A watan Afrilu na shekarar da ake ciki, gwamnatin kasar Sin ta bullo da wani sabon shirin yin gyare-grare kan tsarin yin jiyyar jama'a. Bisa wannan shiri, za a yi kimanin shekaru 3 wajen kafa tsarin ba da tabbacin yin jiyya a matakin farko da zai shafi duk fadin kasar Sin, kuma za a yi kokarin kyautata ingancin ba da aikin jiyya da kuma rage yawan kudaden da mazauna suke kashewa a fannin kiwon lafiya. Sabo da haka, bisa wannan sabon shiri, a cikin shekaru 3 masu zuwa, gwamnatin kasar Sin za ta zuba kudaden da yawansu zai kai kudin Sin yuan biliyan 850 a fannonin ayyukan yau da kullum na kiwon lafiya da kyautata sharuda da muhallin yin jiyyar jama'a.
A kwanan baya, a gun wani taron manema labaru da ofishin yada labaru na gwamnatin kasar Sin ya shirya, Mr. Wang Jun, mataimakin ministan harkokin kudi na kasar Sin ya bayyana yadda ake amfani da wadannan kudi biliyan 850. Mr. Wang ya ce, "Za a tabbatar da ganin an yi amfani da galibin wadannan kudi a kananan hukumomi, musamman a kananan hukumomin da ke tsakiya ko yammacin kasar domin cimma daidaito a tsakanin yankunan gabas da na yammacin kasar a fannin kiwon lafiya. Amma a waje daya, gwamnatin tsakiya za ta samar da tallafin kudi ga yankunan gabashin kasar. Wannan mataki yana dacewa da manufar sanya tsarin kiwon lafiya a matakin farko ya zama ayyukan yau da kullum da za a samar wa jama'a."
Yaya za a iya daidaita matsalar da dole ne sai marasa lafiya sun biya kudi da yawa lokacin da suke ganawa da likitoci, wannan yana jawo hankalin jama'a. Wani dalilin da ya sa marasa lafiya suke biyan kudi da yawa shi ne farashin magani ya yi tsada ainun. A nan kasar Sin, galibin asibitoci sun fi son sayar da magunguna masu tsada domin neman karin riba. A waje daya, sabo da ba a iya samun riba da yawa daga magunguna masu arha, masana'antun yin magunguna ba su son yin irin wadannan magunguna masu arha, asibitoci ma ba su son yin amfani da su. Sakamakon haka, marasa lafiya su kan biya kudi da yawa domin sayen magunguna masu tsada sosai.
Bisa gyare-gyaren da za a yi kan tsarin kiwon lafiya, kasar Sin za ta kafa wani tsarin tabbatar da samar da magungunan yau da kullum masu arha ga jama'a. Bugu da kari kuma, za a dauki karin matakan sa ido kan farashin magunguna. A yayin wani taron manema labaru da ofishin yada labaru na gwamnatin kasar Sin ya shirya, Mr. Peng Sen, mataimakin shugaban kwamitin yin gyare-gyare da ci gaban kasar Sin ya ce, "Za a daidaita ire-iren magungunan da hukumomin gwamnati za su sa ido kan farashinsu. Wato musamman za a kara sa ido kan farashin magungunan da ake amfani da su a kullum. Sannan za a kara sa ido kan ribar da ake samu kan irin wadannan magunguna na yau da kullum domin rage ribar da hukumomin kiwon lafiya suke samu. Haka kuma, za a kara sa kaimi ga asibitoci da su yi amfani da irin wadannan magunguna masu arha domin rage nauyin da ke kan marasa lafiya. Kana kuma, kananan hukumomin kiwon lafiya da gwamnatoci a matakai daban daban suka kafa ba za su iya neman samun riba daga irin wadannan magunguna ba. A waje daya, muna fatan asibitocin gwamnati za su kuma yi gwajin rashin riba. Muna fatan za a iya warware matsalar biyan kudi da yawa da marasa lafiya suke fuskanta."
Wani dalili na daban da ya sa jama'a suke biyan kudi da yawa lokacin da suke ganawa da likita shi ne babban tsarin kiwon lafiya bai iya gama duk fadin kasar Sin ba tukuna, kuma yawan kudin da gwamnati ta kebe bai iya biyan bukatun da ake nema ba. Yanzu tsarin ba da inshorar kiwon lafiya ga ma'aikatan hukumomi da na kamfanoni da tsarin inshorar kiwon lafiya ga mazauna birane da sabon tsarin ba da inshorar kiwon lafiya cikin hadin gwiwa ga mazauna kauyuka su ne manyan tsare-tsaren inshora mafi muhimmanci a kasar Sin. Wadannan manyan tsare-tsaren inshora suna shafar mutanen da yawansu ya kai kimanin biliyan 1.1, amma sauran mutane kimanin miliyan dari 2, ciki har da wasu dalibai da mazauna marasa aikin yi da manoma 'yan ci rani a birane ba su iya samun ribar wadannan manyan tsare-tsaren inshorar kiwon lafiya ba. Sannan lokacin da kasar Sin take kawar da tsarin raya tattalin arziki bisa shiri, kuma take raya tattalin arziki irin na kasuwanci, yawan kudin da gwamnatin kasar Sin ta kebe wa hukumomin kiwon lafiya ya ragu, amma yawan kudaden da jama'a suke kashewa a fannin kiwon lafiya ya karu cikin sauri. Sakamakon haka, yaya dukkan mazauna kasar Sin za su iya samun moriya daga babban tsarin kiwon lafiya ya zama wata babbar matsalar da ke gaban gwamnatin kasar Sin.
