Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-09-30 18:29:46    
Jama'ar Sin suna Alla-Alla wajen zuwan ran 1 ga watan Oktoba

cri

Ranar Alhamis 1 ga watan Oktoba, rana ce ta cika shekaru 60 da kafuwar Jamhuriyar Jama'ar kasar Sin. A kwanan baya, mutane na sassa daban daban na kasasr Sin sun yi murnar ranar kafuwar sabuwar kasar Sin ta hanyoyi daban daban. Wasu sun shirya wasannin fasaha, wasu sun shirya bukukuwan nune zane-zane da na raye-raye da wake-wake, wasu kuma sun samar da abubuwan kyauta da hannunsu, da fatan dai kasar Sin mahaifarsu za ta samu wadatuwa.

A nan Beijing, an yi wa shahararren titin Chang'anjie da sauran muhimman tituna da mahadun tituna ado da danyun furani masu mabambanta launuka da kyawawan jajayen fitilu. Manyan kantunan da ke muhimman titunan kasuwanci kamar Wangfujing da Xidan kuma, an kayatar da su sosai. A shirye suke domin maraba da dimbin masu saye-saye.

A ran 1 ga watan Oktoba, za a yi kasaitaccen bikin faretin soja a babban filin Tian'anmen, yayin da jama'a za su yi maci cikin fara'a. A matsayinsa na daya daga cikin wadanda suka yi shirin yin macin, Zhang Ying, wani dan makarantar sakandare na Beijing bai iya boye zumudi da farin cikinsa ba, inda ya ce,"Yau tabbas ne ba zan yi barci ba. Na ji alfahari matuka da zuwan irin wannan muhimmiyar harka, musamman ma domin murnar cika shekaru 60 da kafuwar sabuwar kasarmu."

A jihar Xinjiang da ke arewa maso yammacin kasar Sin, 'yan kabilu daban daban sun shirya bukukuwan raye-raye da wake-wake domin nuna wa mahaifarsu kasar Sin fatan alheri. Bayan aukuwar tashin hankali a ran 5 ga watan Yuli a bana a birnin Urumchi, makidan jihar Xinjiang sun tsara wata waka mai suna "Mu iyali ne" cikin gajeren lokaci. A gabannin ran 1 ga watan Oktoba, 'yan kabilu daban daban sun rera wannan waka tare cikin Sinanci da harsunan Uygur da Kazak domin nuna hada kan kabilu da kuma karfafa zukatan mutane.

Sebulema, mai shekaru 56 da haihuwa da ke zaune a filin ciyayi a jihar Mongolia ta Gida ta yi rabin shekara tana dinka tufafi 2 masu halin musamman na kabilar Mongolia domin nuna wa mahaifarta kasar Sin fatan alheri. Tana mai cewar,"A sakamakon kyawawan manufofin da Jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin ke aiwatarwa, mun samu babban ci gaba a fannoni daban daban. Ina farin ciki matuka. Ina son in mayar da wadannan tufafi na kabilarmu a matsayin abun kyauta ne na murnar ranar sake kafuwar kasarmu. Ina fatan kasarmu za ta kara samun wadatuwa a sakamakon hadin kan kabilu gaba daya."

A bukukuwan gargajiya, Sinawa kan ci abincin Dumpling, wanda shi ne Jiaozi da Sinanci. A gabannin ran 1 ga watan Oktoba, a unguwar Qingshan ta birnin Yinchuan, babban birnin jihar Ningxia ta kabilar Hui mai cin gashin kanta, mazauna wurin sun samar da wannan irin abinci. A unguwar, wadanda suka fito daga kabilun Han da Hui sun samar da abincin Dumpling guda 2009 tare domin nuna wa kasar Sin mahaifarsu fatan alheri. A cikin wadanda suka samar da wadannan abincin Dumpling, akwai dattijai masu shekaru kusan 80 da haihuwa, da kananan yara, wasu kuma duk zuriyoyi 4 na wani iyali sun shiga wannan harkar dafa abincin. Dukkansu suna himmantuwa wajen dafa abincin. Kowa da kowa cike yake da murmushi a fuskarsa. Li Lihua, wadda ke zaune a wannan unguwa ta bayyana cewa,"A sakamakon wannan harka mai ban sha'awa, mazaune unguwarmu mun yi farin ciki ainun. Muna zama tare cikin jituwa kamar wani iyali. Muna maraba da ranar cika shekaru 60 da kafuwar sabuwar kasar Sin tare kuma da ran 15 ga watan Agusta bisa kalandar gargajiya ta kasar Sin."

A sakamakon kusantowar ran 1 ga watan Oktoba, wato ranar cika shekaru 60 da kafuwar sabuwar kasar Sin, a sassa daban daban na wannan kasa, halin annashuwa zai game ko ina.(Tasallah)