Tun daga watan Oktoba na shekara ta 2007, gidan rediyon kasar Sin, wato CRI ya kafa wani rediyonsa kan zango FM106 a birnin Yamai na Jamhuriyar Niger, inda ake watsa shirye-shiryen Hausa na sa'o'i 6 da na Faransanci na sa'o'i 10 tare da shirye-shiryen harshen Sinanci na sa'o'i 2 a kowace rana. Sabo da haka, muna da shirin daukar ma'aikata 2 da za su yi aiki a sashen Hausa na CRI da ke birnin Beijing, inda hedkwatar CRI take. Sharuda kan samun wannan gurbin aikin su ne:
sex: mace daya, namiji 1
shekarun haihuwa: tsakanin 25 da 35 kafin karshen watan Disamba na shekarar 2009
matsayin ilmi: a kalla takardar shedar karatun digiri a harshen Hausa
aikinka/ki a yanzu: wadanda suka yi a kalla shekaru 3 suna aiki a matsayin DJ ko mai jagorancin shirye-shirye a wani gidan rediyon FM.
Masu sha'awar yin aiki a sashen Hausa na CRI, sai su aiko mana wadannan takardu: takaitaccen bayani da kwafin shedar karatun jami'a da takardun nuna amincewa guda 2 da hoto zuwa e-mail: hausa@cri.com.cn. Ya kamata ku rubuta "neman gurbin aikin yi a CRI" da ya zama taken sakonku.
|