A watan biyar na bana wato shekarar 2009, an yi zama na 11 na gasar cin kofin Surdiman wato gasar kwallon badminton ta duniya tsakanin kungiya kungiya ta gaurayawar namiji da mace a birnin Guangzhou dake kudancin kasar Sin. Kamar yadda kuka sani, gasar cin kofin Surdiman ta hada da gasanni biyar wato gasa tsakanin namiji da namiji da gasa tsakanin mace da mace da gasa tsakanin maza biyu biyu da gasa tsakanin mata biyu biyu da kuma gasa tsakanin namiji da mace da kuma namiji da mace. Idan wata kungiya wadda ta shiga wadannan gasanni biyar ta samu nasara sau uku, to, shi ke nan, sai ta ci nasara ta zama zakara. An sanya gasar cin kofin Surdiman sau daya a duk shekaru biyu, tana da muhimmanci kuma ta yi shahara sosai a duniya, saboda ta nuna mana kasaitaccen matsayin wasan kwallon badminton a duniya.
A yayin wannan gasar da aka shirya a birnin Guangzhou, kungiyoyin da suka zo daga kasashe da shiyyoyi 34 sun taru waje daya a birnin domin yin kara tsakaninsu. Kungiyar kasar Sin wadda ta taba zama zakara a yayin gasar da aka sanya a shekarar 2007 tana da hangen nesa, wato ta samar da damar shiga wannan babbar gasa ga wasu sabbin 'yan wasa matasa kamarsu Wang Lin da Wang Yihan da Ma Jin da sauransu. To, yaya wadannan sabbin 'yan wasa? Ina sakamakon da suka samu bayan da suka shiga wannan gasa? A cikin shirinmu na yau, bari mu yi muku bayani kan wannan.
A cibiyar wasan motsa jiki ta birnin Guangzhou, 'yan kallo sun yi ta shewa domin sa kaimi ga 'yan wasa, kungiyar wasan kwallon badminton ta kasar Sin ta tura 'yan wasa 27 domin shiga wannan gasa, yawan 'yan wasan kasar Sin sun fi yawa, dalilin da ya sa haka shi ne domin an yi wannan gasa ne a kasar Sin, kungiyar kasar Sin ba ta da matsalolin harshe da neman samun visa da kudin tikitin jirgin sama da sauransu. Kuma 'yan wasa 16 dake cikinsu ba su taba shiga irin wannan babbar gasa ta duniya ba. Game da wannan batu, babban malamin horaswa na kungiyar wasan kwallon badminton ta kasar Sin Li Yongbo ya bayyana cewa, idan wani 'dan wasa ya sami damar zuwa wurin gasa, koda yake bai sami damar shiga gasa ba, to, yana da amfani, zai sami ci gaba daga duk fannoni. Li Yongbo ya ce, "A wannan karo, an yi gasar cin kofin Surdiman a gida kasar Sin, shi ya sa halin musamman na babbar gasa ta duniya zai amfanawa 'yan wasa matasa sosai, ko shakka babu, sabbin 'yan wasa za su koyi abubuwa da yawa, musamman ma ga 'yan wasa matasa."
Babban malamin horaswa Li Yongbo ya gaya mana cewa, dalilin da ya sa suke yin kokarin horas da sabbin 'yan wasa matasa a yayin gasar cin kofin Surdiman shi ne domin neman samun babban sakamako a yayin gasar wasannin Olympic ta London. Li Yongbo ya ce, "Gasar wasannin Olympic ta fi muhimmanci, ana yinta sau daya bayan shekaru hudu, makasudin duk kokarin da muke yi yanzu shi ne domin samun sakamako mai gamsarwa a yayin gasar wasannin Olympic, a ko da yaushe, gasar wasannin Olympic burin karshe ne a zuciyata. Yanzu, muna horas da sabbin 'yan wasa matasa, muna fatan matsayinsu zai dagu cikin saurin gaske."
