Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-10-13 18:35:02    
Bayani game da Zemedkun Asfawkun, wani ma'aikacin kamfanin CGCOC a kasar Habasha

cri
A cikin shirinmu na yau, za mu gabatar muku da wani bayani kan yadda Zemedkun Asfawkun wani dan kasar Habasha, kuma wani ma'aikacin kamfanin CGCOC yake aiki a wata masana'antar samar da gilas ta Hansheng wadda kamfanin CGCOC ya zuba jari ya kafa a kasar Habasha.

Malam Asfawkun ya taba yin karatu a nan kasar Sin har na tsawon shekaru 5, kuma ya taba yin aiki a kasar Sin na tsawon shekara 1. Sakamakon haka, ya iya Sinanci sosai, kuma yana son kasar Sin kwarai. Bayan da ya koma kasar Habasha, ya taba yin aiki a wata hukumar gwamati, kuma ya samu cigaba sosai. Amma me ya sa ya bar gurbinsa a hukumar gwamnati, kuma ya shiga wannan masana'antar kamfanin CGCOC? Malam Asfawkun ya gaya wa wakilanmu cikin harshen Sinanci cewar, "Ina farin ciki sosai domin na shiga wannan kamfani. A da, ina aiki a wata hukumar gwamnatinmu, kuma na samu wani muhimmin mukami. Bayan da na shiga wannan kamfani na kasar Sin, ina farin ciki kwarai. Sabo da wannan kamfani yana da ma'anar musamman ga kasar Habasha. Kun sani, ban da kasashen Masar da Afirka ta kudu, a sauran kasashen gabashin Afirka da na tsakiyar Afirka, babu masana'antar samar da gilas. Amma yanzu an kafa ta a kasar Habasha. Ina farin ciki kwarai da gaske, wannan shi ne kamfanin samar da gilas na farko, kuma wanda ya fi girma a kasarmu."

Kamar yadda malam Asfawkun ya fadi, a da, babu masana'antar samar da gilas. Sakamakon haka, sana'ar gine-gine ta kasar Habasha ba ta iya samun bunkasa kamar yadda ake fata ba. Bisa taimakon da asusun raya kasashen Afirka da kasar Sin ta kafa ya bayar, kamfanin CGCOC ya zabi wannan dama ya zuba jari da wannan asusu cikin hadin gwiwa domin kafa wannan masana'antar samar da gilas, wato masana'antar samar da gilas ta farko ta kasar Habasha. Yanzu an riga an shiga zangon karshe na gwaji, an sa ran cewa, za a soma samar da gilas a shekara ta 2009.

Lokacin da yake zantawa kan yadda ake zuba jari kan wannan masana'antar samar da gilas, Mr. Sun Guoqiang, babban direkta na kamfanin Habasha na babban kamfanin CGCOC ya bayyana cewa, "A kasashen Afirka kamar kasar Habasha, a hakika dai suna maraba da kamfanonin kasar Sin da su je kasashensu domin samar da ayyukan yau da kullum, kuma sun fi son kamfanonin kasar Sin da su zuba jari a fannin sana'o'in kere-kere sabo da su ne muhimmin sashen da ba za a iya kyale su daga batun bunkasa tattalin arzikin kasar Habasha ba. Kasashen Afirka sun fi mai da hankali kan jarin da ake zubawa a fannonin tattalin arzikinsu."

Bayan da masana'antar samar da gilas ta Hansheng ta soma samar da gilas a kasar Habasha, za a canja tarihi na rashin yin gilas a kasar Habasha, har ma a duk fadin yankunan gabashin Afirka. Sabo da haka, za a iya fitar da gilas da aka yi a kasar Habasha zuwa sauran kasashen gabashin Afirka. Kasar Habasha za ta iya samun karin kudin musaya. Wannan abu ne mai ma'ana sosai ga gwamnatin kasar Habasha wadda take karancin kudin musaya. Malam Asfawkun ya ce, "A da mun shigo da gilas. Amma yanzu, za mu iya yin amfani da gilas da aka yi a kasarmu, kuma a nan gaba, za mu iya fitar da su zuwa kasashen waje. Wannan zai ba da taimako sosai ga tattalin arzikinmu. Wannan kyakkyawan abu ne a gare mu."

