Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-06-25 09:34:28    
'Yan wasan kungiyar wasan kwallon kafar maza ta kasar Sin suna yin kokari a karkashin jagorancin sabon babban malamin horaswarsu

cri

Daga ran 25 ga watan Mayu zuwa ran 5 ga watan Yuni na bana, kungiyar wasan kwallon kafar maza ta kasar Sin wadda ta hada da sabbin 'yan wasa da yawa ta fara yin wasannin share fage a jere a karkashin jagorancin sabon babban malamin horaswa Gao Hongbo. A yayin gasannin, da farko, kungiyar kasar Sin ta lashe kungiyar kasar Iran, daga baya ta yi kunnen doki da kungiyar kasar Jamus, a karshe kuwa, kungiyar kasar Saudiyya ta ci ta a karon wasa. Abin sha'awa shi ne masu sha'awar wasan kwallon kafa sun sake komowa harkar kallon gasa, amma kafin wannan, kungiyar wasan kwallon kafar maza ta kasar Sin ta taba batawa masu sha'awar wasa rai, har ba su so su je kallon wasanta. To?a cikin shirinmu na yau, bari mu yi muku bayani kan wannan.  "Babban malami mai horaswa na kungiyar wasan kwallon kafar maza ta kasar Sin Gao Hongbo." Mataimakin shugaban hukumar wasan kwallon kafa ta kasar Sin Nan Yong ya sanar da sunan sabon babban malamin horaswa na kungiyar wasan kwallon kafar maza ta kasar Sin, sai Gao Hongbo ya fara sabon aiki. Amma abin sha'awa shi ne 'yan wasan wannan kungiya sun bai wa masu sha'awar wasan kwallon kafa mamaki sosai tun farkon da suka fara yin wasan share fage.

'Dan wasan da ya zo daga kasar Jamus Mario Gomez ya yaba wa kungiyar kasar Sin kamar haka,  "A yayin gasar da aka yi yau, 'yan wasan kungiyar wasan kwallon kafa ta kasar Sin sun yi kokari kuma sun sami babban sakamako."

Lallai masu sha'awar wasan kwallon kafa na kasar Sin su ma sun yi mamaki kuma suna jin dadin kuzarin da wasan kwallon kafa ya kan ba su. A yayin gasa tsakanin kungiyar kasar Sin da ta kasar Saudi Arabia da aka yi a filin wasan motsa jiki na Taida na birnin Tianjing dake arewacin kasar Sin, 'yan kallo sun cika wannan fili kuma sun yi ta shewa da babbar murya, mun ji an ce,  "Da, na kan kalli gasa a gida, yau na zo birnin Tianjing daga Beijing saboda na san 'yan wasan kasar Sin sun kara yin kokari kuma sun samu ci gaba."

Daga nan, ana iya cewa, dalilin da ya sa malaman horaswa da 'yan wasan kwallon kafa na kasar Sin suke cike da imani shi ne domin masu sha'awa sun sake komowa filin wasa domin kallon gasa da idonsu kai tsaye kuma suna goyon bayansu kamar yadda suka yi a da. Babban malamin horaswa Gao Hongbo ya ce,  "'Yan kallo da yawan gaske sun zo filin wasa domin nuna goyon baya ga kungiyar kasar Sin, wannan sakamako ya fi kimarmu, shi ma ya alamanta cewa, gaskiya kungiyarmu ta kawo musu kuzari, kuma suna fatan za mu kara samun ci gaba."

To, ta yaya Gao Hongbo ya samu wannan sakamako mai faranta ran mutane? Yayin da ya kafa wannan kungiya, Gao Hongbo ya zabi wasu sabbin 'yan wasa matasa wadanda ba su taba samun damar shiga kungiyar kasa ba, dalilin da ya sa haka shi ne domin a idonsa, babu 'dan wasa tauraro, sai dai 'dan wasan dake cikin hali nagari.