'Yar wasa Wang Yihan ta zo ne daga birnin Shanghai, bana tana da shekaru 21 kawai a duniya, amma, kawo yanzu, ta riga ta zama zakaran duniya sau tarin yawa. Wannan karo na farko ne da ta shiga gasar cin kofin Surdiman, tana yin farin ciki kwarai da gaske, a sa'i daya kuma, tana cikin damuwa, ta ce, "Ina yin farin ciki kuma ina cikin damuwa, musamman ma tun farkon da na fara yin gasa, amma a kai a kai ne jikina ya sassauta."
'Yar wasa Ma Jin ita ma tana da shekaru 21 da haihuwa, ta zo ne daga jihar Jiangsu, wannan shi ma karo na farko da ta shiga wannan babbar gasa. A yayin gasar, ta shiga gasa tsakanin namiji da mace da kuma namiji da mace tare da tsohon 'dan wasa Zheng Bo, a karshe dai, sun lashe abokan gasa daga kasar Japan da 2:0. Ma Jin ta takaita da cewa, "Ina ji tamkar amfanina ya kara muhimmanci, koda yake na shiga gasa tsakanin kungiya kungiya, amma na yi iyakacin kokari."
Cikin dogon lokaci, babban malamin horaswa na kungiyar wasan kwallon badminton Li Yongbo yana mai da hankali kan dauwamammen ci gaban kungiyarsa. A ganinsa, gasa tsakanin kungiya kungiya za ta kara karfafa hakkin 'yan wasa bisa wuyansu, musamman ma ga 'yan wasa matasa. Alal misali, yayin da 'yar wasa Wang Lin wadda ke da shekaru 20 kawai da haihuwa take yin kara da 'yar wasa daga kasar Ingila, da farko dai, ta kama baya da 5:10, daga baya kuma, hankalinta ya kwanta, ta yi wasa yadda ya kamata, a karshe dai ta lashe abokiyar gasa lami lafiya. Li Yongbo ya ce, gudanarwar lamarin tana da muhimmanci. Ya ce, "Muna yin kokarin horas da sabbin 'yan wasa domin shiga gasannin da za a shirya a nan gaba. 'Yan wasa matasa suna iya tattara fasahohi a yayin babbar gasa, shi ya sa, ana iya cewar, irin wannan babbar gasa tana da amfani gare su, nan gaba, za su san yaya za su yi a yayin babbar gasa."
Bayan wannan gasar cin kofin Surdiman, kungiyar wasan kwallon badminton ta kasar Sin za ta karbi wasu sabbin 'yan wasa. Kamar yadda kuka sani, zakarar gasar wasannin Olympic Zhang Ning ta riga ta yi ritaya, kawo yanzu, fitacciyar 'yar wasa Xie Xingfang ta riga ta kai shekaru 28 da haihuwa, za ta yi ritaya cikin shekaru biyu, wato ba za ta shiga gasar wasannin Olympic ta London ba. Ban da wannan kuma, 'dan wasan maza Bao Chunlai da 'dan wasa tsakanin maza biyu biyu Cai Yun da sauran shahararrun 'yan wasa suna fama da ciwo a sanadin wasa, ba su sami ci gaba ba ko kadan. A karkashin irin wannan hali, dole ne sabbin 'yan wasa matasa su kara ba da amfani. A yayin wannan gasar cin kofin Surdiman, sabbin 'yan wasa matasa suna cike da imani kuma karfin yin kara shi ma ya kara karfafuwa a bayyane. Babban malamin horaswa Li Yongbo ya ce, "Yayin da 'yan wasan kasar Sin suke yin gasa tsakanin kungiya kungiya, dukkansu suna yin iyakacin kokari, koda yake muka taba gamu da wahala, amma a takaice dai, muna iya cewa, mun riga mun cim ma babban buri na horas da kanmu."
Ko shakka babu, bayan shekara daya ko biyu, sabbin 'yan wasa za su zama sabbin zakaru a dandalin wasan kwallon badminton na duniya. (Jamila Zhou)
|