Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-07-10 17:41:21    
Hongkong wani yanki ne na kasar Sin tun zamanin gargajiya

cri
Masu sauraro, kowace rana, muna gabatar muku shirin koyon Sinanci daga nan sashen Hausa na rediyon kasar Sin, kuma shirin na samun karbuwa sosai daga masu sauraro, wadanda har su kan ba mu shawarwari a kan shirin. Ga shi kwanan baya, Naziru Idris Tahir, wanda ya fito daga Kano State College of Arts, Science and Remedial Studies, Kano, Nijeriya, ya aiko mana sakon da ke dauke da shawarwarinsa ga shirin koyon Sinanci, kamar yadda ya fada a cikin sakon, "a gaskiya na san akwai mutane da yawa irina ba ma a Nigeriya ba kawai, harma kaf fadin africa, wadanda da ma can su suna da son kasar Sin, uwa uba ma suna mutukar son koyon harshen kasar Sin da al'adun kasar. Mun yi mutukar farin ciki da kuke koyar da harshen ta rediyonku a kalla kusan kullum. Amma harshen Sin yana da wuyar koyo a rubuce ko a furce, wannan ta sa har wasu a kasar Hausa kamar garin da nike wato Kano, idan ka ce da mutane harshen Sin za ka koya, to sai su ce lalle za ka dau karma kanka dala ba gammo, wato suna nufin kar ka fara domin ba ma zai yiwu ba. To kusan gaskiya haka ne, domin na kai shekara biyu ina nazarin yaya zan bullowa lamarin. A karshe shi ne na yanke shawara in rubuto muku wasika ko za ku share min hawaye. Sannan kuma in shawarce ku idan har da gaske kuke kuna son mutane irina su koya, to, sai ku yi kokarin aiko mana ko da littafi ne wanda zai taimaka mana mutuka gaya wajen koyon harshen a rubuce da furce. littattafan kamar su, kamus na hausa da na harshen Sin da sauransu." To, sakon da Naziru Idris Tahir a Kano, Nijeriya, ya aiko mana ke nan, kuma mun gode da shawarar da ka ba mu. Hakika, ban da malam Naziru, wasu masu sauraronmu su ma sun taba neman littafin koyon Sinanci ko kamus a wajenmu, ciki har da malam Alhassan Jumma a jihar Gombe, tarayyar Nijeriya, wanda a kwanan baya ya aiko mana sakon cewa, "Don Allah ina so ku aikomin da sabon littafinku na koyon sinanci mai taken "koyon Sinanci da harshenka, Sinanci na yau da kullum". Masu sauraro, a gaskiya, yanzu ba mu da wannan littafi na "koyon Sinanci", amma sashen Hausa na wani kokarin bullo da littafin da kamus na Hausa da Sinanci, domin biyan bukatun masu sauraro, ta yadda za ku sami saukin koyon Sinanci. Da fatan Allah ya taimaka mana.

To, sai kuma malama Fatima Musa Abbas daga Katsina, tarayyar Nijeriya, ta aiko mana wani sakon, inda ta yi mana tambaya cewa, "muna so mu san mene ne asalin Hong Kong? Kuma da gaske ne tana a cikin lardunan kasar Sin ko ita ma kasa ce mai cin gashin kanta? Da fatan za ku amsa mani wannan tambayar."

To, malama Fatima, muna miki godiya da aiko mana sakon, kuma a game da tambayarki, muna tabbatar miki da cewa, Hongkong yanki ne na kasar Sin tun zamanin gargajiya, wannan abu ne da babu wani cece-kuce a kansa. Tuni yau da shekaru dubu 4 zuwa dubu 5 da suka gabata, kakanin kakanin al'ummar Sinawa sun fara zaman rayuwa a yankin Hongkong, kuma muna iya gano gaskiyar abin bisa ga kayayyakin tarihin da aka hako a yankin. Sa'an nan, ya zuwa shekarar 214 kafin haihuwar annabi Isa, shahararren sarkin kasar Sin, Qin Shihuang, wanda ya hada kasar Sin baki daya a karkashin mulkinsa, ya kafa hukumomin mulki a Hongkong, kuma tun daga lokacin har kullum Hongkong na karkashin mulkin gwamnatin kasar Sin ba tare da wani sauyi ba, har lokacin da Turawan Birtaniya suka zo.

