Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-09-15 21:10:17    
Ko an canja halin da ake ciki a titin Wall bayan da aka cika shekara daya da rufewar Lehman Brothers?

cri

Yau shekara daya da ta gabata, wato a ran 15 ga watan Satumba na shekarar bara, ba zato ba tsammani aka sanar da rufe bankin zuba jari na Lehman Brothers wanda ya fi girma na hudu a cikin bankunan kasar Amurka. Sakamakon haka, an haddasa rikicin kudi mafi tsanani a duk duniya tun daga shekaru 30 na karnin da ya gabata. Wannan rana ta kuma zama wadda ba za a manta da ita ba har abada ga titin Wall, har ma duk kasar Amurka. Yanzu bisa tallafawar gwamnatin Amurka, tsarin kudi na Amurka yana samun tabbaci a kai a kai, amma ya zuwa yanzu ko an kau da wannan rikicin kudi gaba daya? Ko kuma an samu damar canja halin da ake ciki a titin Wall? Manazarta da yawa suna shakkar irin wadannan tambayoyi.

Ko da yake shekara daya ta wuce, amma har yanzu Amurkawa suna cece-ku-ce game da Lehman Brothers. Bisa wani binciken da "Market Watch", wata tashar intanit da ke kula da harkokin tattalin arziki da kudi ta Amurka ta yi a kwanan baya, an ce, masu karanta shafin intanit da yawansu ya kai kashi 60 cikin kashi dari suna ganin cewa, ya kamata gwamnatin kasar Amurka ta ceci bankin Lehman Brothers. Akwai wasu masu ilmin tattalin arziki da suka taba kimanta cewa, idan gwamnatin kasar Amurka ta ba da tallafin kudi ga bankin Lehman Brothers a watan Satumba na bara, yawan kudin da ya kamata a kashe ya kai dalar Amurka kimanin biliyan 6. Amma yanzu bisa kididdiga mai dumi-dumi da asusun ba da lamunin kudi na duniya ya yi, yawan hasarar da wannan rikicin kudi ya kawo wa duk duniya kai tsaye ya kai dalar Amurka biliyan 1600. Kuma an kimanta cewa, sauran kudin da za a kashe domin kara kyautata tsarin harkokin kudi za su kai dalar Amurka kusan biliyan dubu 12, wato zai kai kashi daya bisa kashi biyar daga cikin jimillar kudaden da ake samarwa a duk duniya a kowace shekara.

A waje daya, a lokacin da ake fada wa juna batun rufe bankin Lehman Brothers, ana yabawa matakan tallafawa tsarin harkokin kudi da gwamnatin Amurka ta dauka. Kwararru suna ganin cewa, ma'aikatar harkokin kudi ta Amurka ta kebe dalar Amurka biliyan dari 7 ga bankuna domin ceton dukiyoyin bankunan da ba su samar da riba, kuma bankin ajiyar kudi na Amurka ya samar da rancen kudi ga masana'antu masu karancin kudin neman ci gaba kai tsaye, kuma gwamnatin Amurka ta ba da lamuni da karin rancen kudin da bankuna suka samar, har ma ma'aikatar kudi ta Amurka ta yi jarrabawa ga manyan bankuna, su ne matakan sa kaimi ga mutane da su yi imani ga tsarin kudi na Amurka, da tabbatar da samar da isashen rancen kudi a kasuwa.

Bayan da gwamnatin Amurka ta dauki wadannan hadaddun matakai, tsarin kudi na Amurka ya soma shiga yanayi mai kyau. Tun daga karshen farkon watanni 3 na shekarar da ake ciki, muhimman kasuwannin hada-hadar kudi na duniya sun soma samun farfadowa. A waje daya, yawan ribar da bankuna suke samu yana ta samun karuwa cikin sauri. Alal misali, a cikin watanni 3 na zango na biyu na shekarar da ake ciki, yawan ribar da bankuna biyar na kasar Amurka, kamar su bankin Goldman Sachs da Jpmorgan Chase da na Wells Fargo da na Citigroup da bankin Amurka suka samu ya kai dalar Amurka biliyan 13, wato ya karu da ninki daya bisa na makamancin lokaci na shekarar bara. Bugu da kari kuma, wadannan bankuna sun dawo da takardun samun ikon mallakar takardun hannun jari. Sannan bankuna da yawa sun mayar da tallafin kudin da gwamnatin Amurka ta samar musu domin dawowa da takardun samun ikon mallakar takardun hannun jari.

Amma a waje daya, manazarta suna ganin cewa, sakamakon da aka samu ba ya bayyana cewa, yanzu rikicin kudi ya riga ya tafi nisa da mu. Sabo da halin da ake ciki a titin Wall bai samu sauye-sauye a zahiri ba. Nan ba da dadewa ba, za a kira taron shugabannin kungiyar kasashe 20 a birnin Pittsburgh. A yayin taron, batun sa ido kan harkokin kudi zai zama daya daga cikin muhimman batutuwan da za a tattauna. Kasashe daban daban sun riga sun yarda da yin kwaskwarima kan tsarin sa ido ga harkokin kudi. (Sanusi Chen)