Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-06-23 20:47:18    
Birnin Chengde yana kokarin zama wani birnin da ke da yanayi mai daukar sauti

cri
Birnin Chengde na arewa maso gabashin lardin Hebei da ke makwabtaka da birnin Beijing. A cikin 'yan shekarun da suka gabata, lokacin da ake kokarin samun ci gaban tattalin arziki, birnin Chengde yana ta yin aikin kiyaye ingancin yanayi mai daukar sauti, kuma yana kara saurin raya sana'o'in da ke amfani da makamashi mai tsabta. Sakamakon haka, yanzu birnin Chengde ya riga ya zama wani bangon da ke hana yashi taba biranen Beijing da Tianjin, kuma ya zama muhimmin wurin da ke samar wa wadannan manyan birane biyu ruwan sha mai tsabta. A cikin shirinmu na yau, za mu bayyana muku yadda birnin Chengde yake kiyaye ingancin yanayi mai daukar sauti da kuma amfani da makamashi mai tsabta.

Ya kasance da kimanin kilomita dari 2 a tsakanin birnin Chengde da birnin Beijing. Birnin Chengde yana da arzikin ma'adinai, musamman yawan adanannen arzikin karkashi na zinariya da ke yankunan birnin Chengde yana matsayi na farko a duk lardin Hebei. Sannan yana da dimbin albarkatun karkashin kasa kamar farin karfin molybdenum da azurfa da tagulla da zinc da duwatsu masu tauri kuma masu kyan gani. Daga cikin wadannan ma'adinai, yawan dutsen vanadium da dutsen titanium da aka gano a yankunan birnin Chengde ya kai kimanin ton biliyan 7, watau yana kan gaba a duk duniya. Sabo da haka, ana kuma kiran birnin Chengde "babban birnin da ke da arzikin duwatsun vanadium da titanium". Amma lokacin da ake tsara shirin raya tattalin arziki, gwamnatin birnin Chengde ta sanya sana'o'in da ke amfani da makamashi mai tsabta kuma ke tabbatar da ingancin muhalli a matsayin da za a raya su a gaba. Mr. Zhang Gujiang, magajin birnin Chengde ya ce, "Ko da yake birninmu yana da arzikin ma'adinai, tattalin arzikinmu yana cikin lokacin ci gaba baki daya. Amma dole ne mu tsaya wajen daidaita huldar da ke tsakanin batutuwan ci gaban tattalin arziki da kyautata zaman rayuwar jama'a da kiyaye ingancin yanayi mai daukar sauti. Wato, lokacin da muke hako ma'adinai, ba mu iya dogara da ma'adinai kawai ba, dole ne mu kyautata tsarin sana'o'inmu da raya tattalin arzikin bola jari da aiwatar da manufofin tabbatar da ingancin muhalli."

Idan ana son raya birnin da ya zama wani birni mai kyan gani, dole ne a kayyade, a kuma yi watsi da masana'antun da ke batar da dimbin kudi da makamashi da kuma gurbata muhalli. Sabo da haka, birnin Chengde ya kara mai da hankali wajen bunkasa sana'o'in yawon shakatawa da masana'antun da ke amfani da makamashi mai tsabta da aikin gona da ke bayyana halin musamman da birnin ke ciki. A waje daya kuma, ya riga ya rufe masana'antu masu gurbata muhalli 146. Bugu da kari kuma, birnin Chengde ya kara karfin yin tsimin makamashi da rage yawan gurbatattun abubuwan da ake fitarwa. Haka kuma, gwamnatin birnin Chengde ta kara sa ido kan yadda ake raya tattalin arzikin bola jari. Mr. Zhang Gujiang ya kara da cewa, "A lokacin da ake nazarin ayyukan da kananan hukumomi suka yi, mun sanya ayyukan kiyaye ingancin muhalli da suka yi a gaban kome domin tabbatar da ganin an rage yawan gurbatattun abubuwa da ake fitarwa a kai a kai."

Birnin Chengde muhimmin wuri ne da ke samar da ruwa mai tsabta ga birnin Beijing. Akwai kogin Luan da kogin Chao a cikin yankunan birnin Chengde. Yawan ruwan da ake sufuri daga kogin Chao zuwa madatsar ruwa ta Miyun ta Beijing ya kan kai cubik mita miliyan 470 a kowace shekara, wato ya kai kashi 59 cikin kashi dari bisa na jimillar ruwan madatsar ruwa ta Miyun. Daya cikin kowane kofn ruwa biyu da mazauna birnin Beijing suka sha ya zo daga birnin Chengde. An bayyana cewa, a shekarar da ake ciki, masana'antun sarrafa gurbataccen ruwa guda 7 za su soma aiki a binrin Chengde. Sakamakon haka, kowace gundumar da ke karkashin jagorancin gwamnatin birnin Chengde tana da wata masana'antar sarrafa gurbataccen ruwa. Irin wadannan masana'antun sarrafa gurbataccen ruwa ba su da girma, amma suna iya biyan bukatun da matsakaita da kananan garuruwa suke da su, kuma ruwan da ake sarrafawa a wadannan masana'antu yana da inganci. Mr. Zhang Gujiang, magajin birnin Chengde ya bayyana cewa, "Bisa shirin da muka tsara, yawan gurbataccen ruwa da za a iya sarrafawa a wadannan masana'antu zai kai ton dubu 190 a kowace shekara a cikin 'yan shekaru masu zuwa. Kuma za a kammala ayyukan gina su gaba daya a karshen shekara ta 2009. Sakamakon haka, ingancin ruwan kogi da ke cikin yankunan birninmu zai samu kyautatuwa sosai, kuma za a iya tabbatar da samar da ruwa mai tsabta ga biranen Beijing da Tianjin."

