Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-09-02 09:24:57    
Za a hana yin amfani da rigar iyon da aka dinka da fasahar zamani daga shekarar 2010

cri

Kwanakin baya ba da dadewa ba, babbar hukumar kula da wasan iyo ta duniya ta bayar da wani umurni inda ta tanada cewa, za a hana 'yan wasa su sa rigar wasan iyon da aka dinka da fasahar zamani yayin da suke fafatawa da juna tun daga shekarar 2010, lamarin ya alamanta cewa, gasar cin kofin duniya ta wasan iyo ta shekarar 2009 da aka yi a birnin Rome na kasar Italiya ta zama babbar gasa ta matsayin duniya ta karshe da za a yi amfani da irin wannan rigar wasan iyo ta zamani. A yayin wannan babbar gasa, rigar wasan iyo ta zamanin da ake kiranta da suna 'fatar kifin shark' ta ba da babban amfaninta kuma ta ba da amfani na karshe. A cikin shirinmu na yau, bari mu yi muku bayani kan wannan.

A wurin da aka shirya gasar cin kofin duniya ta wasan iyo a birnin Rome, akwai kantuna biyu wadanda suka fi jawo hankalin mutane, wani dake cikinsu shi ne kantin sayar da kayayyakin tuna baya, wani na daban shi ne kantin sayar da rigar wasan iyo ta 'Speedo', wato wata shahararriyar alamar ciniki ta kamfanin dake dinka rigar wasan iyo a duniya. A cikin wannan kanti, an yi nune-nunen riguna biyu na wasan iyo wadanda kamanninsu ya yi kama da fatar kifin 'shark', mutane su kan taba kan rigunan saboda suna jin mamaki da ganinsu.

A yayin zagaye na karshe na gasar wasan iyon 'free style' ta mata ta mita 4×200, kungiyar kasar Sin ta karya matsayin bajimta na duniya da kungiyar kasar Australia ta kago a yayin gasar wasannin Olympic ta Beijing da minti 7 da dakika 42 da digo 08, kuma ta zama zakara. Bayan gasar, 'yar wasa ta kungiyar kasar Sin Liu Jing ta bayyana cewa,  "Mun karya matsayin koli na duniya, lamarin ya yi kama da mafarki, amma mun yi iyakacin kokari. Saboda kafin wannan gasa, babban malami mai horas da mu ya gaya mana cewa, idan ba mu iya karya matsayin koli na duniya ba, to, ba zai yiwu ba mu samu zama zakara, shi ya sa muka yi namijin kokari a yayin gasa."

Me ya sa aka kyautata tunani da cewa, idan ana son zama zakara, dole ne su karya matsayin koli na duniya? Game da wannan batu, ana iya cewa, dalilin da ya sa haka shi ne domin rigar wasan iyon da aka dinka ta hanyar fasahar zamani, irin wannan rigar iyo ta sa karya matsayin koli na duniya ya zama abu mai sauki. Ya zuwa ran 30 ga watan Yuli na bana wato shekarar 2009, an riga an karya matsayin koli na duniya sau 20 a yayin wannan zama na gasar cin kofin duniya ta wasan iyo, wasu 'yan wasa sun karya matsayin kolin duniya a yayin karawar kusan karshe, har ma a yayin gasar share fage.

A sanadin haka, wasu alamomin ciniki na rigar wasan iyo kamarsu 'Speedo' da 'Arena' da 'Jaked' da dai sauransu sun fi 'yan wasa jawo hankalin kafofin watsa labarai. Kan wannan, 'dan wasa daga kasar Serbia wanda ya samu zama zakaran wasan iyon 'butterfly' na mita 50 na maza Milorad Cavic ya dauka da cewa, lallai rigar wasan iyon da aka dinka da fasahar zamani ta sa wasan iyo na zamanin yau ya samu manyan sauye-sauye. Ya ce,  "Ban san ainihin amfanin irin wannan rigar wasan iyo ba, ni ma ban yarda da ra'ayin da ake nunawa na cewar sakamakon da aka samu wajen wasan iyo shi ne domin irin wannan riga ba. Amma a hakika dai, rigar wasan iyo ta nuna amfaninta sosai."

