Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-07-20 14:59:52    
Matsalar kudi ta duniya ta kawo sabon kalubale ga duniya ta fuskar yaki da ciwon Sida

cri
A ranar 19 ga wata da dare, an bude babban taro a karo na 5 kan kwayoyin cutar HIV, da yadda za a yi rigakafi da yin jiyya game ciwon na shekarar 2009 a birnin Cape Town na kasar Afrika ta kudu. A gun taron kuma, za a mayar da hankali kan tattauna yadda ake iya kara saurin yin amfani da sabbin sakamakon da aka samu wajen nazarin yaki da ciwon Sida, gami da yin amfani da su kan kasashen da jama'arsu ke samun kudin shiga kalilan ne, da kuma sauran batutuwa. Masu halartar taron da yawa sun bayyana cewa, abin da suka fi nuna damuwa a yanzu shi ne, kasashen yamma sun rage yawan kudin da suke zubawa kan rigakafi da shawo kan ciwon Sida daya bayan daya, sakamakon tasirin da matsalar kudi ta duniya ke kawowa, ta yadda za a samu cikas ga aikin yaki da ciwon Sida na duniya.

Manazarta, da masu aiki kan ciwon Sida, da kuma jami'an hukumomin yaki da ciwon Sida daga kasashe daban daban, wadanda yawansu ya wuce 5000 sun halarci wannan taro na kwanaki 4. Shugaban babban taron, kuma shugaban majalisar kula da ciwon Sida ta duniya Julio Montaner ya bayyana a gun bikin bude taron cewa, yanzu ana cikin muhimmin lokaci kan aikin yaki da ciwon Sidan na duniya, kuma ana fuskantar bullar HIV. Mr. Montaner ya bayyana cewa, yanzu akwai masu kamuwa da ciwon Sida kusan miliyan hudu a kasashen da jama'arsu ke samun kudin shiga kalilan da ba su iya samun jiyya, a waje daya kuma, akwai mutanen da ke dauke da kwayar cutar HIV kimanin miliyan shida da ba a yi musu bincike ba, wadannan mutane kuma suna iya yada kwayoyin cutar a ko wane lokaci.

Majalisar kula da ciwon Sida ta duniya ta bayar da wani takaitaccen jawabi kafin babban taron cewa, sakamakon tasirin da matsalar kudi ta duniya ke kawowa, kasashe da yawa sun rage yawan kudin da suke bayarwa kan aikin yaki da ciwon Sida, wasu kuma sun soke alkawarin da suka yi na kara bayar da kudi kan aikin, ta yadda aka shiga wani mawuyacin halin da ba a taba gani ba.

A watan da ya wuce, M.D.D. ta taba bayar da wani rahoto, inda ta bukaci gwamnatocin kasashe daban daban da kada su rage yawan kudin da suke bayarwa kan akin yaki da ciwon Sida, bisa dalilinsu na wai matsalar kudi. Bayan haka kuma, rahoton ya nuna cewa, yanzu ba a samu isasshen kudi kan aikin yaki da ciwon Sida na duniya, a cikin mutanen da ke dauke da kwayar cutar HIV biyar, mutane biyu ne kawai ke iya samun jiyya.

A lokacin da majalisar kula da ciwon Sida ke yin kira ga kasashen duniya da su kara bayar da kudi kan aikin yaki da ciwon Sida na kasashen da jama'arsu ke samun kudin shiga kalilan, a waje daya kuma, an yi kira ga gwamnatoci na wadannan kasashe da su kara mayar da hankali kan aikin yaki da ciwon Sida, gami da kara karfinsu na yaki da ciwon Sida, da kuma kara bayar da kudi kan aikin.

An ce, kasashen dake kudancin Afrika yankuna ne da aka fi samun ciwon Sida a duniya, kashi 2 cikin uku na mutanen da ke dauke da kwayoyin cutar HIV da yawansu ya kai miliyan 33 suna zaune a yankunan. Kasar Afrika ta kudu dake daukar nauyin shirya babban taron ita ce kuma kasar da aka fi samun ciwon Sida a duniya. Shugaban babban taron, kuma wani jami'in wata hukumar kula da harkokin yaki da ciwon Sida ta jama'a ta kasar Afrika ta kudu, Jerry Cooavadia ya bayyana cewa, aikin yaki da ciwon Sida na kawo babban tasiri ga harkokin siyasa, da zaman al'umma, da tattalin arziki, da kuma zaman rayuwar jama'ar kasar. Ya yi kira ga gwamnatocin kasashe daban daban na Afrika da su kara bayar da kudi kan aikin, da kuma kafa cikakken tsarin kiwon lafiya, domin rage yawan mutanen da suke rasa rayuka sakamakon ciwon Sida a nahiyar Afrika.