A waje daya, birnin Chengde ya kara karfin daidaita tsarin makamashin da yake amfani da shi domin tabbatar da kuma kyautata ingancin yanayi mai daukar sauti na birnin. Sabo da haka, yanzu yana kara saurin gina tasoshin da ke samar da wutar lantarki da karfin iska ko karfin ruwa da sauran makamashi maras gurbata muhalli.

Birnin Chengde yana wani wurin da ke hade da kwarin dutsen Yanshan da filaton Mongoliya. Sakamakon haka, yana da arzikin karfin iskar da za a iya yin amfani da ita domin samar da wutar lantarki. Ya zuwa yanzu, yawan karfin injunan samar da wutar lantarki da karfin iska ya riga ya kai kilowatts dubu 210. Hukumomin gwamnatin kasar Sin sun kuma amince da shirin gina wata tashar samar da wutar lantarki da karfin iska da karfinsa zai kai kilowatts miliyan 1 a birnin Chengde.

Bugu da kari kuma, Mr. Zhang Gujiang ya bayyana cewa, birnin Chengde zai kara karfin raya ayyukan samar da wutar lantarki da karfin ruwa. Yanzu ana nazarin samar da ayyukan samar da wutar lantarki da karfin ruwa na Fengning da ke kunshe da injunan samar da wutar lantarki da karfinsu ya kai kilowatts miliyan 3 da dubu dari 6. Kuma birnin Chengde yana namijin kokarin soma wadannan ayyuka a mataki na farko a karshen shekara ta 2009. Sannan kuma, birnin Chengde yana gaggauta aikin gina madatsar ruwa ta Shuangfeng domin biyan bukatun da ake da su wajen samar da ruwan sha da ruwan da ake amfani da shi ga muhimman masana'antu da kuma aikin ban ruwa. Dadin dadawa, birnin Chengde ya kuma samu ci gaba wajen yin amfani da karfin hasken rana da zafi daga karkashin duniyarmu da dai sauran makamashi mai tsabta. Zhang Gujiang ya kara da cewa , "Bisa shirin da muka tsara, ya zuwa shekara ta 2010, ayyukan samar da wutar lantarki da za mu soma yi zai kai na kilowatts miliyan 3. Sannan ya zuwa shekara ta 2015, wannan adadi zai kai kilowatts miliyan 10. Muna fatan birnin Chengde zai zama tasha mafi girma da ke samar da makamashi mai tsabta da ke arewa da birnin Beijing."

Bisa binciken da aka yi, yawan kwanaki da ingancin iskar cikin garin birnin Chengde ya yi kyau ya kai 320 a shekarar 2008. Yawan bishiyoyin da aka shusshuka a birnin Chengde ya kai fiye da kashi 51 cikin kashi dari bisa na fadin birnin Chengde. Kuma an riga an cimma burin "samun yanayin sararin sama mai launin shudi da yankunan da ke cike da bishiyoyi da duwatsu masu kurmi da ruwa mai tsabta" a yankunan birnin Chengde.

Ko da yake birnin Chengde ya riga ya samu ci gaba wajen tabbatar da ingancin yanayi mai daukar sauti, amma zai ci gaba da yin kokarin yin ayyukan tabbatar da ingancin yanayi mai daukar sauti, musamman zai kara saurin dasa bishiyoyi masu daukar sauti da bishiyoyi masu rigakafin afkuwar guguwar iska da yashi da bishiyoyin da za su iya samar da arziki da kuma bishiyoyin da za su girma cikin sauri da kuma ciyawa mai inganci. Ana fatan yawan bishiyoyin da za a dasa zai kai kashi 55.8 cikin kashi dari bisa fadin birnin Chengde a shekarar 2010. A cikin garin birnin Chengde, matsakaicin fadin filayen bishiyoyi na kowane mazauna birnin zai kai murabba'in mita 60. Mr. Zhang Gujiang ya kara da cewa, "Tabbatar da ingancin yanayi mai daukar sauti yana da muhimmanci. Kuma yanayi mai daukar sauti kuma mai inganci ya iya tabbatar da samun ci gaba ba tare da tangarda ba. Za mu yi kokarin sanya birnin Chengde ya zama birnin da ke cike da bishiyoyi da ruwa mai tsabta da lambunan shan iska da kuma dacewa da yin rayuwa da yawon shakatawa." (Sanusi Chen)