Ran 8 ga watan Mayu na shekarar 1949, aka haifi Mohammed Bin Hamman a kasar Qatar, ya taba yin aiki a kamfanin sadarwa na kasar, amma yanzu ya zama shugaban hukumar wasan kwallon kafa ta kasashen Asiya, kuma shi din memba ne na kwamitin zartaswa a hukumar wasan kwallon kafa ta kasashen duniya. A shiyyar yammacin Asiya, ya yi fice saboda yana da hali nagari, amma kafofin watsa labarai na Asiya suna da ra'ayoyi daban daban kansa. A cikin shirinmu na yau, bari mu yi muku bayani kan mallam Hamman.
Kafin mu fara tambayarsa game da yanayin aikinsa, Hamman ya gaya mana cewa, yana da 'ya'ya biyar, yana kaunarsu sosai da sosai, ya ce, "Ina kaunar dukkansu biyar, ina fatan suna dauka ta a matsayin babansu nagari."
Daga baya kuma, Hamman ya ce, makasudin wannan ziyarar da yake yi a kasar Sin shi ne kokarta habaka wasan kwallon kafa na matasa da yara a shiyyar Asiya, musamman ma a kasar Sin. Kamar yadda kuka sani, tsarin horaswa na wasan kwallon kafa na matasa da yara a Asiya yana a baya baya idan an kwatanta shi da na kasashen Turai, shi ya sa a kullum Hamman yake mai da hankali kan wannan aiki, yanzu, ana tafiyar da aiki wanda ke da lakabin "makomar Asiya" yadda ya kamata. Kan wannan batu, Hamman ya yi mana bayani da cewa, "Don habaka wasan kwallon kafa na matasa da yara a Asiya, mun zabi birane 28 domin yin farfaganda da kuma horaswa, kawo yanzu, a kai a kai matasa da yara na wadannan birane suna kara nuna sha'awar wasan kwallon kafa. A wadannan birane, a da, kila yara ba su da wurin yin wasan kwallon kafa, amma yanzu suna iya yin wasan a karshen mako, kuma suna jin dadin kuzarin da wasan ya kan ba su."
Koda yake wasu mutane a Asiya ba su gamsu da aikin da Hamman ke yi sosai ba, amma lallai ya yi kokari, kuma ya samu sakamako musamman ma wajen ingiza wasan kwallon kafa da kuma yin gyare-gyare kan babbar gasar zama zakara ta wasan kwallon kafa ta Asiya. Ko shakka babu, Hamman ya ba da tallafinsa ga bunkasuwar wasan kwallon kafa a Asiya.
Game da babbar gasar zama zakara ta wasan kwallon kafa ta Asiya ta shekarar 2009, Hamman ya gaya mana cewa, ya gamsu da wannan gasa sosai da sosai. Ya ce, "Ana iya cewa, babbar gasar zama zakara ta wasan kwallon kafa ta Asiya ta wannan shekara ta samu cikakkiyar nasara, 'yan kallo masu sha'awar wasan ko a filin wasa ko ta telebijin sun kara yawan gaske, in an ci gaba da sanya kokari, tabbas ne babbar gasar zama zakara ta wasan kwallon kafa ta Asiya za ta kara samun karbuwa a Asiya da kuma sauran kasashen duniya."
