aka yi tsammani a farkon shekarar bana, haka kuma an inganta yanayin ta yadda aka fara samun murmurewa. Amma ana fuskantar wasu wahalhalu da matsaloli. A cikin karshen watanni uku na wannan shekara, ya kamata a kula da dangantaka yadda ya kamata a fannoni uku, wato kiyaye samun bunkasuwar tattalin arziki cikin sauri, da yin gyare gyare kan tsarin tattalin arziki, da kuma hana hauhawar farashin kaya da za ta iya yiyuwa. Taron ya ci gaba da cewa, ya kamata a ci gaba da gudanar da kyawawan manufofin kudi, da kiyaye manufofin da ake tafiyarwa a halin yanzu, ta yadda za a iya kafa wani tushe mai kyau ga aikin raya tatttalin arziki da zaman al'umma a shekara mai zuwa.(Danladi)