Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-09-30 21:50:20    
Gwamnatin kasar Sin ta shirya gagarumar liyafa domin murnar cika shekaru 60 da kafuwar Jamhuriyar Jama'ar Sin

cri

A ran 30 ga wata da maraice, majalisar gudanarwa ta kasar Sin, wato gwamnatin kasar ta shirya gagarumar liyafa a nan birnin Beijing domin taya murnar cika shekaru 60 da kafuwar Jamhuriyar Jama'ar Sin. Muhimman jami'ai da baki fiye da dubu 4 na kasar Sin da na kasashen waje sun halarci wannan liyafa domin taya murna a yayin wannan biki tare.

A ran 1 ga watan Oktoba na shekarar 1949, an sanar da kafuwar Jamhuriyar Jama'ar Sin. Sabo da haka, kasar Sin ta shiga wani sabon lokaci a tarihinta. A cikin shekaru 60 da suka gabata, kasar Sin ta samu ci gaban da yake jawo hankalin duk duniya a fannonin tattalin arziki da zaman al'umma. Me ya sa al'ummar Sinawa da ta dade tana kasancewa a wannan duniya ta iya samun sabon yanayi a cikin wadannan shekarun da suka gabata? A cikin jawabin da Mr. Wen Jiabao ya yi a yayin bikin, ya ba mu amsa da cewa, "A hakika dai, jama'ar kasar Sin sun ci nasarar samun wata hanyar zamanintar da kasar irin ta gurguzu da ke dacewa da halin musamman na kasar bisa tunanin Mao Zedong da Deng Xiaoping da kuma sauran muhimman tunani. Bisa wadannan tunani, jama'ar Sin sun 'yantar da kwakwalwarsu da kuma daidaita harkoki bisa hakikanin halin da ake ciki a kasar."

Wen Jiabao ya nuna cewa, fasahohin da aka samu a cikin wadannan shekaru 60 da suka gabata sun bayyana cewa, a lokacin da ake kan matakin farko na raya zaman al'ummar gurguzu, dole ne a sanya aikin raya tattalin arziki a gaban kome, kuma a raya tattalin arziki da harkokin siyasa da al'adu da kuma zaman al'umma da tabbatar da ingancin yanayin daukar sauti irin na gurguzu bisa manufofin yin gyare-gyare da bude kofa. Mr. Wen ya ce, "Dole ne kasar Sin ta kara yin gyare-gyare a fannonin tsarin tattalin arziki da na siyasa da makamatansu, kuma ta sa kaimi ga jama'ar duk kasa da su yi kokarin aiwatar da aikinsu da kuma tabbatar musu adalci da daidaito domin tabbatar da ganin duk kasar ta kasance cikin hali mai cike da sabon yanayi."

Mr. Wen ya kara da cewa, kasar Sin za ta tsaya tsayin daka kan matsayinta na tabbatar da kwanciyar hankali da samun babbar moriyar jama'a. Kuma za ta karfafa da kuma raya huldar zaman daidaiwa daida da gama kai da taimakawa juna da zumunci bisa tunanin gurguzu a tsakanin kabilu daban daban.

A waje daya, Wen Jiabao ya jaddada cewa, za a ci gaba da bin manufar "aiwatar da tsare-tsaren zaman al'umma iri biyu a cikin kasa daya" domin tabbatar da dorewar kwanciyar hankali da bunkasuwa a yankunan musamman na Hongkong da Macau cikin dogon lokaci. Bugu da kari, kasar Sin za ta tsaya tsayin daka kan matsayinta na kasancewa daya tak a duniya, kuma za ta hada kan 'yan uwa na Taiwan domin kafa wani sabon halin da ake ciki a tsakanin gabobi biyu na mashigin tekun Taiwan a fannin raya hulda a tsakaninsu cikin lumana, kuma za ta yi kokarin samun hadin kan kasar Sin cikin lumana.

A shekarar da ake ciki, tattalin arzikin duniya ya samu kalubale mai tsanani sosai. Tattalin arzikin kasar Sin ya samu illa kwarai. Game da matsayin da kasar Sin ke dauka domin tinkarar wannan matsala, Mr. Wen Jiabao ya ce, "Kasar Sin ba za ta iya rabuwa da sauran kasashen duniya ba, sauran kasashen duniya suna bukatar kasar Sin. Za mu ci gaba da aiwatar da manufar dilflomasiyya ta 'yantar da kasa mai zaman kanta cikin lumana, kuma za mu ci gaba da bin hanyar neman bunkasuwa cikin lumana har abada. Bugu da kari kuma, za mu ci gaba da yin kokarin tabbatar da dawaumammen zaman lafiya da bunkasuwa da jituwa a duniya." (Sanusi Chen)