Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-08-05 09:18:15    
Ana yin kokari don kara yada rawar salsa a kasar Sin

cri

Rawar salsa rawa ce wadda ke da salon musamman na Latin, mutumin da ya yi rawar salsa ya kan nuna babbar sha'awa, kuma ya kan ji dadin kuzarin da rawar salsa ta kawo masa. In an kwatanta ta da rawar ma'aunin duniya da rawar Latin, rawar salsa ta fi saukin koyo kuma tana da dadin kallo sosai. A daya waje kuma babu tufafin musamman na rawar salwa, sai tufafi na yau da kullum. Kazalika, ana iya yin rawar salsa kamar yadda ake so tare da kida. A sanadin haka, rawar salsa ta sami yaduwa cikin sauri a kasashen Latin Amurka da Turai da kuma wasu kasashen dake gabashin Asiya kamarsu kasashen Japan da Korea ta kudu da dai sauransu. Kawo yanzu, jama'ar kasar Sin su ma suna kara fahimtar wannan rawa mai nuna kuzari. A cikin shirinmu na yau, bari mu yi muku bayani kan wannan.

A shekarar 2003, an kafa kulob na farko na horas da rawar salsa a birnin Beijing. Dongdong tana daya daga cikin malaman da suke horas da rawar salsa a cikin kulob na rawar salsa. Dongdong ta komo kasar Sin ne daga kasar Cuba bayan da ta gama karatun rawar salwa a wannan kasa, tana horas da rawar salsa tare da babanta da 'yarta a kulob din SD da suka kafa. A wancen lokaci, mutane kalilan ne kawai a kasar Sin suka san rawar salsa, a birnin Beijing ma haka ne.

A harshen Spaniyanci, salsa suna ne na wani irin abincin da jama'ar Latin Amurka ke so, a dafa wannan abinci da tumatir da yaji, yana da zafi. Tun bayan shekarar 1930, marubutan kide-kide na kasar Cuba sun kara zagewa don rubuta kide-kiden da suka shafi rawar salsa, kuma sun kara sa kuzari kamar miyar salsa a cikin kidar rawar salsa. Daga nan, an kafa rawa mai salon Latin dake hade da kidan nuna kuzari da miyar salsa tare, ana kiranta da suna rawar salsa.

Rawar salsa ta kan ba da sha'awa da soyayya da kuzari, matasa da yara sun fi son wannan rawa, musamman ma matasan dake aiki a kamfanin jarin waje da daliban dake karatu a jami'a su kan je dakin shan giya inda masu wasan kayan kida da suka zo daga kasar Cuba suke kidar rawar salsa. A kowane daren karshen mako, Dongdong ta kan zo irin wannan dakin shan giya tare da dalibanta domin yin rawar salsa a nan. Ana iya cewa, rawar salsa tana samun bunkasuwa cikin sauri a birnin Beijing.

Kawo yanzu, a kai a kai ne rawar salsa take samun karbuwa a kasar Sin, musamman ma a birnin Beijing. Amma ba ta yada kamar yadda ya kamata ba, wato bunkasuwarta ba ta kai kimarmu ba. Kan wannan batu, Dongdong wadda ta riga ta zama shahararriyar malamar koyar da rawar salsa a birnin Beijing ta bayyana cewa,  "A ganina, rawar salsa ba ta samu karbuwa sosai ba, alal misali, yanzu idan na je dakin shan giya, mutanen da suke yin rawar salsa a ciki ba su karu ba, sai dai kawai mutanen da suka taba zuwa nan. A hakika dai, rawar salsa ba ta samu yalwatuwa kamar yadda ya kamata ba, mutanen dake kaunar wannan rawa ba su da yawa."

