Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-06-26 17:40:47    
Sakwannin masu sauraron da suka yi nasara a gasar kacici-kacici game da ni'itattun wurare a lardin Sichuan na kasar Sin

cri
Masu sauraro, idan ba ku manta ba, kwanan baya, mun dasa aya ga gasar kacici-kacici dangane da ni'imtattun wurare a lardin Sichuan na kasar Sin, har ma mun fitar da wadanda suka yi fice a gasar, ciki har da wanda ya sami gayyatarmu ta zuwa kasar Sin ziyara, wato malam Mohammed Idi Gargajiga, wanda ya fito daga garin Gombe, jihar Gombe, tarayyar Nijeriya. Ga shi, malam Mohammed ya zo nan kasar Sin, ya kuma kai ziyara ga wurare da dama masu ni'ima a lardin Sichuan, ya kuma yi hira da mu a shirinmu na baya, idan kun samu damar sauraronmu. Kome nisan jifa, kasa zai fado, kamar yadda Bahaushe kan ce, malam Mohammed ya kawo karshen ziyararsa ya kuma koma gida, kuma kwanan baya, mun sami wani sakon da ya aiko mana, inda ya ce, "Ina sanar da ku cewa, na sauka a gida Nigeria kuma na isa can gida da ke garina a jihar Gombe lami lafiya ba matsala, kuma ina kara yi muku godiya ta musamman tare da nuna fatan alheri da kuma nuna sahihiyar godiya a gare ku, bisa irin kyakkyawan hadin kai da goyon baya da kuka ba ni a yayin da nake gudanar da ziyarata a kasar Sin, kuma ba ma kawai a gare ni ba, a'a har ma ga dukkan mambobin club na GOMBAWA CRI LITENERS CLUB, dukkan su maza da mata, babba da yaro, sun nuna farin cikinsu tare da babbar godiya ga Sashen Hausa na CRI. Tare da fatan zamu ci gaba da karawa karfen gadar zurfafa zumuncin da ke tsakanin mu a nan gaba." To, malam Mohammed, mun yi farin ciki sosai da samun wannan sako naka, sanin cewa ka koma gida lafiya, kuma mu ma muna nuna maka godiya sabo da kokarin da ka yi wajen shiga gasar kacici-kacici dangane da ni'imtattun wurare a lardin Sichuan. Bayan haka, muna fatan ka amfana ka kuma karu da ziyararka a kasar Sin. Da fatan Allah ya karfafa dankon zumunci a tsakaninmu.

Ban da malam Mohammed, sauran masu sauraronmu sun kuma aiko mana sakwanninsu bayan da suka sami sakamakon gasar. Shugaba Bello Abubakar Malam Gero daga Tudun Wada Riyojin dan Umma Bayan Rima rediyo, Sokoto, Nijeriya, ya aiko mana sakon cewa, "Ina mai nuna matukar farin cikina tare da godiyata ga Allah da ya ba ni ikon shiga gasar kacici kacici ta ni'imtattun wurare na lardin Sichuan da ke kasar Sin. Haka ma ina mai nuna godiyata ga shugabannin gidan rediyon kasar Sin dangane da shiryawa da kuma bayar da ilimin ga masu sauraron wannan gidan rediyo mai tarin albarka ga dukkanin masu sauraro, tare da taya murna ga dukkanin wadanda suka sami damar shiga wannan gasar kacici kacici wadanda suka yi nasara da wadanda ba su sami nasara ba.

Ni dai ina daga cikin wadanda allah yaba nasara zuwa na farko, to alhakika wannan abin jin dadi ne a gare ni tare da murna da ni har ma da iyalina.

Ban da wannan ina mai kara taya murna ga dukkan wadanda suka sami nasara tare da fatar za su ci gaba da bayar da nasu shawarwari masu alfanu ga wannan gidan rediyo, musammam sashen hausa domin mu kara samun nasara ga gudanar da aikin wannan tasha, hannu daya ina mai kara kira ga wadanda ba su sami nasara ba da cewa, su ma su kara kaimi a nan gaba su ma in allah ya so za su samu nasu rabo.

