Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-07-15 15:52:52    
Har wa yau dai makomar tattalin arzikin Amurka tana cikin  halin rashin sanin tabbas

cri

A hakika an samu wasu alamu masu kyau a tsarin tattalin arziki na Amurka,yawan GDP na farkon watanni uku na bana ya ragu da kashi 5.5 bisa dari,wato ya dan ragu da yawansa na kashi 6.3 bisa dari da aka samu a watanni uku na karshen shekara ta 2008. An kuma samu alamun sassauci a kasuwannin gidaje da filaye na kasar Amurka. A kan matsayin ma'aunin da ya shaida ci gaban tattalin arzikin Amurka,masana'antun Amurka a watan Mayu sun dan sassauta raguwa,matsayin ma'auni na ISM ya kai matsayin koli a cikin watanni tara da suka gabata. A sa'I daya kuma yardar mutane kan kasuwannin kudade na fara farfadowa,kasuwar saida hannayen jari ta Dow Jones ta karu da kashi 40 bisa dari daga matsayinta mafi kaskanci a rikicin kudi.duk da haka wasu matsaloli na rika bullowa,wannan ya fadakar da kan jama'a cewa faduwar tattalin arzikin Amurka ba ta kai karshenta ba tukuna. Babban masanin gidauniyar zaman lafiya ta duniya Carnegie Mr Albert Keidel ya bayyana cewa daga adadan tattalin arziki a fannoni daban daban har yanzu da wuya a gane ainihin halin da tattalin arzikin Amurka ke ciki a yanzu, ya ce  " A ganina ana cikin halin rashin sanin tabba a yanzu. Wannan karo ne na farko da aka ga rikicin kudi da shirin sa kaimi na gwamnati a sa'I daya a kasar Amurka.kokarin nuna goyon bayan harkokin kudi na bankuna na tafiyar hawainiya kamar yadda aka yi tsammani a da,gwamnatin na kokarin samo manufofi a wannan fanni.sabili da haka halin rashin sanin tabbas ya game ko ina,kasuwannin hada hada hannun jari na faduwa, farashin danyen mai ma na ci gaba da faduwa, da wuya a ce wane lokaci tattalin arzikin kasar Amurka zai sauya."

1 2 3