A ran 5 ga wata da dare, shugaban kasar Venezuela Hugo Chavez ya bayyana cewa, sabo da Amirka ta yi ta yin barazana ga kasarsa ta hanyar tura sojojinta zuwa kasar Colombia, kasar dake makwabtaka da ita, shi ya sa gwamnatin Venezuela za ta sayi tankoki da dama daga kasar Rasha domin tsaron kasar, al'amarin nan ya kara lalata dangantakar tsakanin kasashen 2 wadda da ma ta samu dan inganta.
Cikin jawabin da Chavez ya yi a ran nan da dare ta talabijin ya bayyana cewa, a tsakiyar watan Satumba na wannan shekara Venezuela za ta sa hannu kan yarjejeniyar jan damara a tsakaninta da Rasha, wadda take hade da sayen makaman fada, da taimakawa sojojin kasar domin kara karfin daga, da kuma inganta tsarin tsaron kasar, da yin adawa da farmakin da za a kai mata daga sararin sama. Chavez ya kuma ce, dazu ya zanta da Vladimir Putin, firaministan kasar Rasha ta wayar tarho, cikin waya Putin ya bayyana kyakkyawan fatan ganawar juna da za su yi a watan Satumba mai zuwa.
Manazarta sun bayyana cewa, aikin sayen makamai da Venezuela ta yi a wannan gami ya zama martani ne da ta mayar ga Colombia wadda ta lamuci Amirka da ta kafa sansanonin soja da dama a yankunanta, bisa yarjejeniyar da aka daddale tsakanin Colombia da Amirka an ce, bayan wa'adin iznin da Amirka ta samu wajen yin amfani da sansanonin soja a kasar Ecuador ya cika, Colombia ta yarda da Amirka da ta kawar da mutane da na'urori zuwa cikin yankunanta, kuma ta amince da Amirka da ta kafa sansanonin soja da dama da kara jabge mutane zuwa cikin kasar. Sabo da haka ba shakka Venezuela ta maida martani ga lamarin.
Cikin shekaru 10 da suka gabata, yawan kudin da Venezuela ta ware domin sayen makamai daga Rasha ya kai dala biliyan 3. Kwanan baya Chavez ya bayyana cewa, kasarsa ba ta son sayen tarin makamai ta yadda za a jawo gasar jan damara, amma abun da ya zame mata tilas ga yin haka shi ne sabo da Colombia ta yarda da Amirka da ta jibge sojojinta zuwa cikin yankunanta.
Manazarta sun bayyana cewa, maganar da Chavez ya yi ta nuna bacin ransa ga Barack Obama, shugaban kasar Amirka. Bayan da Obama ya dara kan karagar mulki a watan janairu na wannan shekara, ya taba kyautata danganatar da ke tsakaninta da kasashen Latin-Amirka, kasashe masu sassaucin ra'ayi ciki har da Venezuela da Ecuador da Cuba su ma sun rage yawa zarge- zargensu gare ta. A gun taron shugabannin kungiyar kasashen nahiyar Amirka da aka yi a watan Afril na wannan shekara, Obama da Chavez sun taba yin musahafa da juna har sau 3, kuma sun yi zantakaya da juna cikin halin aminci, Chavez ya kuma gaya wa Obama cikin Turanci cewa, "Ina son kulla abuta da kai". Ban da wannan kuma kasashen 2 sun sake aika wa junansu jakadu, ta yadda suka mayar da huldar jakadanci yadda ya kamata a tsakaninsu. Amma cikin wata daya da ya wuce, an yi abubuwa 3 bi da bi wadanda suka sa dangantaka da ke tsakanin kasashen 2 ta lalace sosai. Da farko, a ran 28 ga watan jiya an kifar da Zeyala, shugaban kasar Honduras, kuma abokin arzikin Chavez wajen siyasa daga kan mukaminsa, Chavez ya zargi Amirka bisa laifinta na sarrafa al'amarin nan a baya. Daga bisani kuma majalisar dokoki ta Amirka ta kaddamar da rahoto wanda ya zargi gwamnatin Venezuela wai tana zuga 'yan fasa-kwaurin miyagun kwayoyi. Ga shi yanzu Amirka za ta kafa sansanonin soja da dama a kasar Colombia, al'amarin nan ya kara fusata Chavez sosai, ya bayyana cewa, wadannan al'amura sun bayyana cewa, bayan Obama ya dara kan karagar mulki, Amirka tana ci gaba da jawo kiyayya ga Venezuela. Manazarta sun bayyana cewa, yanzu dangantakar da ke tsakanin Amirka da kasashen Latin-Amirka tana fuskantar sabon kalubale. (Umaru)
|