To, ina dalilin da ya sa haka? Dongdong ta kyautata tunani da cewa, muhimmin dalilin da ya sa haka shi ne domin ba a kafa cibiyar horaswa ta rawar salsa a birnin Beijing ba. Wannan ya hana masu koyon rawar salsa da su ci gaba da koyon wannan rawa bisa mataki daban daban, a sanadin haka, ba su iya kara fahimtar ainihin ma'anar rawar salsa ba. Dongdong ta kara da cewa,  "Yanzu, a birnin Beijing, babu isasshiyar cibiyar horaswa ta rawa wato 'dance studio', a cikin irin wannan cibiyar horas da rawa, babu na'urori, sai dai malaman horaswa da daliban da suke koyon rawa da kide-kide masu dacewa kawai. Malamai za su koyar da dalibai yadda suke yin rawar salsa, sa'an nan kuma matsayin dalibai zai dagu a kai a kai bisa shirin malamai."

Ban da wannan kuma, yanzu ba a fidda tsarin sana'ar rawar salsa a birnin Beijing ba tukuna, wasu kamfanoni sun kafa ajin horas da rawar salsa kamar yadda suke so domin neman samun riba. Dalibai masu koyon rawar ba su iya koyon ainihin rawar salsa a irin wannan aji ba, shi ma ya bata sunan rawar salsa a zukatunsu. Dongdong ta ce,  "Malaman sana'a na koyar da rawar salsa ba su da yawa a birnin Beijing, wasu malamai suna koyar da wannan rawa, amma ba su da isasshen ilmin dake shafar rawar salsa, a sanadin haka, rawar salsa za ta zama rawar motsa jiki ce kawai, masu koyon rawar salsa da masu kallon rawar salsa suna dauka cewa, shi ke nan, rawar salsa haka take kawai, ba dadi."

Kazalika, cibiyoyin horas da rawar salsa daban daban suna karuwa saboda suna son kara samun riba. A karkashin irin wannan hali, ba za a iya tabbatar da cudanyar rawa tsakaninsu ba, shi ya sa rawar salsa ba ta samu ci gaba yadda ya kamata ba.

Dongdong ta kyautata tunani da cewa, ainihin rawa tana bukatar ainihin malamin horaswa, koda yake Dongdong tana nuna kwazo da himma domin kara yada rawar salsa da al'adun Latin a kasar Sin, amma ba ta samu sakamako mai gamsarwa ba. Wasu daliban dake koyon rawar salsa ba su fahimci ainihin ma'anar rawar ba, suna ganin cewa, fasahar rawa ta fi muhimmanci. Game da wannan, Dongdong ta yi mana bayani cewa,  "A halin da ake ciki yanzu, wasu malaman horas da rawar salsa sun fi son mai da muhimmanci kan fasahar rawa, wato suna mayar da rawar salsa kamar gasa, amma a hakika dai, babban burin rawar salsa shi ne saki jiki, makasudin yin rawar salsa shi ne neman samun farin ciki da kuzari, ba gasa ba ce. Muna yin bakin ciki kwarai saboda ba a tabbatar da ainihin nufin rawar salsa a kasar Sin ba."

Yanzu a birnin Beijing, ana iya cewar, bunkasuwar rawar salsa ya shiga halin kaka-nika-yi, matsaloli iri daban daban suna kasancewa a gabanmu, kuma ba a warware su ba tukuna. Amma abin sha'awa shi ne rawar salsa ta riga ta shiga zukatun jama'ar birnin Beijing, kuma ta riga ta kara samun karbuwa a birnin Beijing. Wasu jama'ar birnin Beijing suna mayar da rawar salsa kamar wata sabuwar hanyar motsa jiki. Dongdong ta ce,  "Ana iya cewa, kawo yanzu, jama'ar birnin Beijing dake sha'awar rawar salsa suna karuwa a kwana a tashi. Da, matasa ne kawai suke yin rawar salsa, amma yanzu tsofafi da masu matsakaitan shekaru su ma sun san rawar salsa, suna koyon rawar salsa kuma suna yin rawar salsa."

Masu sauraro, kamar yadda kuka sani, rawa ba ta da iyakar kasa, kida shi ma ba shi da iyakar kasa, ko shakka babu, rawar salsa tana samun bunkasuwa a karkashin kokarin da ake yi tare, muna fatan za ta kara samun ci gaba. (Jamila Zhou)