Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-08-05 15:02:39    
Bayani kan kaddarar dake tsakanin 'dan kasuwa Zhang Mingfu da kauyukan Sin

cri
Kafin ranar bikin 'yan kwadago ta duniya a kowace shekara, gwamnatin Sin ta kan yaba wa 'yan kasuwa da ma'aikata da suka yi aiki da kyau. A cikin wadanda suka samu yabo a bana, da akwai wani dan kasuwa mai suna Zhang Mingfu da ya zo daga birnin Zunyi na lardin Guizhou dake kudu maso yammacin kasar Sin. Zhang Mingfu ya kafa sabbin masana'antu yayin da ake rufe masana'antu sakamakon matsalar kudi ta Asiya, kuma ya yi watsi da masana'antun da za su kawo masa riba da yawa, maimakon haka, ya kafa kamfanonin sarrafa kayan abinci a kauyuka masu nisa, kana ya yi bincike kan batutuwan kauyuka wadanda ba su da nasaba da bunkasuwar masana'antu. Duk da ana ganin cewa wannan 'dan kasuwa yana nuna wauta, amma firayim ministan kasar Sin Wen Jiabao ya nuna babban yabo gare shi. A cikin shirinmu na yau, za mu gabatar muku da wani bayani kan yadda wannan 'dan kasuwa ya yi aiki a kauyukan kasar Sin.

An haifi Zhang Mingfu a shekarar 1962, yanzu ya riga ya zama mashahurin mutum a garinsa wato lardin Guizhou. Kamfanoni biyu da Zhang Mingfu ya kafa wato kamfanin sarrafa kayan ado da na kiwon kaji sun kawo masa riba da yawa. Sabo da haka, yawan kudin da Zhang Mingfu ya samu ya wuce miliyan dari. Ya zuwa yanzu, Zhang Mingfu shi wakili ne na majalisar wakilan jama'a ta lardin Guizhou, kuma shi tauraro ne na wadanda suka kafa kamfani masu zaman kansu na kasar Sin, kuma shi manomi ne da ya kafa masana'antu. Zhang Mingfu ya fi son a dinga kiransa manomi mai kafa masana'antu.

"A lokacin da, gidana ya fi talauci sosai. Yayin da nake yin karatu a karamar makarantar midil, ina iya sa takalma cikin wata daya ne kawai a yanayin dari, amma a sauran lokuta, ba na iya sa takalmai duk da ina karatu ko aiki. Ban da wannan kuma, ba mu da isasshen abinci. Idan mun ci abinci da safe, ba za mu ci abinci da yamma ba. A wancan lokaci, mahaifina ya kan ari kudi daga sauran makwabta. A wata rana ma, ba mu samun abinci, kuma ba ni da kudin yin karatu, dole tasa na daina yin karatu."

A shekaru 80 na karnin da ya gabata, Zhang Mingfu wanda ya daina yin karatu bayan watanni biyu na yin karatu a makarantar midil yana son kafa kamfani mai zaman kansa, amma ba shi da jari. A cikin shekaru bayan haka, Zhang Mingfu ya yi aikin dako da na fenti, kuma ya dinga yin kankanan ciniki. Sakamakon kokarin aikin da ya yi cikin shekaru goma, Zhang Mingfu yana da kudin Sin yuan miliyan biyu wanda ya zama jarinsa na farko na kafa kamfaninsa.

A shekarar 1998, matsalar kudi ta barke a Asiya, kamfannoni da dama da suke sarrafa kayan ado a yankin gabar teku na kasar Sin sun yi hasara mai tsanani, kuma an rufe kamfanoni da yawa. Amma Zhang Mingfu ya hada kai da wani kamfani na Hongkong, kuma sun kafa wani kamfani mai suna "Meng Liya" wanda ya dinga sarrafa kayan ado a garinsa wato birnin Zunyi. Yayin da yake hira kan wannan kuduri mai cike da rikici, Zhang Mingfu ya ji dadi sosai.

"A wancan lokacin da ake fama da matsalar kudi mai tsanani, amma kayan ado abu ne da jama'a ke bukata yau da kullum. A wannan lokaci, fararen hula sun yi tsamani sosai yayin da suke sayen kayayyaki, kuma suna son su sayi wani irin kaya mai kyau kuma mai araha. Domin kayayyakin da muka sarrafa suna da inganci, kuma suna da araha, sabo da haka, kayayyakinmu sun zama kaya na farko da za su gaba. Sakamakon haka, ba kawai matsalar kudi ba ta kawo illa ga sayar da kayayyakinmu ba, hatta ma mun sayar da kayayyaki da yawa."

Sabo da kokarin aiki da Zhang Mingfu ya yi, kamfaninsa mai suna "Meng Liya" dake sarrafa kayan ado ya samu bunkasuwa a yayin da ake yin fama da matsalar kudi mai tsanani. Mai kudi Zhang Mingfu yana son yi yawon shakatawa sosai, amma bai yi yawon shakatawa a kasashen ketare tare da iyalansa ba kamar yadda sauran mutane suke yi, maimakon haka, ya kan je kauyuka na nesa da birane. Zhang Mingfu ya ce, ya kan je kauyuka, da yin hira da manoma, da kuma gano zaman rayuwar manoma, wannan abu ne da ya fi son yi.

