Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-10-18 17:26:11    
An yaba wa aikace-aikacen da kasar Sin ta gudana bisa matsayin babbar bakuwa a bikin baje kolin littattafan kasashen duniya a birnin Frankfurt

cri

A ran 17 ga wata, kwamitin da ke kula da aikace-aikacen da kasar Sin take gudanarwa bisa matsayin babbar bakuwa a bikin baje kolin littattafan kasashen duniya a birnin Frankfurt na shekarar 2009 ya shirya taron manema labarai wato taron rufewa, inda aka sanar da aikace-aikacen da kasar ta gudana a wannan bikin baje koli.

Darekta mai kula da harkokin yin mu'amala da hadin kai da kasashen waje na babbar hukuma mai kula da madaba'a da watsa labarai ta kasar Sin Mr. Zhang Fuhai ya gabatar a gun taron cewa, adadin aikace-aikacen da kasar Sin ta gudanar bisa matsayin babbar bakuwa zai zarce 620. kamfanonin kasar Sin da yawansu ya kai 225 sun shiga bikin baje koli, ya zuwa ranar 16, an daddale kwangiloli 1310 na fitar da ikon mallakar dabi zuwa kasashen waje, da kwangiloli 883 na shigar ikon mallakar dabi zuwa kasar Sin. Ana kyautata zaton cewa, yawan kwangilolin zai karu a yayin da za a rufe bikin baje koli.

Kwararren da ya zo daga kamfanin da ke kula da dangantaka da ke tsakanin bangarori daban daban na al'umma na WBCO na kasar Jamus, wanda ya taimakawa kasar Sin wajen shirya aikace aikace Mr. Frank Wollstein ya bayyana a gun taron cewa, kasar Sin ta gudanar da wani kyakkyawan aiki a wannan bikin baje koli, sakamakon haka kafofin watsa labaru daban daban sun buga labarai da yawa dangane da kasar Sin.(Danladi)