Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-10-09 16:11:49    
ranar bikin haduwar iyali

cri
To, masu sauraro, bayan dubun gaisuwa mai tarin yawa, duk ma'aikatanmu na sashen Hausa muna fatan kuna cikin koshin lafiya kamar yadda muke a nan birnin Beijing. A makon da ya gabata, mun yi gagarumin bikin murnar cika shekaru 60 da kafa jamhuriyyar jama'ar Sin a filin Tian'anmen dake birnin Beijing na Sin. Masu sauraronmu da yawa sun ba mu sakwanninsu domin nuna gaishe-gaishe da fatan alheri da kuma taya murna, a ciki har da malam Mohammed Idi Gargajiga daga jihar Gombe, tarayyar Nijeriya, ya bayyana cewa, "Bisa matsayinmu na aminan jama'ar kasar Sin baki daya, muna taya murna da farin ciki sosai ga gwamnatin kasar Sin da jama'arta domin cika shekaru 60 da kafa sabuwar kasar Sin da irin babbar moriyar da Sin ta samu a cikin shekaru 60 da suka gabata. Jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin tana tafiyar da tsarin mulki mai kyau da kuma gudanar da siyasa cikin tsabta. Kasar Sin tana kara karfi a duk duniya, kuma bunkasuwar tattalin arzikin kasar tana ba da babbar gudunmawa ga duniya. Muna fatan alheri cewa, kasar Sin tana da nasara kuma za ta kara yin nasara a nan gaba cikin sabon tarihi da Sin za ta shiga. Na jaddada cewa, kasar Sin za ta tsaya tsayin daka kan hanyar raya sha'anin gurguzu mai sigar musamman na kasar sin, da nacewa ga bin manufar yin gyare-gyare a gida da bude kofa ga kasashen waje, da tabbatar da aikin samun ci gaba ta hanyar kimiyya da fasaha, da kuma sa kaimi ga raya wata zamantakewar al'uma mai jituwa, da sanyawa bangarorai daban-daban sabon kuzari, da kara karfinsu na kirkira cikin himma da kwazo, ta yadda za a tattara hazikanci da karfi daga dukkan fadin kasar Sin wajen kara gina zamantakewar al'umma ta Sin mai wadata. Tare da fatan duk jama'ar kasar Sin za su sanya dukkan karfinsu wajen kara ingiza bunkasuwar kasar Sin, domin Sin ta zama wata kasa mafi karfi a duk duniya."

To, mun gode? malam Mohammed Idi Gargajiya daga jihar Gombe, tarayyar Nijeriya da duk membobin kungiyarka. A cikin sakonka, mun gano cewa, ka fahimci manufofi da dama da gwamnatin Sin take dauka, kamar manufar bude kofa ga kasashen waje da yin kwaskwarima a gida da dai sauransu. Ba shakka, kana sauraronmu cikin dogon lokaci, wannan ya burge mu kwarai da gaske. A cikin wannan muhimmin lokaci na cika shekaru 60 da kafa sabuwar kasar Sin, muna fatan za ka ci gaba da mai da hankali kan shirye-shiryenmu kamar yadda kake yi, Allah ya karfafa dankon zumunci a tsakaninmu, amin.

To, sakon malam Mohammed Idi Gargajiga ke nan. bayan haka kuma, malam Musa Adamu Abubakar, Katsina, tarayyar Nijeriya ya rubuto mana cewa, "A ra'ayina, wannan wani irin biki ne da za a gabatar da shi da dukkan mutanen Sin da na duniya baki-daya za su shaida. Ni Musa Adamu Abubakar, ina tabbatar da cewa, za ku samu goyon baya da yawa daga kasashen duniya a kan wannan biki, da fatan mu mika wannan biki lafiya da alheri."

To, mun gaida malam Musa Adamu Abubakar daga Katsina, tarayyar Nijeriya. Lalle, wannan gagarumin biki na cika shekaru 60 da kafa sabuwar kasar Sin ya sami babban goyon baya daga kasa da kasa, kuma ya gudana lami lafiya. Mun godewa duk wadanda suka ba da taimako, da fatan za mu sada zumunta tsakaninmu har abada.

