Watakila kun sami labarin, mahaukaciyar guguwa a karo na takwas a bana mai suna Morak ta iso yankin kudancin kasar Sin, wato lardin Zhejiang da Fujian da Anhui da Jiangsu da sauransu, wadda ta janyo manyan hasarori ta fannin rayukan jama'a da tattalin arziki. Kawo yanzu dai, ana gudanar da aikin ceto yadda ya kamata. Dadin dadawa, a ran 10 ga wata, mataimakin firaministan Sin Hui Liangyu ya kai ziyara a lardin Fujian da Zhejiang da sauransu, a yunkurin ba da jagoranci ga aikin ceto.
To, game da lamarin kuma, kwanan baya mun samu wani sako daga malam Musa Adamu a Gombe ta yanar gizo, wato internet da cewar, "Assalam alaikum. Dangane da labarin da muka ji a wasu kafofin watsa labarai na irin bala'in da ya auku na rushewar gidaje sabo da ruwan sama, kungiyar Jeyrala ke mika jajantawa da alhininta ga irin hasarar da aka yi, da kuma fatan Allah ya kiyaye a nan gaba."
To, mun gode, malam Musa Adamu, sabo da jajantawa da alhini da ka mika mana. Yanzu ana gudanar da aikin ceto yadda ya kamata kamar yadda muka ambata a baya. Lalle, 'yan uwanmu sun sha wahalhalu masu dimbin yawa. Amma ko shakka babu za mu cimma nasarar yaki da mahaukaciyar guguwar Morak tare da sake gina wadannan wurare.
To, sakon malam Musa Adamu ke nan. Kwanan baya, malam Lawal Ibrahim, wani dan Nijeriya ya aiko da wata tambaya dake cewa, "Don Allah ku ba ni tarihin kungiyar Boko Haram ta Nijeriya." To, yanzu za mu kokarta amsa wannan tambaya.
A: Bayan musanyar wuta mai tsanani ta tsawon kwanaki uku, a ran 29 ga watan Yuli, sojoji masu kwantar da kura na Nijeriya sun kwantar da tashe-tashen hankali da wasu masu tsattsauran ra'ayin addinin Musulunci suka tayar. Da farko an tada zaune tsaye a jihar Bauchi dake arewa maso gabashin Nijeriya, daga bisani, tashe-tashen hankali sun shafi jihohi uku dake kewaye, wato jihar Borno da Yobe da Kano, wadanda suka yi sanadiyyar mutuwar mutane sama da 300. To, mene ne dalilin abkuwar wadannan tashe-tashen hankali? Ko za su yi illa ga Nijeriya? Yanzu za mu buga waya ga wakilinmu Wei Xiangnan dake Lagos,Nijeriya, don ya ba mu bayani. Assalamu alaikum, don Allah ka ba mu dalilin abkuwar wannan tashin hankali.
B? To, madallah, wata kungiya mai tsattsauran ra'ayin addinin musulunci da ake kira "Taliban ta Nijeriya" ko "Boko Haram" ta tada zaune tsaye. A ranar 26 ga watan Yuli, wasu membobin kungiyar Boko Haram sun hallara a kewayen ofishin 'yan sanda a birnin Bauchi, hedkwatar jihar Bauchi tare da makamai, a yunkurin samun ikon gudanar da gagarumar zanga-zanga, ta yadda za su iya yada ra'ayinsu na komawa addinin musulunci na tsantsa ga jama'a. Bayan da gwamnatin jihar Bauchi da 'yan sanda suka nuna ra'ayinsu na ki amincewa da lamarin, wasu mutane sun bude wuta ga 'yan sanda. Daga bisani an yi musanyar wuta tsakanin bangarorin biyu. Daga karshe dai, dakarun sun janye jiki bayan da 'yan sanda da sojojin kwantar da kura suka mai da martani mai tsanani. Amma a ran 27 ga watan Yuli, dakarun sun sake tada zaune tsaye a jihohin Yobe da Kano da Borno a sakamakon zugar shugaban kungiyar Mohammed Yusuf. Sun cunna wuta ga ofishin 'yan sanda da gine-ginen gwamnati da sauran manyan ayyukan jama'a, tare da yin musanyar wuta da 'yan sanda da sojojin. Hakan ya yi sanadiyyar mutuwa da raunata mutane da yawa, yayin da wasu sama da dubu suka rasa gidajensu.