Haka ma ina mika gaisuwata ga gwarzon wannan sashe wato wannan da Allah yaba nasara samun gayyata zuwa kai ziyara a kasar Sin wato MOHAMMED IDI GARGAJIGA da ke jihar gombe a tarayyar Nigeria." To, muna gai da shugaba Bello Abubakar malam Gero, kuma muna godiya da ka aiko mana wannan sakon, haka kuma muna godiya sabo da sauraronmu da shiga gasar da ka yi.

Sai kuma sakon da Salisu Mohammed Dawanau daga Garki Abuja, tarayyar Nijeriya, ya aiko mana ya nuna cewa, "ina isar da godiya ta musamman gare ku dangane da "T-shirt" din da ku ka aiko mini. Yau da rana na karbo rigar daga Gidan Waya. Na yi murna kwarai da gaske." To, malam Salisu, mu ma mun gode maka da shiga gasarmu ta kacici-kacici, kuma muna fatan za ka ci gaba da sauraronmu da kuma shiga gasar da za mu shirya a nan gaba.

Har wa yau kuma, a madadin shugaban kungiyar Jeyrala, wato Musa Adamu Abubakar ne, Musa Ibrahim Shongo daga kungiyar ya aiko mana sakon cewa, "Bayan gaisuwa mai yawa tare da fatan alheri, ina fatan kuna lafiya kamar yadda muke a nan birnin Gombe lafiya. Bayan haka, shugaba Musa Adamu Abubakar ya umurce ni da na turo wannan wasikar zuwa gare ku, don mika murnarsa da godiyarsa gare ku bisa nasara da ya samu a bana game da gasar kacici-kacici da aka bayyana sakamakon a ranar juma'a ran 25 ga watan Mayu na shekarar 2009, wanda ya zo a cikin rukunin wadanda suka zo matsayi na daya. Shugaban ya ce na shaida muku wannan babbar nasara ce a gare shi da kuma dukkan membobin kungiyar JEYRALA. Shugaba ya ce in shaida muku, Membobin kungiyar JEYRALA suna nan suna dakon wata sabuwar gasar da suke tsammani za su shige ta da kafar dama in ALLAH ya yarda."

To, madallah, mun gode, shugaba Musa Adamu Abubakar da Musa Ibrahim Shongo da kuma mambobin kungiyar Jeyrala baki daya?sabo da irin tsayayyen goyon baya da kuke ba mu a kullum, kuma muna fatan za ku ci gaba da sauraronmu da kuma ba mu shawarwari.

Bayan haka, muna sake taya masu sauraronmu da suka yi nasara a gasar murna. Sa'an nan, wadanda ba su yi nasara ba, kada dai ku yi kasa a gwiwa, kun yi kokari, kuma muna fatan za ku rubanya kokarinku a gasar kacici-kacici da za mu shirya a nan gaba, ko ba dade ko ba jima, nasara ta Allah ce. Muna kuma farin cikin sanar da masu sauraronmu baki daya cewa, kasancewar shekarar da muke ciki shekara ta cika shekaru 60 da kafuwar Jamhuriyar Jama'ar Sin, domin karawa masu sauraronmu fahimtar sauye-sauyen da kasar Sin ta samu a cikin wadannan shekaru 60 da suka gabata ta fannonin tattalin arziki da zaman al'umma da dai sauransu, tun daga ran 1 ga watan Yuni zuwa ran 1 ga watan Satumba na shekarar da ake ciki, mun fara gabatar muku wata sabuwar gasar kacici kacici ta murnar cika shekaru 60 da kafuwar sabuwar kasar Sin ta rediyo da kuma yanar gizo. Muna kuma kira ga masu sauraronmu baki daya da ku shiga gasar, da fatan Allah zai sa ku samu nasara. (Lubabatu)