Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-10-02 18:20:40    
Kasar Sin za ta ci gaba da bin hanyar da take bi yanzu, kuma za ta sauke nauyin da ke kanta kan harkokin kasa da kasa

cri
Muhimmin jawabin da shugaba Hu Jintao na kasar Sin ya yi na mintoci 8 ya kasance na daya daga cikin muhimman abubuwa na bikin taya murnar cika shekaru 60 da kafuwar Jamhuriyar Jama'ar Sin da aka shirya a ran 1 ga watan Oktoba. Masanan kasar Sin suna ganin cewa, jawabin da Mr. Hu ya yi ya sheda wa sauran kasashen duniya cewa, kasar Sin za ta ci gaba da tsayawa tsayin daka kan matsayin bin hanyar gurguzu da ke dacewa da halinta na musamman, kuma tana son hada kan sauran kasashen duniya domin sauke nauyin da ke kanta ta fuskar neman ci gaba da zaman lafiya a duniya, kuma tana son bayar da gudummawarta kamar yadda ya kamata.

Mr. Zhu Yan, wani shehun malami wanda ke nazarin tarihin jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin ya ce, ko da yake, jawabin da shugaba Hu ya yi ba shi da tsawo, amma yana kunshe da abubuwa da yawa. Mr. Zhu ya ce, "Jawabin da shugaba Hu ya yi wani kyakkyawan bayani ne da ke takaita tarihi, kuma shi ne wani fatan alheri ga makomar al'ummar Sinawa. Ya tabo tarihin sabuwar kasar Sin na shekaru 60 da suka gabata, ya kuma tabo hakikanin halin da kasar ke ciki yanzu da nauyin da ke kanta, har ma da yadda za a samu ci gaban kasar a nan gaba. Sannan ya tabo nauyin da ke kan kasar Sin lokacin da take kokarin daidaita harkokin kasa da kasa."

Bana shekara ce ta cika shekaru 60 da kafuwar sabuwar kasar Sin, kuma shekara ce ta cika shekaru 60 da jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin take rike da karagar mulkin kasar. Mr. Zhu Yan ya ce, a cikin jawabinsa, Mr. Hu ya yi waiwaye da kuma takaita tarihin juyin juya hali da na raya kasar da kuma na yin gyare-gyaren jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin ta yi a kasar, kuma ya fi mai da hankali kan muhimman abubuwa uku.

"Da farko dai, ci gaban da sabuwar kasar Sin ta samu cikin shekaru 60 da suka gabata sun sheda cewa, tunanin gurguzu ne kawai ya iya samun damar ceto kasar Sin. Tarihi ya shaida cewa, kasar Sin ta yi daidai wajen bin hanyar gurguzu. Na biyu, Mr. Hu ya yaba wa babbar manufar yin gyare-gyare a gida da kuma bude kofa ga kasashen waje. Shugaba Hu ya kuma jaddada cewa, bin manufar yin gyare-gyare a gida da kuma bude kofa ga kasashen waje ne kawai zai ciyar da kasar Sin gaba. Bugu da kari kuma, shugaba Hu ya yaba wa manufofin neman ci gaba bisa hanyoyin kimiyya."

Game da bunkasuwa da hanyoyin neman ci gaba da kasar Sin ta samu kuma take bi, Mr. Qin Xiaoying wani fitacce a kasar Sin yana ganin cewa, a cikin jawabin da Mr. Hu ya yi ya bayyana cewa, shugaba Hu ya jaddada musamman cewa, kasar Sin za ta hada kan sauran kasashen duniya, ta yadda za ta iya bayar da gudummawarta wajen shimfida zaman lafiya da bunkasuwa a duk duniya cikin lumana. Mr. Qin ya ce, "A ganina, wannan furucin da shugaba Hu ya yi yana da ma'ana sosai. Yau shekaru 60 da suka gabata, marigayi Mao Zedong, shugaban kasar Sin na wancan lokaci ya taba bayyana cewa, tabbas ne kasar Sin za ta bayar da karin gudummawarta ga bil Adam gaba daya. Mao Zedong ya fadi haka ne a wancan lokaci domin bayyana imanin sabuwar kasar Sin da burin da take kokarin cimmawa. Bayan shekaru 30 da aka yi gyare-gyare da bude kofa ga kasashen waje, yanzu kasar Sin tana da karfi da tunani na sauke nauyin da ke kanta kan harkokin kasa da kasa."

Mr. Qin Xiaoying ya kara da cewa, bayar da karin gudummawa ga kokarin shimfida zaman lafiya da ci gaban duk duniya, nauyi ne da ke kan kasar Sin, kuma ba za ta iya mantawa da shi ba yanzu, har ma a nan gaba. (Sanusi Chen)