Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-09-30 09:28:23    
Ana yin kokari don sake jawo hankulan 'yan kallon gasar wasan kwallon tebur

cri

A cikin 'yan shekarun da suka gabata, a ko da yaushe, kungiyar wasan kwallon tebur ta kasar Sin ta zama a matsayin koli a duniya, ko a yayin gasar wasannin Olympic, ko a yayin gasar cin kofin duniya, a kullum kungiyar kasar Sin tana samun zama zakaru, a yayin gasa, manya ko kanana, a zagaye na karshe, 'yan wasan kasar Sin biyu sun yi karawa domin neman samun zama zakara, a sanadin haka, a kai a kai 'yan kallo ba za su rike sha'awa kan irin wannan gasa ba, shi ya sa yanzu ana yin kokari don sake jawo hankulan 'yan kallon gasar wasan kwallon tebur. A ran 25 zuwa ran 26 ga watan Agusta na bana, an yi wata gasa a birnin Beijing musamman domin canja irin wannan hali. A cikin shirinmu na yau, bari mu yi muku bayani kan wannan. 

A ran 25 zuwa ran 26 ga watan Agusta na bana, an yi gasar gaba da gaba ta wasan kwallon tebur ta tashar Asiya tsakanin 'yan wasa taurari na Turai da na Asiya ta shekarar 2009 a birnin Beijing. A yayin karawa, kungiyar 'yan wasa taurari ta Turai wadda ke hade da shahararrun 'yan wasa Vladimir Samsonov daga kasar Belarus da Kreanga Kalinikos daga kasar Girka da Michael Maze daga kasar Denmark da Ovcharov Dimitrij daga kasar Jamus da Jorgen Persson daga kasar Sweden da kungiyar 'yan wasa taurari ta Asiya wadda ke hade da shahararrun 'yan wasa Ma Lin da Ma Long daga kasar Sin da Joo Se Hyuk daga kasar Korea ta kudu da Zhuang Zhiyuan daga birnin Taipei na kasar Sin da Zhang Yu daga Hongkong, yankin musamman na kasar Sin sun yi gasa sau biyu, a karshe dai, kungiyar Asiya ta lashe kungiyar Turai bisa rinjaye kadan. Ana iya cewar, karfin wadannan kungiyoyi biyu ya tashi daidai da juna, wato dukkan 'yan wasa sun yi iyakacin kokari a yayin gasar, 'yan kallo ba su san wane ne zai ci nasara ba, shi ya sa sun sake jin dadin kallon gasa.

Kamar yadda kuka sani, a yayin gasar cin kofin duniya ta wasan kwallon tebur da aka shirya daga shekarar 2005 zuwa shekarar 2009, kungiyar kasar Sin ta sami dukkan zakaru sha tara. A yayin gasar wasannin Olympic ta shekarar 2008, 'yan wasan kwallon tebur na kasar Sin su ma sun sami dukkan zakaru hudu. Ban da wannan kuma, a gun wadannan manyan gasanni, kusan dukkan zakaru da lambobin azurfa sun fito ne daga 'yan wasan kasar Sin. A sanadin haka, ba ma kawai 'yan kallo na kasashen ketare sun rasa sha'awa kan gasar wasan kwallon tebur ba, har ma a kai a kai ne masu sha'awar wasan kwallon tebur na kasar Sin su ma ba za su mai da hankali kan zagaye na karshe na gasar neman samun zama zakara kamar yadda suka yi a da ba. Kan wannan batu, Liang Guanghua wanda shi mai sha'awar wasan kwallon tebur ne na birnin Beijing ya gaya mana cewa,  "Idan ka san 'yan wasan kasar Sin za su samun zama dukkan zakaru kafin su gama gasa, to, gasar ba dadi."