Masu sauraro, ranar 3 ga watan Oktoba na bana rana ce ta haduwar iyali irin ta gargajiya, tana da muhimmanci kwarai a kasar Sin, wadda take biye da bikin ranar sabuwar shekara kawai. Ko kuna sha'awarta? Mene ne asalinta? Yaya ake yi a lokacin ranar haduwar iyali a kasa da kasa? Ko akwai bambanci tsakaninsu? Watakila akwai ayoyin tambaya da dama a zukatanku, to, yanzu za mu kokarta kawo muku wani cikakken bayani kan wannan ranar biki.

Ranar 15 ga watan Agusta na kowace shekara bisa kalandar manoma ta kasar Sin, ranar gargajiya ce ta haduwar iyali. Kuma a kan rada mata wani suna na daban, wato ranar tsakiyar yanayin kaka, sabo da ta kan zo a wannan lokaci. Bisa kalandar noma ta kasar Sin, an kasa shekara daya zuwa kashi hudu, kowane kashi kuma ya hada da matakai uku, wato Meng, da Zhong, da Ji. Yanayin kaka ya kunshi watanni uku, wato daga wata na bakwai zuwa wata na tara na kalandar noma ta Sin. Shi ya sa, wata na takwas yake tsakiyar yanayin kaka, yayin da ranar 15 take tsakiyar wata na takwas. A sabili da haka, an kira wannan rana, ranar tsakiyar yanayin kaka.

Bisa labarin da aka bayar, an ce, a wannan rana, duniyar wata ta fi kusa da duniyar kasa, shi ya sa duniyar wata ta fi girma da kuma yin haske. Don haka, a kan sheda ta a wannan rana. Dadin dadawa, duk 'yan matan da suka je gidan mahaifansu dole ne su koma gidan mazajensu a wannan rana domin samun alheri.

An fara murnar ranar haduwar iyali, wato ranar tsakiyar yanayin kaka a daular Tang. Daga bisani, a daular Ming, an fara cin wainar wata da 'ya'yan itatuwa domin murna. A yanzu kuma, a kan shirya liyafa domin shedar duniyar wata da iyalai, tare da shan giya da cin wainar wata, a yunkurin fatan alheri da koshin lafiya ga iyalai.

Bisa tasirin kasar Sin, wasu kasashen kudu maso gabashin Asiya da na arewa maso gabashin Asiya su ma sun taya murnar ranar haduwar iyali, musamman ma wasu mutanen Sin dake zama a wadannan kasashen Asiya.

A kasar Japan, mutane su kan kira wannan rana bikin duniyar wata a tsakiyar yanayin kaka. Su ma su kan sheda duniyar wata a wannan rana. Amma sun ci tuwon wata a maimakon wainar wata.

A kasar Vietnam, yara su kan taka muhimmiyar rawa. Sabo da a wannan rana, akwai wainar wata iri-iri da fitilu masu launuka da kayayyakin wasa iri daban daban, wadanda suka jawo hankulan yara kwarai da gaske. Bayan haka kuma, a kowace shekara, a kan gudanar da bikin shaida fitilu masu launuka domin murnar ranar haduwar iyali.

A Singapore kuma, mutanen Sin sun fi yawa, shi ya sa mutanen kasar sun fi dora muhimmanci kan wannan ranar bikin haduwar iyali. A wannan rana, su kan yi mu'amala da abokai da ma'aikatan aiki da sauransu, da ba da kyautar wainar wata, a yunkurin nuna godiya da gaishe-gaishe da fatan alhari.

A Malaysiya, cin wainar wata da jin dadin kallon duniyar wata da kuma rike da fitila domin yin fareti sun zama al'adun mutanen Sin zuriya bayan zuriya.

To, masu sauraro, bayanin ke nan kan ranar haduwar iyali. Bayan haka, kwanan nan, shugaba Abdullahi Baji daga Freedom Radio, Kano, tarayyar Nijeriya ya bugo mana wayar tarho domin nuna gaisuwa ga duk ma'aikatanmu na sashen Hausa na CRI, mun gode kwarai. Akwai kuma wasu sakwannin gaishe-gaishe daga wajen malam Salisu Dawanau, Abuja, tarayyar Nijeriya, da malam Sabobawa Bako, kaduna, tarayyar Nijeriya da dai sauransu, wadanda ba mu iya karanta sakwanninsu duka ba sabo da karancin lokaci, amma muna godiya a gare ku duka, kuma Allah ya karfafa dankon zumunci a tsakaninmu. Sai mako mai zuwa idan Allah ya sa.(Fatima)