Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-07-21 16:39:15    
Masana'antun samar da kuma yin amfani da makamashi mai tsaba suna samun ci gaba cikin sauri a kasar Sin

cri
Jama'a masu karatu, idan an kwatanta wutar lantarki da ake samu da makamashin kwal da yake fitar da abubuwan dumama yanayin duniya, wutar lantarki da ake samu da makamashin iska tana da kyau na a-zo-a-gani. Ya kasance tamkar makamashi mai tsabta, lokacin da ake samar da wutar lantarki da makamashin iska, ba a fitar da kowane irin sinadarin guba, kuma ba a gurbata muhalli. Sakamakon haka, kasar Sin ta sanya makamashin iska da ya zama daya daga cikin sabbin makamashin da za ta kara mai da hankali wajen yin amfani da su.

Kasar Sin kasa ce mai arzikin makamashin iska. Jimillar makamashin iska da za a iya yin amfani da shi ya kai kimanin kilowatts biliyan 1, wato idan kasar Sin ta yi amfani da kashi 60 cikin kashi dari daga cikinsu, za a iya biyan dukkan bukatun da take da su yanzu.

Game da yadda kasar Sin take amfani da makamashin iska yanzu, Mr. Shi Lishan, mataimakin direktan ofishin sabon nau'o'in makamashi ta hukumar makamashi ta kasar Sin ya bayyana cewa, "Yawan injunan samar da wutar lantarki da makamashin iska ya karu fiye da ninki goma. Ya zuwa karshen shekara ta 2008, jimillar injunan samar da wutar lantarki da makamashin iska da kasar Sin take amfani da su ta kai kilowatts miliyan 12, wato kasar Sin tana matsayi na hudu a duk duniya bayan kasashen Amurka da Jamus da Spaniya. Yawan injunan samar da wutar lantarki da makamashin iska da aka ajiye a kasar Sin ta karu da ninki da yawa a cikin jerin shekaru 3 da suka gabata. Bisa wannan sauri, ya zuwa karshen shekara ta 2010, jimillar injunan samar da wutar lantarki da makamashin iska da za a yi amfani da su a kasar Sin za ta kai kilowatts miliyan 30."

Kasar Sin ta tsara da kuma aiwatar da jerin manufofi domin sa kaimi ga gwamnatocin matakai daban daban da masana'antu da su yi amfani da makamashin iska. A lokacin da ake kara saurin amfani da makamashin iska, masana'antun kasar Sin sun taka muhimmiyar rawa sosai wajen yin amfani da sabon makamashi. Yau da shekaru 4 da suka gabata, kamfanin Long Yuan na samar da wutar lantarki, wato kamfani ne mafi girma wajen yin amfani da makamashin iska domin samar da wutar lantarki a kasar Sin ya kafa wani kamfanin yin amfani da makamashin iska domin samar da wutar lantarki a lardin Jiangsu da ke gabashin kasar Sin domin kafa tasoshin yin amfani da makamashin iska wajen samar da wutar lantarki a yankunan bakin teku a lardin. Bisa shirin da aka tsara, ya zuwa watan Oktoba na shekarar da ake ciki, yawan wutar lantarki da wannan kamfani zai samar ta hanyar yin amfani da makamashin iska zai biya bukatun gidaje a kauyuka da cikin gari dubu dari 8 da ake da su a duk shekara. Mr. Huang Qun, mataimakin babban direktan kamfanin Long Yuan ya bayyana cewa, sabo da kasancewar makoma mai kyau, kamfaninsa zai kara saurin kafa tasoshin yin amfani da makamashin iska domin samar da wutar lantarki. Mr. Huang ya ce, "Yanzu, kamfanin Long Yuan yana kafa tasoshin yin amfani da makamashin iska domin samar da wutar lantarki a larduna 16. Bisa shirin da muka tsara, ya zuwa shekarar 2010, yawan injunan yin amfani da makamashin iska domin samar da wutar lantarki da za mu ajiye zai kai kilowatts miliyan 6, ya zuwa shekara ta 2012, zai kai kilowatts miliyan 9, sannan ya zuwa shekara ta 2020, zai wuce kilowatts 20."

Bisa kididdigar da hukumar makamashi ta kasar Sin ta bayar, an ce, ya zuwa yanzu an riga an kafa tasoshin yin amfani da makamashin iska domin samar da wutar lantarki guda 240 a larduna fiye da 20 na kasar Sin. Yawan injunan yin amfani da makamashin iska domin samar da wutar lantarki ya kai fiye da dubu 11.