Kawo yanzu, Hamman ya riga ya zama shugaban hukumar wasan kwallon kafa ta Asiya a tsawon shekaru 7, a cikin wadannan shekaru 7, Hamman ya kan nace ga bin ra'ayinsa, shi ya sa wasu kungiyoyin wasan kwallon kafa na kasashen Asiya ba su gamsu da aikinsa ba, ban da wannan kuma, kafofin watsa labaran wasan motsa jiki na Asiya su ma su kan yi sharhi kan aikinsa. A watan Maris na bana, a fili Hamman ya zargi 'dan kasar Korea ta kudu Chung Moon-Joon, mataimakin shugaban hukumar wasan kwallon kafa ta kasashen duniya da cewa, ana tuhumarsa da ya bai wa hanci ga wasu kungiyoyin wasan kwallon kafa na Asiya domin neman samun goyon bayansu, ta yadda zai taimaka wa 'dan kasar Bahrain Sheikh Salman ya kada Hamman shi kansa a zaben memban zartaswa na hukumar wasan kwallon kafa ta duniya da za a yi a watan Mayu na bana. Yayin da muka takalo magana kan wannan batu, Hamman ya ce, "Gaskiyarku, ba na sonsa, shi ma haka, ba damuwa, karamar matsala ce, a hakika dai, ba na sa lura a kanta."
Wasu kafofin watsa labarai na Asiya sun taba yin sharhi kan Hamman kamar haka: "Hamman ya yi mulkin kama karya a Asiya, a sanadin haka, wasan kwallon kafa a wasu kasashe wadanda suka fi karfi a wannan fanni ya kara samun bunkasuwa, amma wasu kasashe marasa karfi wajen wasan kwallon kafa sun rasa ikon magana."
Game da wannan, Hamman ya kyautata tunani da cewa, abu mafi muhimmanci shi ne bisa matsayi na shugaban kungiyar wasan kwallon kafa ta Asiya, ya cancanci yabon da aka yi wa aikinsa. Hamman yana cike da imani ga makomar wasan kwallon kafa ta Asiya, ya ce, "Ko shakka babu, makomar wasan kwallon kafa ta Asiya tana da haske, a karkashin kokarin da za mu yi a cikin shekaru goma masu zuwa, kila matsayin wasan kwallon kafa na Asiya zai kai na kasashen Turai da Amurka."
Mun ji an ce, wasu kungiyoyin wasan kwallon kafa na Asiya sun yabi aikin Hamman sosai, amma wasu kuwa ba su gamsu da aikinsa ba. Kan wannan, Hamman yana fatan masu sha'awar wasan kwallon kafa na Asiya da na kasashen duniya za su kara mai da hankali kan aikin da ya yi a cikin 'yan shekarun da suka shige, amma ba kan abubuwan da ya fada ba kawai. Ya ce, "Na riga na yi aikin shugaban hukumar wasan kwallon kafa ta Asiya a shekaru 7, aikina ya sa hukumar wasan kwallon kafa ta Asiya da wasan kwallon kafa na Asiya sun samu manyan sauye-sauye, sai ku duba ku bincika da kuma yin sharhi kan kokarin da na yi kan aiki kamar yadda kuke so. Na hakkake cewa, za su zabe ni da na zama memban zartaswa na shiyyar yammacin Asiya na hukumar wasan kwallon kafa ta kasashen duniya."
Ran 8 ga watan Mayu na bana, membobin kungiyar wasan kwallon kafa ta Asiya guda 46 sun yi zabe kan memban zartaswa na shiyyar Asiya na hukumar wasan kwallon kafa ta kasashen duniya, a karshe dai, Hamman ya lashe mai takara da shi Sheikh Salman wanda shi ne shugaban hukumar wasan kwallon kafa ta kasar Bahrain tare da dan rinjaye. Hamman ya sake yin nasara. Abu mai ban sha'awa shi ne wannan rana ranar haihuwa ce ta Hamman, wato ya zuwa wannan rana, ya riga ya kai shekaru 60 da haihuwa. Ana iya cewa, nasarar da ya samu a wannan zabe babbar kyauta ce da aka ba shi musamman domin taya shi murnar cikarsa shekaru 60 a duniya. A nan, muna fatan Hamman zai ci gaba da yin kokari kuma zai samu cimma fatan alherinsa wato matsayin wasan kwallon kafa na Asiya zai kai na kasashen Turai da Amurka bayan kokarin da muke yi tare a cikin shekaru goma masu zuwa. (Jamila Zhou)
|