Mr. Sun Guoqiang ya bayyana cewa, sabo da wannan masana'antar yin gilas ta farko ce da aka kafa a kasar Habasha. Sakamakon haka, horar da 'yan kwadago na Habasha da su kware kan fasahar yin gilas da masanan Habasha da za su iya tafiyar da wannan masana'anta, ko shakka babu nauyi ne da ke kan bangaren kasar Sin. Yanzu a cikin wannan masana'anta, ban da kwararru wadanda suka kware kan fasahar yin gilas da manyan manajoji, sauran 'yan kwadago mutane ne na wurin. Horar da kwararru, wannan bukata ce ta bangaren Habasha, kuma shiri ne na bangaren kasar Sin. Mr. Sun ya ce, "Muna da nauyin horar da ma'aikatan wurin. Dokar gwamnatin kasar Habasha ta kuma bukace mu da mu yi haka. Dole ne mu horar da 'yan kwadago na wurin da su zama 'yan kwadago masu kwarewa kan aikinsu a cikin shekaru 2 ko 3. Bayan da su mallaki fasaha, za su iya hawa kan gurbinsu na aiki. A hakika dai, idan mun yi amfani da 'yan kwadago da yawa na wuri, za mu iya yin tsimin kudaden da za mu kashe domin hayan 'yan kwadago."

Malam Asfawkun ya ce, bisa shirin da ya tsara a da, yana son yin aiki a cikin wannan masana'anta shekaru 2 ko 3 ne kawai, amma yanzu ya canja shirinsa. Ya ce, zai yi aiki a cikin wannan masana'anta har abada idan Allah ya yarda.

"Lokacin da na shiga wannan masana'anta, na taba gaya wa jagoran masana'antar cewa, zan yi aiki a wannan masana'anta na tsawon shekaru 2 ne kawai. A nan gaba, zan ci gaba da yin karatu, kuma mai yiyuwa ne zan shiga harkokin siyasa. Ina son samun mukami mafi muhimmanci, ba kamar na yanzu ba. Ya zuwa yanzu, na riga na yi shekaru 2 ko fiye ina aiki a cikin wannan masana'anta. Kuma na riga na canja tunanina. Zan ci gaba da yin aiki a wannan masana'anta."

Har yanzu ba a kammala bayani game da Zemedkun Asfawkun. Malam Asfawkun ya ci gaba da yin aiki a wannan masana'antar yin gilas, wannan kyakkyawan abu ne ga shi da kuma kamfanin CGCOC. A waje daya kuma, kamfanonin kasar Sin sun nemi bunkasa a kasar Habasha, shi kuma kyakkyawan abu ne ga kamfanonin kasar Sin da kuma bangaren kasar Habasha. A waje daya kuma, kamfanonin kasar Sin za su samu ribar da suke so, kuma za su iya isar da fasahohin zamani na yin kayayyaki da na tafiyar da masana'antu a kasashen Afirka. Sabo da haka, kasashen Afirka za su iya samun saurin neman bunkasuwa. Mr. Tadesse Haile, karamin ministan cinikayya da masana'antu na kasar Habasha ya gaya wa wakilanmu cewa, "Muna tsammani cewa, hanyar neman bunkasa da kasar Sin ta kirkiro tana kasancewa tamkar wani abin koyi ga kasar Habasha wajen neman cigaba. A nan gaba, za mu shiga irin wannan zango na neman cigaba. Muna son koyon fasahohin kasar Sin wajen neman bunkasuwa. Kuma mun sa kaimi ga masana'antun kasar Sin da su zo Afirka, ciki har da Habasha. Kowa yana ganin cewa, masana'antun kasar Sin sun zo kasarmu tare da guraban aikin yi da saurin daidaita harkokin yau da kullum da kuma alkawari. A waje daya kuma, gwamnatin kasar Sin ta sa kaimi kan masana'antunta da su zuba jari a Afirka. Ta kuma kafa asusun raya Afirka. Kasar Habasha tana samun moriya daga irin wadannan shirye-shirye. Wannan shi ne hadin gwiwar da ake samun moriyar bangarorin biyu." (Sanusi Chen)