Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-10-19 21:20:16    
An shirya taron share fage ga taron shugabanni na musamman na kungiyar AU kan batun 'yan gudun hijira

cri

An shirya taron share fage ga taron shugabanni na musamman na kungiyar tarayyar Afirka wato AU kan batun 'yan gudun hijira a ran 19 ga wata a birnin Kampala, babban birnin kasar Uganda. Firayin ministan kasar Mr. Apollo Robin Nsibambi ya bayyana a gun bikin bude taron cewa, taron shugabanni na kungiyar AU da za a shirya a nan gaba ba da dadewa ba zai dukufa wajen kafa wani tsari na dogon lokaci domin kare da taimakawa 'yan gudun hijira na kasashen Afirka.

Mr. Apollo Robin Nsibambi ya fadi cewa, nahiyar Afirka ta fi samun 'yan gudun hijira a duk duniya, sakamakon haka, ko za a iya kafa wani tsari mai amfani wajen kare 'yan gudun hijira, da samun wata kyakkyawar hanya da ake bi wajen rage yawan 'yan gudun hijira ko a'a yana da muhimmiyar ma'ana ga samun zaman lumana da bunkasuwa a kasashen Afirka. A gun wannan taron shugabanni na musamman, za a daddale yarjejeniyar kare da taimakawa 'yan gudun hijira na Afirka, ta yadda za a iya samun fatan alheri da kara hada kai a tsakanin kasa da kasa domin daidaita matsalar 'yan gudun hijira a nahiyar Afirka.(Danladi)