Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-08-11 09:41:19    
Gasar wasannin Olympic ta Beijing a tunanin wani dan jaridar Zimbabwe

cri

Masu karatu, barka da war haka! Ran 1 ga watan Oktoba na wannan shekara, rana ce ta cika shekaru 60 da kafuwar jamhuriyar jama'ar kasar Sin, dan haka, tun daga yau sashen Hausa na gidan rediyonmu za mu gabatar muku da wani shirin musamman a ran Talata da ta Jumma'a a ko wane mako. Ni ce Tasallah da ke yi muku marhabin cikin wannan shiri.

Ran 8 ga watan Agusta na shekarar da muke ciki, rana ce ta cika shekara guda da bude gasar wasannin Olympic ta Beijing. Gasar wasannin Olympic da aka yi a nan Beijing, hedkwatar kasar Sin a shekarar bara ta faranta rayukan biliyoyin Sinawa matuka, har ma ba za su iya mantawa da ita ba har abada. Haka kuma, gasar wasannin Olympic ta Beijing ta shiga cikin zukatan baki masu tarin yawa. Goodwill Zunidza, shugaban sashen labarun wasannin motsa jiki na jaridar Sunday Mail ta kasar Zimbabwe ya taba kawo wa kasar Sin ziyara har sau 2 a shekarar da ta wuce bisa gayyatar da cibiyar watsa labaru ta kasa da kasa ta Beijing ta shekarar 2008 ta yi masa, ya kuma tattara labaru kan gasar wasannin Olympic ta Beijing kai tsaye.

A kwanan baya, Goodwill ya zanta da wakilinmu a Zimbabwe, inda ya waiwayi abubuwan da suka auku a lokacin da yake tattara labaru kan gasar wasannin Olympic ta Beijing. Ya bayyana cewa, ba zai iya mantawa da gasar wasannin Olympic ta Beijing ba. Har ma kamar a ce ya bar zuciyarsa a birnin Beijing.

Goodwill yana shugabantar sashen labarun wasannin motsa jiki na jaridar Sunday Mail, wadda jarida ce mafi girma da ake bugawa sau daya a ko wane mako a kasar Zimbabwe. A shekarar da ta gabata, ya taba zuwa birnin Beijing sau 2 domin tattara labaru kan gasar wasannin Olympic ta Beijing. Dangane da abubuwan da suka faru a kansa a birnin Beijing, ya zuwa yanzu dai Goodwill ya yi zumudi sosai. Yana mai cewar,"Abin da nake so in gaya muku shi ne, na bar zuciyata a birnin Beijing, ban koma gida tare da zuciyata ba. Da isowata birnin Beijing, wannan birni mai girma ya girgiza ni sosai. A wancan lokaci, ina tsammani cewa, tabbas shi ne birni mafi girma a duk duniya. Na taba ganin biranen New York da Washington da kuma London a telibijin da kuma fina-finai, ko da yake ban taba zuwa wadannan birane ba tukuna, amma a ganina, ba za a iya kwatanta su da birnin Beijing a fannonin girma da kwarewar jawo hankalin mutane da muhumman ayyukan al'umma ba."

Kasar Zimbabwe, wata kasa ce mai tasowa. Ko da yake jaridar Sunday Mail tana zama kan gaba a duk kasar Zimbabwe, amma ta dade tana fama da matsalar karancin kudi domin aika wakilanta su tattara labaru kan gasar wasannin Olympic kai tsaye. Goodwill yana ganin cewa, ya taki sa'a ainun. Saboda a shekarar bara, cibiyar watsa labaru ta kasa da kasa ta Beijing ta shekarar 2008 da hukumar birnin Beijing ta kafa ta ba shi dukkan kudin tattara labaru kan gasar wasannin Olympic ta Beijing, ta haka bai gamu da matsala ko kadan a lokacin da yake tattara labaru a birnin Beijing ba a shekarar bara. Goodwill ya ce,"Wannan shi ne karo na farko da na sami damar tattara labaru kan gasar wasannin Olympic kai tsaye. A kasarmu ta Zimbabwe, da wuya ne sosai mu sami damar tattara labaru kan gasar wasannin Olympic kai tsaye. Jaridarmu ta Sunday Mail ba ta taba tura wakilai su tattara labaru kan gasar wasannin Olympic kai tsaye a da ba. Amma a shekarar bara, kasar Sin ta ba mu taimako da yawa. Ta taimake ni wajen tattara labaru kan gasar wasannin Olympic ta Beijing. A da, kasashen da suka shirya gasar wasannin Olympic ba su yi tunanin bai wa kasashen da suka gaza wajen tura manema labaru domin tattara labaru kai tsaye dama ba. Duk da haka, a shekarar bara, kasar Sin ta kaddamar da cikakken shirin samar da zarafi gare mu, ta haka manema labaru da yawa da suka fito daga kasashen Afirka sun samu zarafin tattara labaru kai tsaye a kasashen da suka shirya gasar wasannin Olympic."