Ya zuwa shekarar 1840, Birtaniya ta gabatar da yaki a kan kasar Sin, wadda kuma a shekarar 1842, ta tilasta wa mahukuntan daular Qing ta gargajiyar Sin da ta daddale yarjejeniyar Nanjing, kuma bisa yarjejeniyar, Birtaniya ta kwace tsibirin Hongkong daga hannun kasar Sin. Daga bisani kuma, Birtaniya ta kara kwato yankunan da ke kewayen Hongkong bisa ga yarjejeniyoyi marasa adalci da ta tilasta wa mahukuntan daular Qing ta rattaba hannu a kai. Wadannan yarjejeniyoyin kuma sun yi sanadiyyar mulkin mallaka na tsawon shekaru fiye da 100 da Birtaniya ta kafa a Hongkong.

Sai kuma ya zuwa shekarar 1982, Sin da Birtaniya suka fara shawarwari na tsawon shekaru biyu kan batun Hongkong. Daga karshe, a ran 9 ga watan Disamba na shekarar 1984, a hukunce firaministan kasar Sin da takwaransa na Birtaniya sun rattaba hannu a kan hadaddiyar sanarwa kan batun Hongkong, inda aka sanar da cewa, gwamnatin kasar Sin za ta maido da Hongkong a karkashin mulkinta a ran 1 ga watan Yuli na shekarar 1997.

Da karfe sha biyu na safiyar ranar 1 ga watan Yuli na shekara ta 1997, bisa kide-kiden taken kasar Sin ne, aka daga tutar jamhuriyar jama'ar kasar Sin da kuma tutar yankin musamman na Hongkong a yankin Hongkong, lallai ne, Hongkong ta komo hannun kasarta ta asali a karshe bayan sauye-sauyen da ta samu a cikin shekaru fiye da 100 da suka wuce, kuma daga nan, gwamnatin kasar Sin ta maido da mulki a kan yankin Hongkong.

Da karfe 12 da minti 4, Jiang Zemin, tsohon shugaban kasar Sin ya sanar da cewa, bisa sanarwar hadin kan Sin da Birtaniya a kan batun Hongkong, gwamnatocin kasashen biyu sun yi bikin komo da Hongkong bisa lokacin da aka tsai da, kuma mun sanar da maido da mulki a kan Hongkong, kuma gwamnatin yankin musamman ta Hongkong na jamhuriyar jama'ar Sin ta kafu a hukunce. Daga nan kuma, an bude wani sabon babi a Hongkong.

Bayan da aka komo da Hongkong a karkashin mulkin kasar Sin, ana aiwatar da manufar 'kasa daya amma tsarin mulki guda biyu' a yankin, wato ban da harkokin tsaro da diplomasiyya, Hongkong tana da babban ikon tafiyar da harkokin kanta, wato tana da ikon tafiyar da harkokin mulkinta da 'yancin kafa doka da kuma 'yancin gudanar da shari'a da cikakken ikon yanke hukunci a fannin shari'a, kuma bisa doka, mazaunan Hongkong suna da 'yanci a fannoni daban daban. Yankin musamman na Hongkong zai bunkasa tsarin dimokuradiyya da ya dace da hakikanin halin da yake ciki sannu a hankali.

To, amsarmu ke nan ga malama Fatima Musa Abbas daga Katsina, tarayyar Nijeriya, da fatan kin ji kuma kin gamsu da bayaninmu.

To, bayan haka, za mu kuma gai da Haruna Muhammad a Katsina, tarayyar Nijeriya, da Bala Sani 'yan rariya Jega, a jihar Kabbi, tarayyar Nijeriya, da malam malam mai zanen hula Gololo, Gamawa, jihar Bauchi, tarayyar Nijeriya, da Mussa Niassa a Dakar Senegal, da sauran wadanda suka rubuto mana sakwannin gaishe-gaishe da na sada zumunci, mun gode, kuma da fatan Allah ya karfafa dankon zumunci a tsakaninmu.(Lubabatu)