Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-06-08 17:59:57    
Masana'antu kanana da matsakaita na kasashen Sin da Larabawa za su inganta hadin gwiwarsu

cri
Ran 8 ga wata, a birnin Ningbo na lardin Zhejiang, an bude taron tattaunawa kan yin hadin gwiwa a tsakanin masana'antu kanana da matsakaita na kasashen Sin da Larabawa da Sin da Afirka. A yayin taron na tsawon kwanaki 2, masu masana'antu kanana da matsakaita kusan dari 1 da suka zo daga kasashen Larabawa za su yi shawarwari da takwarorinsu na kasar Sin kan yin ciniki. Sun nuna cewa, a sakamakon matsalar hada-hadar kudi ta duniya a yanzu, ya kamata masana'antu kanana da matsakaita na bangarorin 2 su inganta hadin gwiwarsu a hakikakin fannoni domin jure wahala tare.

A yayin bikin bude taron, Li Jinjun, darektan kwamitin shirya taron tattaunawar kuma mataimakin shugaban sashen yin cudanya da kasashen waje na kwamitin tsakiya na Jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin ya yi jawabin cewa,"Matsalar kudi ta duniya ta kawo wa masana'antu na kasashe masu tasowa, musamman ma masana'antu kanana da matsakaita wahalhalu. Jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin tana son gama kanta da jam'iyyun kasashen Larabawa da Afirka da suke sada zumunci a tsakanin juna domin yin kokarin sa kaimi kan masana'antu kanana da matsakaita su inganta hadin gwiwarsu da jure wahala tare."

Lardin Zhejiang, wani lardi ne da ake samun masana'antu kanana da matsakaita da yawa. Alal misali, a birnin Ningbo, akwai masana'antu kanana da matsakaita fiye da dubu 80, wadanda suke da muhimmanci matuka a fannin raya tattalin arzikin wurin. Chen Guoqiang, mataimakin babban sakataren gwamnatin birnin Ningbo, kuma mataimakin darektan zartaswa na taron tattaunawar ya yi karin bayani da cewa,"Matsalar kudi ta duniya ta kawo wa wasu masana'antu kanana da matsakaita na lardinmu, musamman ma birninmu babbar illa kai tsaye. Muna daukar matakai da yawa domin jure wahala. Wani muhimmin mataki da muke dauka shi ne raya sabbin kasuwanni, kamar wadanda suke a kasashen Afirka da na Larabawa. Muna yin hadin gwiwa tare a fannin yin cinikin waje, ta haka za mu iya samun sabbin kasuwanni da kafa sabbin hanyoyin ciniki."

Sa'an nan kuma, masana'antun kasashen Larabawa da suke halartar taron tattaunawar suna fatan yin hadin gwiwa da takwarorinsu na kasar Sin masu karfi a fannin kera kayayyaki domin kyautata fasaharsu, za su nemi shigar da jarin kasar Sin domin samun isasshen kudi ta fuskar raya kansu. Hashim Mohamed, babban darektan wani kamfanin sarrafa amfanin dabbobin gida na kasar Sudan ya ce,"Muna bukatar yin hadin gwiwa a fannonin masana'antu da aikin gona da sarrafa abinci da dai sauransu, wadanda ke dacewa da masana'antu kanana da matsakaita. Ban da wannan kuma, muna fatan Sin za ta ba mu rancen kudi na dogon lokaci ko kuma matsakaicin lokaci wajen raya muhimman ayyuka a kasarmu ta Sudan. Muna sa ran samun sakamako a wannan fanni a yayin wannan taron tattaunawa."

Bakin da suka zo daga kasashen Larabawa masu halartar taron sun nuna babban yabo ga wannan taron tattaunawa. A ganin Mohamed S. Ismail, jakadan kasar Iraki a kasar Sin, wannan taron tattaunawa ya sa kaimi kan yin hadin gwiwa a tsakanin kasashen Sin da Larabawa, ya kuma kyautata dangantaka a tsakaninsu ta fuskar siyasa da tattalin arziki, inda ya ce,"Taron tattaunawa da ake yi a wannan karo ya inganta da raya hadin gwiwa a tsakanin bangarorin 2 ta fuskar ciniki da siyasa da tattalin arziki. Zai kuma raya irin wannan hadin gwiwa zuwa sabon mataki. An shirya wannan taron tattaunawa ne domin yin tattaunawa da shawarwari kan muhimman batutuwan da ake bukatar a warware su cikin gaggawa a halin yanzu. Kasashen Sin da na Larabawa dukkansu suna Alla-Alla wajen halartar taron, kuma suna neman raya dangantaka a tsakaninsu ta fuskar siyasa da tattalin arziki ta hanyar halartar taron."(Tasallah)