Bisa labarin da muka samu daga hukumar da ke kula da kayayyakin tarihi ta jihar Tibet mai ikon tafiyar da harkokin kanta, an ce, jihar Tibet tana da hukumomin musamman 17 bisa matakai daban daban da ke kula da kayayyakin tarihi, ma'aikatan hukumomin sun kai kusan 300, sakamakon haka, jihar Tibet ta riga ta kafa wani tsarin kula da kayayyakin tarihi mai cikakke, da ke iya gudanar da ayyuka daban daban dangane da kayayyakin tarihi, da kuma yake da kwararru bisa wani babban mataki.
Jihar Tibet jiha ce da ke da albarkatun kayayyakin tarihi masu yawa a kasar Sin. Yawan wuraren tarihi da aka yi rajista a jihar Tibet ya zarce 3400, albarkatun kayayyakin tarihi ba kawai sun sa kaimi ga bunkasuwar tattalin arziki na yawon shakatawa a Tibet ba, har ma sun bayar da tsauraran bukatu ga ayyukan kare kayayyakin tarihi.(Danladi)
|