A lokacin da yake birnin Beijing, Goodwill ya kalli bikin bude gasar wasannin Olympic ta Beijing kai tsaye, ya kuma tattara labaru kan wasu gasannin da bai san su sosai ba. Sa'an nan kuma, masu aikin sa kai da suka ba da hidima mai kyau da kuma filayen wasa masu kyan gani sun burge shi kwarai, inda ya ce,"Bayan da na dawo gida, na rubuta wani bayani mai lakabi haka 'Wannan ita ce gasar wasannin Olympic mafi kyau', inda na yi amfani da kalmomin shugaban kwamitin wasan Olympic na kasa da kasa. Shugaban kwamitin shirya gasar wasannin Olympic ta London shi ma ya ce, da wuya ne matuka za a shirya gasar wasannin Olympic da za ta fi wadda aka yi a Beijing kyau. A ganina, masu aikin sa kai kimanin miliyan 1 sun ba da taimako a cikin filayen wasa da kuma waje da su. In ka tambayi hanya, ko kuma ka nemi sanin sauran labaru, kullum kana iya samun tallafi daga wajen wadannan masu aikin sa kai. Kazalika kuma, dakin wasan ninkaya na kasar Sin wato 'Water Cube' ya jawo hankalin mutane sosai, inda kuma aka karya matsayin bajimta da yawa. Dalilin da ya sa haka shi ne Sinawa sun share fage sosai."

Bugu da kari kuma, game da gasar wasannin Olympic da aka yi a birnin Beijing a shekarar da ta gabata, Goodwill bai manta da kirkin Sinawa ba, wadanda suke son karbar baki. Goodwill ya ce,"Mutanen Sin na da kirki kwarai da gaske. Su mutane ne masu fara'a kuma masu son karbar baki. Suna Alla-Alla wajen taimakawa wasu. Mutanen Sin suna da ilmi, an ilmantar da su yadda ya kamata. Kuma sun kara imani, ba su bi al'adun kasashen waje kwata-kwata ba, a maimakon haka, sun darajta al'adun kasarsu sosai."

A lokacin da yake waiwaya abubuwan da suka auku yau da shekara guda da ta wuce, Goodwill ya mayar da zuwa kasar Sin domin tattara labaru tamkar dukiya ce da take ba shi taimako a duk tsawon rayuwarsa. Ziyarasa a kasar Sin ba kawai ta zurfafa fahimtarsa kan wasannin motsa jiki ba, har ma ta bude masa wata kofa ta kara sanin al'adun kasar Sin, wannan shi ne abu mai muhimmanci da ya samu daga tattara labaru kan gasar wasannin Olympic ta Beijing. Goodwill ya nuna cewa,"Ziyarata a kasar Sin a shekarar bara ta bude mini ido sosai, ta ba ni sabuwar hanyar kara fahimtar wasannin motsa jiki. A ganina, na dawo gida ne tare da wani irin al'adu na daban. Al'adun kasar Sin sun ba ni taimako matuka wajen gudanar da ayyuka. Ya zuwa yanzu dai na ci gajiyar al'adun kasar Sin sosai. Tsayawa tsayin daka kan koyon al'adun kasar Sin ya sanya na kara sanin wasannin motsa jiki. A takaice dai, ziyarata a birnin Beijing a shekarar da ta gabata ta kyautata kwarewata wajen jin dadin kallon wasannin motsa jiki. Ina fatan nan gaba in sami karin damar tattara labaru kan gasanni."(Tasallah)