A: To, yanzu ko za ka gabatar mana da tarihin kungiyar Boko Haram dake Nijeriya?
B: Kungiyar Taliban ta Nijeriya, ko Boko Haram wata kungiya ce mai tsattsauran ra'ayin addinin Musulunci. An kafa ta a shekarar 2004, kuma hedkwatarta a birnin Maiduguri, hedkwatar jihar Borno ta Nijeriya. Mafi yawan membobin kungiyar dalibai ne da suka katse karatunsu a jami'o'i. Suka yi watsi da karatun boko, kuma sun dora niyyar kafa kotunan shari'a a duk jihohin Nijeriya 36, tare da kafa wata kasar musulmi a arewacin Nijeriya. Bugu da kari, kungiyar ta kafa wani sansani a jihar Yobe, inda su kan yi tarzoma da 'yan sanda. Sabo da ra'ayin kungiyar ya tashi daya da na kungiyar Taliban dake Afghanistan, shi ya sa 'yan Nijeriya suka rada mata sunan kungiyar "Taliban ta Nijeriya" ko boko haram. 'Yan Nijeriya ba su amince da danyun ayyuka da kungiyar take yi ba. Bayan abkuwar tashe-tashen hankali, kungiyoyin addini da na zaman al'umma na Nijeriya sun gabatar da sanarwoyi, a yunkurin yin suka ga wadannan danyun ayyuka, da kuma yin kira ga kungiyoyin addinin Musulunci dake Nijeriya da su zauna tare cikin lumana. A ran 28 ga watan Yuli kuma, mataimakin kakakin babban sakataren MDD Farhan Haq ya bayyana cewa, babban sakataren MDD Ban Ki-moon ya yi Allah wadai da wannan danyen aiki. Ya bukaci mahukunta na Nijeriya da su yi bincike kan wadanda suka tsara wannan tashin hankali da kuma gabatar da su a gaban kotu tun da wuri.
A: To, wane irin mataki ne mahukunta na Nijeriya suka dauka a kokarin kawo karshen tashe-tashen hankali?
B: Ta la'akari da yanayi mai tsanani, a ranar 28 ga watan Yuli, shugaban Nijeriya Umaru Yar'Adua ya ba da umurni ga hukumar tsaron kasa, inda ya bukaci hukumar da ta dauki kwararan matakai domin yaki da masu tsattsauran ra'ayin addini. Kuma bisa kokarin 'yan sanda da sojoji masu kwantar da kura na Nijeriya, yanzu an shawo kan tashe-tashen hankali a kasar.
A: To, mun gode wakilinmu Wei Xiangnan. Bayan haka kuma, a ran 30 ga watan Yuli, gwamnatin Nijeriya ta tabbatar da mutuwar shugaban kungiyar Boko Haram Mohammed Yusuf. Wani mai magana da yawun gwamnatin jihar Borno ya ce, 'yan sanda sun harbe shi ne a yayin da yake yunkurin tsira.
To, bayaninmu ke nan ga tambayar malam Lawal Ibrahim, kuma da fatan ka ji ka gamsu da shi.
Bayan haka kuma, kwanan nan, mun sami sakwannin gaishe-gaishe daga wajen malam Namadina Yahya daga Senegal da malam Ibrahim Gyaranya daga Nijeriya da dai sauransu, wadanda ba mu iya karanta sakwanninsu duka ba sabo da karancin lokaci, amma muna godiya a gare ku, kuma Allah ya karfafa dankon zumunci a tsakaninmu.
|