Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-08-25 11:37:09    
Kasar Sin ta samu babban ci gaba ta fuskar kimiyya da fasaha cikin shekaru 60 da suka wuce

cri
A cikin shekaru 60 da suka wuce, kasar Sin ta yi ta daga matsayinta na kimiyya da fasaha, kuma abubuwan kimiyya da fasaha suna shafar zaman rayuwar mutane baki daya.

Batun abinci ya taba caza kan mutanen kasar Sin sosai. A shekarar 1949, matsakaicin yawan hatsi da ko wane mutumin Sin ya ci ya kai kilogram dari 2.

Yuan Longping, wani kwararre ne mai ilmin shinkafa na kasar Sin. Wannan tsoho mai shekaru kusan 80 da haihuwa ya taba shan wahalar karancin abinci. Tun bayan wancan lokaci, ya yi aniyar samar da wani nau'in shinkafa mai yalwa, ta haka kasar Sin za ta iya samun karin hatsi. Dan haka, Yuan Longping ya mai da hankali kan nazarin shinkafa mai aure, wadda ta taba rikitar da tunanin mutanen duniya a wancan lokaci. Mr. Yuan ya ce,"Dalilin da ya sa na nuna karfin zuciya sosai kan nazarin wannan shi ne na gano fifikon da shinkafa mai aure ke nunawa. Na yi imani da cewa, a sakamakon ci gaban kimiyya da fasaha, za mu iya kara yawan hatsi sosai. Duk da haka, na yi shekaru 9 ina nazarin irin wannan shinkafa tun daga shekarar 1964."

Dubban gwaje-gwajen da Yuan Longping ya yi a cikin wadannan shekaru 9 sun taimakawa kasar Sin ta cimma buri na samun karin shinkafa daga ko wace gona da kuma hauhawar jimillar shinkafa a duk fadin kasar. Yuan Longping kuma ya zama mai ilmin kimiyya na farko da ya sami nasarar yin amfani da fifikon shinkafa mai aure.

Daga baya kuma, Yuan Longping ya ci gaba da nazarin wata irin shinkafa mai aure ta daban da ta kara yin yalwa. Bayan da ya warware matsalolin fasaha a jere, yanzu yawan irin wannan shinkafar da a kan yi girbi a ko wane Mu, wato misalin murabba'in mita 670 ya kai kilogram dari 8, wanda ya ninka sau biyu bisa na shinkafa da mu kan gani kullum. Mr. Yuan ya ce,"A da burina shi ne samun nasarar samar da wannan shinkafa mai aure da ta kara yin yalwa. Amma ban yi tsammanin cewa, irin wannan shinkafa ta iya samar mana shinkafa mai yawan haka ba."

Sakamako da yawa da kasar Sin ta samu a fannin nazarin shinkafa mai aure sun taimake ta samun karin shinkafar da yawanta ya kai misalin ton miliyan 600. A sakamakon ci gaba kimiyya da fasaha, kasar Sin ta samar wa kasashen duniya wani abun al'ajabi ta fuskar noman hatsi. Ta ciyar da mutanen da jimillarsu ta kai kashi 22 cikin dari bisa ta duk fadin duniya ta hanyar yin amfani da gonakin da fadinsu ya kai kashi 7 cikin dari bisa na duk fadin duniya. Ban da wannan kuma, fasahar kasar Sin kan shinkafa mai aure ta yadu zuwa kasashe da yankuna fiye da 20.

A hakika, a nan kasar Sin, cikin sauri aka yi amfani da sakamakon da masu ilmin kimiyya da yawa suka samu domin kawo albarka. An yi amfani da su wajen raya tattalin arziki da zaman al'ummar kasa. Muhimmin dalilin da ya sa haka shi ne a cikin shekaru 60 da suka wuce, kasar Sin na kara mai da hankali kan ganin kimiyya da fasaha na taka muhimmiyar rawa.

Xu Heping, darektan ofishin harkokin nazari na ma'aikatar kimiyya da fasaha ta kasar Sin ya yi nuni da cewa,"Kasarmu ta kara rage gibi a tsakaninta da matsayin ci gaban duniya ta fuskar kimiyya da fasaha. A wasu fannoni kuma, tana kan gaba a duniya. Ta inganta tasirinta kan bunkasuwar kimiyya da fasaha ta kasa da kasa cikin sauri. Kimiyya da fasaha sun aza wa kasar Sin harsashi mai inganci wajen bunkasa tattalin arziki da zaman al'ummar kasa da kuma tabbatar da tsaron kanta."

