|
|
|
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye | more>> |
|
|
|
|
|
|
|
(GMT+08:00)
2009-06-09 15:42:57
|
|
Masana'antun zirga-zirgar jiragen sama na Afrika sun hada kai don magance matsalar kudi
cri
Masana'antun zirga-zirgar jiragen sama na duniya su ma sun gamu da illar da matsalar kudi ke kawowa, ciki har da na Afrika. Yanzu, masana'antun zirge-zirgar jiragen sama daban daban na Afrika suna daukar matakai a jere, kamar su kulla kawance, da habaka kasuwannin shiyyar, da dai sauransu, don kawar da matsalolin da ake fuskanta a yanzu tare.
Mataimakin shugaban majalisar sufuri ta zirga-zirgar jiragen sama ta duniya , wanda ke kula da harkokin Afrika ya ce, yawan rabon kasuwa da masana'antun zirga-zirgar jiragen sama na Afrika suka samu a nahiyar yana ta raguwa, sakamakon shigowar da masana'antu na duniya suka yi. Kamar misali, a farkon shekarar da muke ciki, kamfanin Zambia Airways ya dakatar da zirga-zirgar jiragen sama ala-tilas. Sabo da haka, tilas ne masana'antun sifirin jiragen su daidaita manufofinsu, don magance kalubalen.
Masugudanar da harkokin sifirin jiragen sama a Afrika suna ganin cewa, ta hanyar kulla kawance, da karfafa hadin kai, da hada kayayyakinsu, da rage yawan kudin da suke kashewa ne kawai, za su iya kyautata muhallin da ake ciki a yanzu. Babban sakataren hadaddiyar kungiyar kamfanonin sifirin jiragen sama ta Afrika ya ce, tilas ne a hade kananan masana'antun sifirin jiragen sama na Afrika, ko su shiga gamayyar masana'antun sifirin jiragen sama ta shiyyar, ta yadda za su iya yin takara tare da masana'antu daga sauran shiyyoyi.
Yanzu, da akwai manyan gamayyar masana'antun sifirin jiragen sama guda uku ne a duniya, wadannan gamayya kuma sun sanya mambobinta da su kara ribar da suka samu bisa babban mataki, a waje daya kuma sun habaka kasuwanni mafi yawa.
Wani jami'in wata mujalla game da sifirin jiragen sama ya bayyana cewa, idan kamfanonin sifirin jiragen sama na Afrika suka hada kansu, don kafa gamayya, to za su iya rage kudaden da suke kashewa kan gudanar da harkokinsu da yawansu ya wuce dalar Amurka biliyan daya, kazalika kuma za su habaka kasuwarsu a shiyyoyin da ke da wuyar zuwa, da kuma warware matsalar rashin yin cudanya tsakanin wurare daban daban na Afrika, sakamakon rashin samun sauki a fannin sufuri.
Kan kafa dangantakar hadin kai kuma, wasu kamfanonin jiragen sama na Afrika sun soma yin kokari kan wannan, amma har zuwa yanzu ba su samu ra'ayi iri daya a fannin kafa babbar gamayya ta dukkan nahiyar ba. Kamar misali, kamfanin RAM, wato Royal Air Maroc, da kamfanin sifirin jiragen sama na Senegal, wato ASI suna neman habaka harkoki a yammacin Afrika, da tsakiyar Afrika tare. Kamfanin Ethiopian Airlines, wato ETRTH, da kamfanin South African Airways, wato SAA, da kuma kamfanin Angola Airlines, wato TAAG sun kafa wani kamfanin hadin kai.
Bayan haka kuma, kwanan baya, kamfanonin sifirin jiragen sama na Afrika sun soma karfafa hanyoyin raya kasuwar sifirin jiragen sama a Afrika, don magance kalubalen da kamfanonin sauran shiyyoyi ke kawowa. Ciki kuma, kamfanin Kenya Airways ya kara hanyoyin sifirin jiragen sama a babban yankin Afrika, a waje daya kuma, ya sayi sabbin jiragen sama don biyan bukatun nahiyar Afrika. Kamfanin Virgin Nigeria kuma yana da shirin kara hanyoyin zirga-zirgar jiragen sama daga Lagos zuwa Kinshasa, da kuma daga Banjul zuwa Freetown. Dadin dadawa kamfanin Air Malawi zai kara yawan jiragen sama da ke kan hanyoyin zirga-zirga daga Dar es Salaam zuwa Johannesburg, don biyan bukatun kasuwannin shiyyar.
|
|
|