Masu saurare, kirkiro da yin amfani da wayar tafi-da-gidanka dake dauke da kalmomin kabilar Tibet, ba ma kawai ya kawo sauki ga zaman rayuwar manoma da makiyaya a jihar Tibet ba, har ma ya bunkasa harshe da kalmomin Tibet zuwa wani sabon zamani. Shugaban hukumar kula da harkokin fassara ta jihar Tibet, wanda kuma shi ne darektan ofishin kwamitin kula da aikin bunkasa harshe da kalmomin Tibet Mista Tsewang Banjor ya ce: "Harshe da kalmomin kabilar Tibet na da dadadden tarihi. Dole ne a tsara wasu ka'idoji, ta yadda za'a yi amfani da kalmomin Tibet masu tsawon tarihi a wannan zamanin da muke ciki ba tare da matsala ba."
Mista Tsewang Banjor ya kara da cewa, kasar Sin tana maida hankali sosai kan kiyaye da raya harshe da kalmomi na kabilar Tibet, a shekara ta 2004, Sin ta zuba kudi har Yuan miliyan 33 don kaddamar da wata manhaja dake dauke da kalmomin kabilar Tibet.
Dadin dadawa kuma, gwamnatin jihar Tibet ita ma tana maida hankali sosai da sosai kan aikin bada ilimi a fannin harshe da kalmomin Tibet. Ana koyar da harshe da kalmomin Tibet a makarantun firamare, da sakandare, gami da jami'o'i daban-daban a jihar. Mista Tsewang Banjor ya cigaba da cewa: "Za'a iya gada da yayata nagartattun al'adun gargajiya na kabilar Tibet, ta hanyar koyo, da yin amfani, da kuma bunkasa harshe da kalmomin kabilar. Daga shekara ta farko a makarantar firamare har zuwa makarantar sakandare a jihar, an kafa darussan koyar da harshe da kalmomi na Tibet. A wasu jami'o'i da kwalejoji kuma, an kafa fannonin ilimi na musamman don nazarin harshe da kalmomi na Tibet." 1 2 3
|