To, masu saurare, yaya zaman rayuwarku? Yaya al'amura ke gudana a gare ku a makon da ya gabata? Muna fatan kuna cikin koshin lafiya kamar yadda muke a nan birnin Beijing. Kuma duk ma'aikatanmu na giden rediyon CRI muna fatan za ku ji dadin shirye-shiryenmu tare da samun ilmi daga cikinsu. Bayan haka kuma, muna godiya ga duk wadanda suka aiko mana sakwanninsu, a kokarin sada mana gaishe-gaishe ko kuma shawarwari masu kyau, a ciki har da malam Mohammed Idi Gargajiga, daga jihar Gombe, tarayyar Nijeriya, wanda ya aiko mana sakon da cewar, "Assalam alaikum. Dalilin da ya sa na rubuta wannan sako shi ne domin mu sanar da sashin Hausa na CRI da cewa, duk masu sauraren sashin Hausa na kungiyar masu saurare ta Gombawa ta jihar Gombe suna nuna murna da farin ciki da kuma sahihiyar godiya tare da jinjinawa ga CRI da hukumar yawon shakatawa ta lardin Sichuan na Sin, da suka ba da gagarumar kyauta ta lambar yabo a sakamakon cimma nasarar da na yi a gasar kacici-kacici da kuka shirya a shekarar 2008 dangane da ni'imtattun wurare a lardin Sichuan. A gaskiya wannan girmamawa ba ga kungiyarmu ba ne kawai, har ma ga jihar Gombe da Nijeriya, ko mu ce ga Afirka baki daya. Sabo da haka, kamar yadda muka yi muku alkawari a lokutan baya na cewa, za mu ci gaba da sauraren dukkan shirye-shiryenku na CRI, kuma za mu kara jan damara da kuma kara kwazo wajen turo muku ambaliyar wasiku da tambayoyi iri daban daban. Bayan haka kuma, muna sanar da ku cewa, ba za mu yi barci ba ko yin kasa a gwiwa domin shiga gasar kacici-kacici ta cikon shekaru 60 da kafa jamhuriyar jama'ar kasar Sin. Daga karshe, muna fatan za mu samu babbar nasara a wannan gasa."
To, mun gode, malam Mohammed daga jihar Gombe, tarayyar Nijeriya, da fatan kana sauraronmu. Mu ma mun yi farin ciki da ziyarar da ka kawo mana a nan birnin Beijing da lardin Sichuan na Sin. Kuma muna godiya ga duk membobin kungiyar masu saurare ta Gombawa da ku kokarta shiga sabuwar gasar kacici-kacici da muka shirya. To, masu saurare, ko kun san da cewa, ranar daya ga watan Oktoba na bana rana ce ta cikon shekaru 60 da kafa jamhuriyyar jama'ar kasar Sin. A wannan rana, za a gudanar da gagarumin bikin murna a filin Tian'anmen dake birnin Beijing na Sin. Domin taya murnar ranar, mun shirya wata sabuwar gasar kacici-kacici dangane da lamarin. Kuma muna fatan za ku shiga wannan gasa cikin yakini tare da cimma nasara. Muna maraba da amsoshinku duka.
To, sakon malam Mohammed ke nan. Bayan haka kuma, za mu kokarta amsa wata tambaya daga malam Usman Sani, a Kano, tarayyar Nijeriya ta cewa, "Assalam alaikum. A cikin shirinku na "Zaman rayuwar Sinawa", na ji an ce an yi husufin rana a kasar Sin. Don Allah, ku ba ni cikakken halin da ake ciki dangane da husufin rana." To, yanzu ga abin da ya faru a waccan rana.
A ran 22 ga watan Yuli na bana, an yi husufin rana a yankin kogin Yangtse na Sin, wanda lokacinsa ya fi tsawo a cikin shekaru 500 da suka gabata ko za su zo, wato daga shekarar 1814 zuwa shekarar 2309. Masana da masu sha'awar ilmin taurari da sauran jama'a sun yi sha'awar ganin wannan abin al'ajabi.
A wannan rana da safe da misalin karfe 8, rana ta fara yin husufi. Daga bisani, bayan awa daya kawai, an yi cikakken husufin rana. Mutane masu dimbin yawa sun hallara a filayen wasa da kan duwatsu da gabobin teku, a yunkurin sheda husufin rana. Bayan cikakken husufin rana kuma, nan take yanayin zafi ya ragu sabo da karancin hasken rana. Tsawon lokacin husufin rana ya kai mintoci 6, amma a hakika dai, lokacin abkuwarsa yana da bambanci a biranen Sin. Kuma a wasu birane, an sheda shi yadda ya kamata, yayin da a wasu birane, ba a sheda shi ko kadan ba sabo da yawan gajimare.
A lokacin kuma, wakilinmu Zuo Aifu yana birnin Wuhan na lardin Hubei na Sin, ga abin da ya ce,
"Yanzu kamar karfe 9 da minti 24 na safe, a birnin Wuhan, an riga an yi cikakken husufin rana, ba na iya ganin kome. Yawan mutanen da suke sheda husufin rana a wannan wuri ya kai sama da dubu 10. Dazun nan kuma, suna murna kwarai da gaske. An kunna fitilu dake gefen hanyoyi sabo da duhu. Mutane da yawa suna daukar hotuna da yin shawarwari."
A wurin kuma, wata mace mai suna He Yaqing ta yi magana da wakilinmu inda ta bayyana cewa,
"Ina jin farin ciki kwarai. Na ga duk abin da ya faru, kuma na dauki wasu hotuna domin tunawa da shi. Wannan karo na farko ne da na sheda husufin rana, lalle wannan abin al'ajabi ne."
Ban da Sinawa kuma, akwai mutanen kasashen waje da dama, wadanda suka je birnin Wuhan musamman domin sheda husufin rana. Wani dan Japan mai suna Oka Katvm ya shedawa wakilinmu cewa,
"Da kyar ya sheda husufin rana a rayuwarsa. Shekaruna sun kai sama da 50 a duniya. Zan yi bakin ciki kwarai idan na rasa damar ganinsa a wannan karo."
Amma wasu mutane ba su taka sa'a kamar yadda He Yaqing da Oka Katvm suka taka ba, kamar wani tsoho mai shekaru 81 a duniya. Ya gaya wa wakilinmu cewa,
"Na iso wurin nan da sassafe, amma ban ga kome ba. Watakila Allah ya sa haka."
A sa'i daya, masanan ilmin taurari da na ilmin yanayi sun yi nazari kan husufin rana, tare da samun kyakkyawan sakamako.
To, bayaninmu ke nan ga tambayar malam Usman Sani dake birnin Kano, tarayyar Nijeriya, kuma da fatan ka ji ka gamsu da shi.
Bayan haka kuma, kwanan nan, mun sami sakwannin gaishe-gaishe daga wajen malam Danjuma Aliyu Mohammed daga Kaduna, tarayyar Nijeriya da dai saura, wadanda ba mu iya karanta sakwanninsu duka ba sabo da karancin lokaci, amma muna godiya a gare ku, kuma Allah ya karfafa dankon zumunci a tsakaninmu.(Fatima)
|