A cikin sabon shirin yin gyare-gyare kan aikin kiwon lafiya, za a kara yawan mutanen da za su iya samun moriya daga sabon babban tsarin kiwon lafiya. A waje daya, za a samar wa mazauna da karin kudin kiwon lafiya. Mr. Hu Xiaoyi, mataimakin ministan kula da albarkatun 'yan kwadago da ba da tabbaci ga jama'a na kasar Sin ya ce, "Daidaita matsalar biyan kudin kiwon lafiya da yawa da jama'a suke fuskanta wani aiki ne mai sarkakiya. Da farko dai, za a kara yawan mutanen da za su iya samun moriya daga sabon babban tsarin kiwon lafiya. Shi ne wani muhimmin aikin da za mu yi a cikin shekaru 3 masu zuwa. Za mu sanya dukkan mazauna kasar Sin su samu tabbacin kiwon lafiya. Kuma za a iya rage yawan kudin da marasa lafiya suke kashewa domin ganin likita. A waje daya, za a samar da karin kudi domin tabbatar da aiwatar da manyan tsare-tsaren ba da tabbaci guda ukku, wato za a kayyade yawan kudin da marasa lafiya za su biya, kuma za a mayar wa marasa lafiya bangaren kudin da suka kashe. Sannan za a kara jimillar kudin ga babban tsarin ba da tabbacin kiwon lafiya ga jama'a. A lokacin da ake samun ci gaban tattalin arzikin kasar, gwamnatin kasar Sin za ta samar da karin tallafin kudi ga mazauna da manoma wadanda suka halarci babban tsarin inshorar kiwon lafiya."
A lokacin da ake sa kaimi ga dukkan jama'ar kasar da su halarci babban tsarin ba da tabbacin kiwon lafiya, bisa wannan sabon shiri, za a yi kokarin shigar da jari mai zaman kansa a asibitocin da ba na neman riba ba. Kuma za a tabbatar da ganin dukkan hukumomin kiwon lafiya sun yi takara cikin adalci. Sannan za a rage yawan harajin da ake bugawa kan asibitocin da ba na neman riba ba. Kana kuma bisa sabon shirin yin gyare-gyare kan tsarin kiwon lafiya, za a mayar da wasu asibitocin gwamnati da su zama asibitoci masu zaman kansu. Masana suna ganin cewa, wannan manufa za ta iya shigar da takara a tsakanin hukumomin kiwon lafiya. Mr. Guo Bo, babban direktan kamfanin sayar da magunguna na fararen hula da ke birnin Beijing ya ce, "A da babu irin wannan manufa. Asibitoci masu zaman kansu sun gamu da wahalhalu da yawa, alal misali, likitan da yake aiki a wani asibiti ba zai iya ganawa da marasa lafiya a wani asibiti na daban ba. Amma idan kwararru sun iya shiga kasuwa, ba ma kawai yawan kudin da likitoci suke samu zai iya karuwa ba, har ma asibitoci masu zaman kansu za su iya shiga kasuwa kuma za su iya yin takara a kasuwa cikin adalci."
A cikin dogon lokacin da ya gabata, jama'a fararen hula na kasar Sin su kan nuna damuwa idan sun kamu da ciwo ko sun tsufa. Sakamakon haka, jama'a fararen hula sun fi son ajiye kudinsu a banki. Masana sun nuna cewa, bayan da aka aiwatar da sabon shirin yin gyare-gyare kan manufofin kiwon lafiya a duk kasar, jama'a fararen hula za su iya samun tabbaci a fannin kiwon lafiya. Wannan zai kuma sassauta damuwar da jama'a fararen hula suke nunawa, kuma za su iya kashe kudadensu kamar yadda suke so. Madam Li Ling, mataimakiyar direktan cibiyar nazarin tattalin arziki ta jami'ar Beijing ta ce, "Ba ma kawai shirin yin gyare-gyare kan manufofin kiwon lafiya zai daidaita matsalar biyan dimbin kudi da jama'a fararen hula suke fuskanta ba, har ma zai yi kyakkyawan tasiri ga kokarin tabbatar da lafiyar jama'a fararen hula, kuma zai yi tasiri ga ci gaban tattalin arzikin kasar." (Sanusi Chen)
|