Ranar 20 ga wata, a nan birnin Beijing, babban magatakardan kungiyar kula da harkokin hadin-gwiwa ta fannin masana'antu ta kasar Sin Mista Zheng Boliang ya bayyana cewa, za'a kaddamar da "dandalin tattaunawa kan neman bunkasuwa da hadin-gwiwar Sin da Afirka ta fannin masana'antu na shekara ta 2009" a ranar 21 ga watan Nuwamba a nan birnin Beijing, lamarin da zai samar da wani sabon dandali ga hadin-gwiwar Sin da Afirka ta fannonin tattalin arziki da cinikayya.
Mista Zheng ya ce, makasudin shirya wannan dandalin tattaunawa shi ne, a ci gaba da inganta dangantakar abokantaka ta hadin-gwiwa bisa manyan tsare-tsare tsakanin Sin da Afirka, da karfafa hadin-gwiwar bangarorin biyu wajen zuba jari da yin mu'amala ta fannin masana'antu.
Bisa labarin da muka samu, an ce, babban taken dandalin tattaunawa a wannan gami shi ne, "nuna amincewar juna da neman cimma moriyar juna", haka kuma dandalin tattaunawar zai samu halartar ministocin masana'antu da wakilan kamfanoni daban-daban da zasu zo daga kasashen Afirka sama da 40.(Murtala)
|