Jama'ar Sin na cin gajiyar bunkasuwar kimiyya da fasaha ainun a zaman rayuwarsu. Ma Qin, wadda ke zaune a gundumar Qinglanshan ta lardin Gansu na kasar Sin ta fahimci wannan sosai. Hanyar zamani ta fuskar noma da reno ta kyautata zaman rayuwarta da sauran 'yan gundumarta sannu a hankali. Kazalika kuma, yanzu daruruwan iyalan mazauna gundumar Qinglanshan sun kafa wuraren renon dabbobin gida na zamani, ta haka suna iya isar da kazantar mutane da ta dabbobin gida a 'yan kananan tabkunan samar da makamashin gas da ke karkashin wadannan wuraren renon dabbobin gida na zamani, inda kazantar ta kan ruba, daga baya kuma, a kan samu makamashin iskar, wadda ake yin amfani da ita tamkar makamashi. Ruwan da ya yi saura bayan samar da makamashin iskar kuwa, a matsayinsa na taki, ana yin jigilarsa zuwa gonaki. Ma Qin ta gaya mana cewa,"A ko wace shekara za mu yi tsimin kudin sayen makamashi da yawansa ya kai yuan dubu 2 zuwa dubu 3. Muna yin amfani da ciyawar shinkafa da ta masara da dai sauransu domin renon dabbobin gida, a maimakon kone su. Yanzu muna iya yin tsimin kome da kome."

Dadin dadawa kuma, fasahar yanar gizo ta Internet da take samun saurin ci gaba ta ba gwamnatin Sin karin taimako wajen kyautata hidimomin jin dadin jama'a. Yau da shekaru 5 da suka wuce, kasar Sin ta kaddamar da aikin ba da ilmi ga 'yan makarantar firamare da midil a kauyuka ta hanyar internet. Makarantun da yawansu ya kai kashi 80 cikin dari a kauyuka sun ci gajiyar aikin. A ganin Li Xiang, wani dan makarantar firamare ta garin Huizhai a lardin Guangdong da ke kudancin kasar Sin, irin wannan hanyar zamani ta inganta sha'awarsa kan koyon ilmi, inda ya ce,"Ina koyon ilmi ta wannan hanyar zamani ne kamar ina kallon sinima, akwai hotunan kwaikwayo da murya. Darussa na da ban sha'awa ainun."

An nuna saurin ci gaban kimiyya da fasaha da kasar Sin ta samu a cikin shekaru 60 bayan kafuwar sabuwar kasar Sin baki daya a yayin gasar wasannin Olympic ta Beijing a shekarar bara. Abubuwan kimiyya da fasaha sun shafi dukkan fannonin gasar. An yi amfani da sakamakon sabuwar fasaha a fannonin gina filin wasa da aikin sadarwa da zirga-zirga da ingancin abinci da yin hasashen yanayi da tsaron lafiyar al'umma da dai sauransu, ciki har da bikin bude gasar wasannin Olympic ta Beijing, wanda a ganin wasu, aka hada ruhun wasan Olympic da kimiyya da fasaha ta zamani tare yadda ya kamata. Mehmet Ali Sahin, tsohon ministan harkokin wasannin motsa jiki na kasar Turkiyya ya bayyana cewa,"Na taba halartar bukukuwan bude gasannin wasannin Olympic da dama, amma a ganina, bikin bude gasar wasannin Olympic ta Beijing ya fi saura kayatarwa. Haka kuma, an fi yin fice wajen yin amfani da fasahar zamani a yayin wannan biki."

A gabannin ranar cika shekaru 60 da kafuwar sabuwar kasar Sin, mutane na da dalilin da ya sa su gaskata cewa, kimiyya da fasaha za su kawo wa zaman rayuwarsu karin farin ciki da mamaki. Saboda a nan kasar Sin, masu ilmin kimiyya da yawa suna yin kokari domin kara kai wa babban matsayi ta fuskar fasaha, kamar yadda masanin ilmin shinkafa Mr. Yuan Longping yake yi. Mr. Yuan ya ce,"Makasudinmu na yin gwajin noman shinkafa mai aure a rukuni na 3 shi ne samun shinkafar da yawanta zai kai kilogram dari 9 a ko wane Mu. Ina cike da karfin zuciya. Na yi shirin cimma wannan buri a shekarar 2010."(Tasallah)