Rong Hao yana daya daga cikinsu, bana, yana da shekaru 22 da haihuwa ne kawai, ya ce,  "Gasa ta kan dauke hankalina, shi ya sa na yi iyakacin kokari a yayin gasar motsa jiki, ina fatan zan sake samun damar shiga sabuwar gasa a nan gaba."

Sabbin 'yan wasan kungiyar wasan kwallon kafar maza ta kasar Sin su kan nuna kwazo da himma kuma su kan yi wasa tare kafada da kafada a yayin gasa, a sanadin haka, Gao Hongbo ya nuna musu babbar godiya, ya ce, "Ina so in nuna godiya ga wadannan 'yan wasa, musamman ma ga wasu 'yan wasa wadanda ba su taba samun damar shiga babbar gasar duniya ba, na yi farin ciki ainun saboda 'yan wasan kungiyar wasan kwallon kafar maza ta kasar Sin dukkansu suna cikin hali nagari na gasa."

Kowace rana, kafin 'yan wasa su fara yin atisaye, kullum Gao Hongbo ya kan bukace su da su yi sowar cewa, "Kungiyar kasar Sin! Bari mu yi kokari." Gao Hongbo yana son gaya musu cewa, hadin gwiwa tsakanin 'yan wasa yana da muhimmanci sosai da sosai. Ya ce,  "Wasan kwallon kafa wani irin wasa ne tsakanin 'yan wasa fiye da daya, idan an jefa kwallo cikin raga, to, ba amfani ne na wani 'dan wasa ba, kuma idan an jefa kwallo cikin ragarmu, to, ba laifin mai tsaron gida shi kadai ba ne."

Kawo yanzu, ana iya cewa, kungiyar wasan kwallon kafar maza ta kasar Sin ta riga ta samu ci gaba bisa mataki na farko, amma abu mafi muhimmanci shi ne kamata ya yi a yi bincike da kuma nazari kan abubuwan da suka faru a yayin gasannin motsa jiki da aka yi.

A yayin gasa tsakanin kungiyar kasar Sin da ta kasar Saudiyya, babban malamin horaswa Gao Hongbo ya gabatar da damar shiga gasa ga yawancin 'yan wasa, wato 29 dake cikin 31 na dukkan 'yan wasan wannan kungiya sun shiga wannan gasa. A sanadin haka, malaman horaswa na kungiyar sun cim ma burinsu na duba halin da 'yan wasa ke ciki. Kan wannan batu, Gao Hongbo ya nuna gamsuwarsa, ya ce:  "Mun yi karawa da kungiyoyi uku cikin kwanaki goma, mun yi kokari. Ban da wannan kuma, bisa matsayina na babban malamin horaswa, bari in gaya muku cewa, na samu babban sakamakon da nake bukata a yayin gasanni."

A hakika dai, bayan wadannan gasanni, Gao Hongbo ya fara fidda tsarin fasahar horaswa don bunkasuwar kungiyar wasan kwallon kafa dake karkashin jagorancinsa a nan gaba. Ko shakka babu, wannan batu yana da muhimmanci kwarai ga sabuwar kungiyar wasan kwallon kafar maza ta kasar Sin.

Koda yake a halin da ake ciki yanzu, matsayin kungiyar kasar Sin bai kai matsayin koli a duniya ba tukuna, amma, a yayin gasa, mun tarar da cewa, 'yan wasan kasar Sin sun riga sun kara fahimtar halin gasa nagari yadda ya kamata, saboda a ko da yaushe, babban malamin horaswarsu Gao Hongbo yana ihu kamar haka: "Kada ku janye jiki, ku kara yin kokarin sarrafa kwallo."

Game da nufinsu a nan gaba, Gao Hongbo ya ce,  "Nufin karshe na wannan kungiya shi ne shiga gasar kofin duniya da za a yi a kasar Brazil a shekarar 2014, yanzu, muna yin kokarin kasancewa cikin kungiyoyi 32 mafiya karfi a duniya." (Jamila Zhou)