"Ni manomi ne, kuma ni 'dan ci rani ne. Duk manoma na kauyukan da na je su kan nuna maraba gare ni sosai. Sabo da haka, na kan yi zama tare da su, kuma na yi aiki tare da su."

Burin da kan sa shi ya je kauyuka shi ne jin dadin zaman rayuwar zaman kauyuka masu ban sha'awa. Amma abin da Zhang Mingfu ya gani shi ne, manoma na kauyuka na nesa suna fama da wahalhalu da dama, kuma abu mafi tsanani shi ne, yawancin 'yan ci rani su kan yi aiki a manyan birane, hakan ya sa yawan yara da tsofaffin da suke yin zaman kadaici a kauyuka ya karu da dama, kuma ana fama da matsalar rashin ci gaba a kauyuka.

Wadannan abubuwa sun girgiza zuciyar Zhang Mingfu sosai, kuma sun sa ya tuna da lokacin da ya yi fama da talauci a da. Sabo da haka, taimakawa manoma ya zama muhimmin burin dake a ransa. A shekarar 2005, Zhang Mingfu ya yi watsi da shirinsa na bunkasa kamfanin sarrafa kayan ado, kuma a garinsa, ya kafa wani kamfanin kiwon kaji wanda ba zai kawo riba da dama ba, ta yadda zai jawo manoma su komo garinsu don bunkasa sana'ar kiwon dabbobi.

"ni ba 'dan kasuwa ne cikakke ba, domin dole ne 'dan kasuwa ya so samun riba da dama. Idan na yi la'akari da riba da bunkasuwar kamfanina, ba zan bunkasa sana'ar kiwon kaji ba, kuma tilas ne na ci gaba da sarrafa kayan ado, domin kayan ado ya fi kawo riba da yawa, wannan abu ne da kowa ya sani. Amma garina ya fi taulauci, sabo da haka, kamata ya yi mu yi kokarin taimakawa garina, ta yadda za a samu arziki sosai. Hakan ya sa na yi aikin kiwon kaji."

Bayan haka, Zhang Mingfu ya yi ta mai da hankali kan batutuwan kauyuka da na manoma. A shekarar 2006, Zhang Mingfu ya yi bincike a kauyuka na lardunan Liaoning, da na Jiangxi, da kuma na Hu'nan da dai sauransu, inda ya gano cewa, dole ne a kafa masana'antu da yawa a kauyuka, 'yan ci rani za su komo garinsu, yadda za a warware batutuwan manoma da na kauyuka.

A farkon shekarar 2007, bisa takardar binciken da ya yi, Zhang Mingfu ya rubuta wata wasika zuwa ga firayim ministan kasar Sin Wen Jiabao, inda ya bayyana batutuwan da ake fama da su a kauyuka a halin yanzu, kuma ya ba da shawarwari a kai. 'Yar Zhang Mingfu, Zhang Lihong ta ga wasikar da mahaifinta ya rubuta, kuma ta sa alamarta a kan wasikar. Yayin da take tunani da wannan, ta ji farin ciki sosai.

"Yayin da yake rubuta wasika, muna tsaye a gefensa muna kallo, mahaifina da kauwata da ni mun gama wanna wasika da sassafe. A ganina abubuwan da muka bayyana a wasika, hakikanan abubuwa ne da mu kan gani yau da kullum, mun rattaba hannu a kai, domin bayyana niyyarmu, abubuwan da muka rubuta, abubuwan ne na gaskiya."

Bayan wata daya da suka mika wannan wasika, Zhang Mingfu da 'yarsa sun samu amsa daga firayim minista Wen Jiabao, inda mista Wen Jiabao ya nuna babban yabo ga shawarwarinsa. Kuma mista Wen Jiabao ya tabbatar da wasu shawarwarinsa a cikin manufofin kauyuka na tsakiyar Sin. Hakan ya sa kaimi ga Zhang Mingfu na jagorantar manoma su samu kudi.

Ya zuwa yanzu, kamfanin Zhang Mingfu na kiwon kaji yana samar da kananan kaji, kuma yana sayen kwai da naman kaji don kara sarrafa su, hakan ya samar da guraban aikin yi da dama ga manoman kauyuka.

Sabo da ya mai da hankali sosai kan batutuwan kauyuka da na manoma, kuma ya ba da gudummawa wajen kyautata zaman rayuwar manoma, Zhang Mingfu ya sami lambar yabo ta ranar bikin 'yan kwadago ta kasar Sin, wannan lambar yabo ce mafi koli ga 'yan kasuwa na kasar Sin. Yayin da ya zo birnin Beijing don karbar lambar yabo, ya zo tare da yaransa.

Lokacin da aka tambayi Zhang Lihong kan mahaifinta ya tsufa domin ya kan yi aiki tare da manoma, ta ba da amsa kamar haka

"Ina ganin cewa, bai kamata mu manta garinmu ba, ko da yake shi 'dan kasuwa ne, amma shi manomi ne. Ra'ayinsa ya fi zamani, ba zai fi tsufa ba domin ya kan yi aiki tare da manoma."