Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-10-14 07:29:10    
'Dan wasan kwallon kafa daga kasar Belarus Vyacheslav Slava Hleb yana yin wasa a kasar Sin

cri

Kamar yadda kuka sani, yanzu, a kasar Sin, an riga an kafa manyan gasannin sana'a ta wasannin kwallon kwando da kwallon tebur da kwallon kafa da sauransu. Duk wadannan gasanni suna kawo babban tasiri a duk fadin duniya, a sanadin haka, bi da bi ne fitattun 'yan wasa da yawan gaske suka zo kasar Sin daga wurare daban daban na kasashen ketare domin buga wasa. Wadannan shahararrun 'yan wasa suna ba da gudumawarsu wajen daga matsayin wasannin kasar Sin, kuma sun kara daukan hankulan masu sha'awar wasanni na kasar Sin.

Babbar hadaddiyar gasar wasan kwallon kafa ta kasar Sin tana daya daga cikin manyan gasannin sana'a na matsayin koli a shiyyar Asiya, shi ya sa wasu shahararrun 'yan wasa taurari su ma sun zo kasar Sin domin shiga wannan gasa. A cikin shirinmu na yau, bari mu yi muku bayani kan wani 'dan wasa daga kasar Belarus wanda ke buga wasa a kulob din wasan kwallon kafa na Shenghua na birnin Shanghai, sunansa shi ne Vyacheslav Slava Hleb.

Vyacheslav Slava Hleb shi ne kanen shahararren 'dan wasa Aliaksandr Helb, a shekarar 2000, su biyu sun shiga kulob din Stuttgart na kasar Jamus tare, daga baya, a kai a kai ne Aliaksandr Helb ya fi kanensa samun ci gaba wajen fasaha, kuma ya je kulob din Arsenal wanda ya fi karfi a duniya, ya shahara a duniya. Amma abun bakin ciki shi ne Vyacheslav Slava Hleb bai samu karbuwa yadda ya kamata ba. Ya zuwa shekarar 2005, ya komo garinsa, ya yi kokari ya buga wasa a birnin Minsk, daga baya ya ci nasarar zama fitaccen 'dan wasa a kasar Belarus, a sanadin haka, ya jawo hankalin kulob din wasan kwallon kafa na kasar Sin.

Tun farkon shekarar 2008, rikicin kudi mai tsanani ya kawo babban tasiri ga kasashen duniya, manyan gasannin sana'a na kasashen Turai sun gamu da matsalar karancin kudi. Amma a shiyyar gabashin Asiya, musamman ma a kasar Sin, ba haka yake ba. Babbar hadaddiyar gasar wasan kwallon kafa ta kasar Sin wadda ke da isashen kudi tana jawo hankulan wasu 'yan wasan kasashen Turai. Vyacheslav Slava Hleb shi ne daya daga cikinsu. A watan Maris na bana wato shekarar 2009, Vyacheslav Slava Hleb ya sauka a birnin Shanghai ya fara buga wasa a kulob din wasan kwallon kafa na Shenghua. Vyacheslav Slava Hleb ya gaya mana cewa,  "Da, idan an gayyace ni zuwa kasar Sin domin buga wasa a nan, ba zai yiwu ba gare ni ko kadan. Amma yanzu, kome ya canja, kasar Sin ta kara mai da hankali kan bunkasuwar wasan kwallon kafa, amma kasashen Turai suna fama da rikicin kudi. Ban da wannan kuma, ina kaunar birnin Shanghai sosai."

Kawo yanzu, Vyacheslav Slava Hleb ya riga ya zama muhimmin 'dan wasa a kulob din Shenghua. Game da babbar hadaddiyar gasar wasan kwallon kafa ta kasar Sin, Vyacheslav Slava Hleb ya kyautata tunani da cewa, koda yake matsayin wannan babbar gasa bai kai koli a duniya ba, amma kowane 'dan wasa yana yin matukar kokari, ana iya cewar, wannan babbar gasa tana da makoma mai haske. Ya ce,  "In an kwatanta wasan kwallon kafa na kasar Sin da na kasashen Turai, to, akwai banbanci, wasan kwallon kafa na kasar Sin ya fi mai da hankali kan karfi da karawa, dukkan kungiyoyin wasan kwallon kafa na kasar Sin suna sanya matukar kokari a yayin gasa, kuma matsayinsu ya yi kama da juna."