Dalilin da ya sa haka shi ne domin matsayin 'yan wasan kwallon tebur na kungiyar kasar Sin ya fi yawancin 'yan wasan sauran kasashen duniya, kuma ba kadan ba. Amma fasahar wasa ta wasu 'yan wasan kasashen Turai ita ma tana da karfi, har ta yi kama da ta 'yan wasan kasar Sin. Kazalika, a yayin wannan gasar dake tsakanin kungiyar Turai da ta Asiya, kasar Sin ta tura 'yan wasa biyu ne kawai, saboda haka, wannan gasa ta fi jawo hankulan 'yan kallo. Game da wannan,tsohon shahararren 'dan wasa na kasar Sweden Persson ya bayyana cewa,  "Idan an zabi 'yan wasan da za su shiga wannan gasa kamar yadda suke so, to, kamata ya yi a zabi 'yan wasa a kalla hudu daga kasar Sin. Amma yanzu 'yan wasa daga kasar Sin sun kai biyu ne kawai. Irin wannan gasar gaba da gaba ta fi samun karbuwa daga wajen 'yan kallo da kuma masu sha'awar wasan kwallon tebur."

Babban malamin horaswa na kungiyar 'yan wasa taurari ta Turai daga kasar Jamus Richard Prause shi ma ya dauka cewa, irin wannan gasa tana da kyau, saboda gasa mai cike da alla-alla za ta ba da gudumowa ga bunkasuwar wasan kwallon tebur. Ya ce, "'Yan wasa sun fi son shiga irin wannan gasa, koda yake 'yan wasa sun fi mai da hankali kan gasar cin kofin duniya da gasar wasannin Olympic, amma irin wannan gasar gaba da gaba tsakanin 'yan wasan Turai da na Asiya wadda ta sa 'yan kallo suke alla alla domin sanin sakamako na karshe ita ma tana da muhimmanci. Musamman ma bayan da aka watsa labaran da abin ya shafa ta telebijin, ko shakka babu za a ciyar da wasan kwallon tebur gaba."

Babbar hukumar kula da wasan kwallon tebur ta Asiya da ta Turai sun shirya wannan gasar gaba da gaba tare. Nan gaba, kowace shekara za a shirya wannan gasa sau daya, kuma za a yi a tasoshi biyu wato Asiya da Turai. Babban sakataren babbar hukumar kula da wasan kwallon tebur ta Asiya kuma mataimakin shugaban kwamitin wasannin Olympic na Hongkong na kasar Sin Yu Guoliang ya gaya mana cewa,  "Ina fatan wannan gasa za ta sa kaimi ga yalwatuwar wasan kwallon tebur a sauran kasashe da shiyoyyi na Asiya."

Babban malamin horaswa na kungiyar Turai Prause ya ba da shawara cewa, ya fi kyau a rage 'yan wasan kasar Sin a yayin gasar da za a shirya a nan gaba. Ya ce,  "Ina tsammani cewa ya fi kyau a kara wani 'dan wasa daga kasar Japan, kuma a rage wani 'dan wasa daga kasar Sin, wato kowace kasa ta tura wani 'dan wasa daya kawai."

A hakika dai, babbar hukumar kula da wasan kwallon tebur ta Asiya ita ma tana yin la'akari kan wannan lamari. Babban sakataren wannan hukuma Yu Guoliang ya fayyace cewa, a yayin gasa ta tasha ta Turai da za a shirya a kasar Turkey a watan Nuwamba na bana, wani 'dan wasan kasar Japan zai shiga wannan gasa. Kuma za a rage 'yan wasan kasar Sin daga biyu zuwa daya.

Domin ciyar da wasan kwallon tebur na duniya gaba, a ko da yaushe kungiyar wasan kwallon tebur ta kasar Sin tana yin matukar kokari, kungiyar wasan kwallon tebur ta kasar Sin ita ma tana goyon bayan gasar gaba da gaba tsakanin Turai da Asiya. Babban malamin horaswa na kungiyar Asiya kuma malamin horaswa na kungiyar maza ta kasar Sin Liu Guoliang yana ganin cewa,  "Dalilin da ya sa aka shirya wannan gasar gaba da gaba tsakanin 'yan wasan Turai da na Asiya ita ce domin kara ingiza bunkasuwar wasan kwallon tebur a ko ina a duniya, a sa'i daya kuma za a sa 'yan kallo su kara jin dadi a wurin gasa." Duk da haka, idan matsayin 'yan wasan kwallon tebur na sauran kasashen duniya ya kai na 'yan wasan kasar Sin, to, 'yan kallo za su kara jin dadi.(Jamila Zhou)