Kasar Sin tana da arzikin makamashin iska da yake kasancewa a dukkan wuraren kasar. A yankunan kudu maso gabashin kasar, ko a yankunan arewa maso yammacin kasar, kamar su jihohin Xinjiang da Mongoliya ta gida, dukkansu yankuna ne da ke da arzikin makamashin iska. Sabo da haka, ana samun sauki sosai wajen yin amfani da makamashin iska. Gundumar Burtsin tana cikin kwarin kogin Ertsis, wato daya daga cikin yankunan da su kan samu mahaukaciyar guguwa a jihar Xinjiang. Mahaukaciyar guguwa ba ta daina bugawa a duk shekara a cikin wannan kwarin kogin na Ertsis. A 'yan shekarun baya, gundumar Burtsin ta kara karfin yin amfani da makamashin iska, kuma ta jawo kamfanoni 8 da su kafa tasoshin samar da wutar lantarki da makamashin iska a gundumar. Ya zuwa yanzu, an riga an gama wata babbar tasha daga cikin wadannan, kuma an soma samar da wutar lantarki ga tsarin samar da wutar lantarki. Game da wannan tasha, Mr. Zhou Laiguo wanda ke kula da aikin kafa wannan tasha, ya ce, "Da farko dai, an ajiye injunan samar da wutar lantarki da makamashin iska guda 66. Jimillar karfinsu ta kai fiye da kilowatts dubu 49, wato wadannan injuna sun yi aiki awa daya, za su iya samar da wutar lantarki kilowatts dubu 49. Wannan wutar lantarki za ta iya biyan kashi 4 cikin kashi dari bisa na bukatun da garin gundumar Burtsin yake da su."

Sabo da sana'ar yin amfani da makamashin iska domin samar da wutar lantarki ta samu ci gaba cikin sauri a kasar Sin, sauran sana'o'in da ke da nasaba da wannan sana'a su ma sun samu ci gaba. Yanzu, kasar Sin ita kanta tana samar da yawancin injunan yin amfani da makamashin iska domin samar da wutar lantarki, farashinsu ma ya ragu sosai. Mr. Shi Lishan ya ce, kasar Sin ta samu ci gaba sosai wajen mallakar fasahohin kera injunan yin amfani da makamashin iska domin samar da wutar lantarki. Mr. Shi ya ce, "Sana'o'in kera injunan yin amfani da makamashin iska domin samar da wutar lantarki sun samu ci gaba cikin sauri sosai. A shekara ta 2004, mun iya kera injin da karfinsa bai wuce na kilowatts dari 6 ba kawai. Amma bayan shekaru 4 da suka gabata, yanzu, mun iya samar da injin da karfinsa ya kai kilowatts 1500 zuwa kilowatts dubu 2. Haka kuma, nan gaba ba da dadewa ba, za mu iya samar da injin yin amfani da makamashin iska domin samar da wutar lantarki da karfinsa ya kai kilowatts dubu 3."

Yanzu kamfanonin kasar Sin sun riga sun mallaki fasahohin kera manyan jerin injunan yin amfani da makamashin iska domin samar da wutar lantarki. Yawan masan'antun da suke da karfin kera irin wadannan manyan jerin injunan samar da wutar lantarki da makamashin iska ya kai fiye da 70. A waje daya, wasu masana'antu suna kera kayayyakin gyara ga irin wadannan manyan injuna. Sakamakon haka, an riga an kafa wani tsarin kera jerin manyan injunan yin amfani da makamashin iska domin samar da wutar lantaki da kayayyakinsu na gyara.

Bisa shirin da aka tsara, an ce, a cikin shekaru 2 masu zuwa, kasar Sin za ta kafa manyan tasoshin yin amfani da makamashin iska domin samar da wutar lantarki fiye da 10 da karfin kowaccensu zai kai kilowatts miliyan 1 a lardunan Hebei da Mongoliya ta gida da Liaoning da Jilin da Xinjiang, kuma za a kafa wasu tasoshin yin amfani da makamashin iska domin samar da wutar lantarki da karfin kowaccensu zai kai kilowatts miliyan 10. Ba ma kawai kasar Sin za ta kara saurin kafa irin wadannan tasoshi a kasa ba, har ma za ta kara saurin kafa tasoshin samar da wutar lantarki da makamashin iska a teku.

Bugu da kari kuma, kasar Sin za ta ci gaba da kyautata manufofi da yanayin kirkiro sabbin fasahohin zamani domin samar da wutar lantarki da aka samu ta hanyar yin amfani da makamashin iska a gidajen jama'ar wajen, za a kara kyautata karfin kera injunan zamani na samar da wutar lantarki da makamashin iska, ta yadda za a iya raya sana'o'in da suke da nasaba da makamashin iska ba tare da tangarda ba kamar yadda ya kamata. (Sanusi Chen)