A sansanin horaswa na kulob din Shenghua a birnin Shanghai, a ko da yaushe, Vyacheslav Slava Hleb yana yin kokari. Abu mai sha'awa shi ne a yanzu ba ya jin sinanci ko kadan, shi ya sa yana bukatar taimakon mai fassarawa. Amma yana iya yin hira da wani aboki a kungiyarsa wato Yanko Valkanov wanda ya shiga kulob din Shenghua daga kasar Bulgaria da harshen Rashanci, su kan yi musayar ra'ayi kan wasa.

Vyacheslav Slava Hleb ya gaya mana cewa, yanzu, koda yake shi da wansa Aliaksandr Helb ba su zama a birni daya ba, amma su kan buga waya da juna domin gaisuwa. Vyacheslav Slava Hleb ya ce,  "Na kan buga waya ga wana, mun yi hira ta waya, amma ba kowace rana ba, sai sau daya a duk kwanaki biyu, shi ma ya kan buga mini waya."

Abun farin ciki shi ne matar Hleb ta zo birnin Shanghai tare da shi, sun yi aure ba da dadewa ba. Kowace rana, bayan wasa, Hleb ya yi saurin komawa gida domin cin abincin dare tare da matarsa. Hleb yana jin dadin irin wannan zaman rayuwa a birnin Shanghai, ya yi mana bayani cewa,  "Kulob din Shenghua na birnin Shanghai ya sama mini da sharadi da hidima masu inganci, ina jin dadi a nan, kamar kowa ya sani, birnin Shanghai birni ne mai wadata, kuma yana da kyan gani. Yanzu matata ta zo kasar Sin tare da ni, ita ma tana kaunar birnin Shanghai. Idan na yi hutu, kullum mu kan je yawo a lambun shan iska, muna jin dadi."

A gidan Hleb, mun tarar da kayayyaki biyu masu ban sha'awa, daya daga cikinsu shi ne karamin mutum mutumin da aka sassaka da tukwane, da wani hoton panda da matar Hleb ta zana. Hleb ya gaya mana cewa, ya sayi karamin mutum mutumin da aka sassaka da tukwane a birnin Xi'an na lardin Shanxi ne yayin da ya buga wasa a can. Game da hoton panda kuma, matarsa ta gaya mana cewa, tana son panda kwarai, amma ba ta iya zana hoto sosai ba. A hakika dai, hoton panda yana da kyan gani.

Kamar yadda kuka sani, a birnin Shanghai, masu sha'awar wasan kwallon kafa suna da yawan gaske, kuma a shekarar gasa ta shekarar 2008 ta babbar hadaddiyar gasar wasan kwallon kafa ta kasar Sin, kulob din Shenghua ta zama lambatu. A yayin wannan shekarar gasar, Hleb yana fatan za su zama zakaran wannan babbar gasa bayan kokarin da yake yi tare da abokan wasansa na kulob din Shenghua, kuma za su kawo wa masu sha'awar wasan kwallon kafa na birnin Shanghai kofin zinari mai daraja. Vyacheslav Slava Hleb ya ce,  "A cibiyar birnin Shanghai, ko a kantuna, masu sha'awar wasan kwallon kafa su kan kira sunana da babbar murya, su kan kira 'Hleb', 'Hleb', ina jin dadin haka."

Vyacheslav Slava Hleb ya karfafa magana cewa, lallai yana kaunar kasar Sin yana kaunar birnin Shanghai, kuma yana jin dadin kaunar masu sha'awar wasan kwallon kafa. (Jamila Zhou)