Abu mai ban sha'awa shi ne, rigar wasan iyon da aka dinka ta hanyar fasahar zamani ta kawo karshen tarihin al'ajabi na shekaru 4 na 'dan wasa tauraro na kasar Amurka Michael Phelps a birnin Rome. A yayin zagaye na karshe na karawar wasan iyo na 'free style' na maza na mita 200, 'dan wasa daga kasar Jamus Paul Biederman ya lashe Phelps da minti 1 da dakika 42, ya zama zakara kuma ya karya matsayin koli na duniya. A yayin karawar karshe ta wasan iyo na 'free style' ta maza ta mita 200, Biederman ya sa rigar iyo ta 'Arena', ya yi ninkaya cikin saurin gaske, a karshe dai, ya nuna matsayinsa na koli wajen sauri da dakika 3, a yayin karawar mita 400 kuwa, ya nuna matsayinsa na koli wajen sauri da dakika 6. Biederman ya amince da cewa, sakamakon da ya samu yana da nasaba da rigar iyo, amma haka ba laifinsa ba ne. Ya ce,  "Ko shakka babu, rigar iyo ta taimake ni, amma wannan ba laifina ba ne, shi ma ba laifin 'Arena' ba ne, kawo yanzu, babbar hukumar wasan ninkaya ta duniya ba ta hana a sa irin wannan riga ba."

Domin gudanar da gasa bisa adalci, da kuma kara sha'awar jama'a kan wasan iyo kansa, wato ba rigar wasan iyo ba, babbar hukumar wasan iyo ta duniya ta kira wani babban taro inda aka tsai da cewa, daga shekarar 2010, za a hana 'yan wasa su sa rigar iyon da aka dinka ta hanyar fasahar zamani domin shiga gasa. 'Yawancin 'yan wasa sun nuna fahimta da goyon baya kan wannan kuduri. 'Yar wasa daga kasar Amurka wadda ta zama fitacciya a wasan iyo mai salo daban daban ta mita 200 ta mata a yayin gasar cin kofin duniya ta Rome Ariana Kukors ta bayyana cewa,  "Bayan a daina yin amfani da rigar iyo ta fasahar zamani, dukkan 'yan wasa za su fara daga matsayi daya, koda yake da kyar za su karya matsayin koli na duniya a nan gaba, amma nune-nunensu zai kara burge 'yan kallo."

Phelps shi ma ya nuna fatansa cewa, ya kamata a kara mai da hankali kan wasan iyo, amma ba rigar iyo ba ne. Ya ce,  "A cikin 'yan shekarun da suka gabata, fasahar zamani tana kawowa babban tasiri ga wasan iyo, musamman ma rigar wasan iyo, ina fatan za a kara sa muhimmanci kan wasan iyo, wato wasa ne kawai."

Duk da haka, wasu 'yan wasa ba su gamsu da wannan kuduri ba. 'Yar wasan iyo na salo daban daban na mata na mita 200 daga kasar Autralia Stephanie Rice ta bayyana cewa, hana yin amfani da rigar wasan iyo ta fasahar zamani zai sa wasan iyo ya koma baya. Ta ce,  "Kowa da kowa na fatan za su ketare matsayin kansu, a bayyane, rigar iyo ta fasahar zamani ta gabatar mana dabara mai amfani. Idan babbar hukumar wasan iyo ta duniya ta gyara ka'idar da abin ya shafa, to, akwai wuya mu sake samun sakamakon da muka samu yanzu."

Amma, shugaban kwamitin watsa labarai na babbar hukumar wasan iyo ta duniya Cameron Camiti ya kyautata tunani da cewa, makasudin aiwatar da wannan kuduri shi ne a nuna biyayya ga 'yan wasa musamman ma ga 'yan wasan da suka samu zama zakaru a yayin karawa. Ya ce,  "Koda yake wannan kuduri zai rage yawan sabbin matsayin koli na duniya da za a kago. Amma na hakkake cewa, a ko da yaushe, fitattun 'yan wasa za su kara samun babban sakamako bisa adalci."(Jamila Zhou)