Masu sauraro, idan ba ku manta ba, tun daga ran 15 ga watan Oktoba na shekarar da ta gabata, muka fara gasar kacici-kacici dangane da "ni'imtattun wurare a lardin Sichuan na kasar Sin", inda muka bayyana wa masu sauraronmu wurare masu ni'ima na lardin Sichuan da al'adun al'ummar wurin da kuma dadadden tarihinsa, kuma a ran 15 ga watan Afrilu na wannan shekara, muka kawo karshen gasar. A cikin tsawon rabin shekara, gaba daya sassa daban daban na tashar CRI sun samu amsoshin masu sauraro sama da dubu 520 da suka zo daga kasashe da shiyyoyi 151, ciki har da masu sauraron sashen Hausa da suka fito daga Nijeriya da Nijer da Kamaru da Ghana da Senegal da dai sauransu.
Bayan da muka kawo karshen gasar, mun sha samun sakwannin masu sauraronmu, wadanda suka nemi sanin sakamakon gasar, wato wadanda suka yi fice a cikin gasar. To, masu sauraro, yau ga shi ina farin cikin sanar muku da cewa, mun riga mun fito da wadanda suka yi nasara a gasar, kuma za mu fara da wadanda suka samu nasara cikin rukuni na uku.
Wadanda suka zo na uku su ne:
Maryam Abubakar Yiraso
P.O.Box 41 Numan
Adamawa State
Nigeria
Abba Ibrahim Wanzam
P.O.Box 66
Darazo L.G.A
Bauchi State
Nigeria
Balarabe Abdu Tela
P.O.Box 2483 Bau
Bauchi State
Nigeria
Aisha Abubakar Tukur
P.O.Box 1678
Maiduguri
Borno State
Nigeria
Jummai Haruna
P.O.Box 110 Biu
Borno State
Nigeria
Fatsuma Adamu
P.O.Box 474
Gombe
Gombe State
Nigeria
Abdullah Bala
P.O.Box 266
Bawku
Upper East Region
Ghana
Ado Amadu Medi
Medu Special Primary School
P.O.Box 9 Gumel
Jigawa State
Nigeria
Abubakar Halilu
Govt.Commercial College
P.O.Box 231 sabon gari zaria
Kaduna State
Nigeria
Lawal B.Usman
P.O.Box 1420 Zaria
Kaduna State
Nigeria
Auwalu Haruna Giginyu
Kano Capital School
P.O.Box 1058 Kano
Kano State
Nigeria
Abdullahi Sodangi
P.O.Box 1456 Katsina
Katsina State
Nigeria
Umar Mohammed
P.O.Box 169 Argungu
Kebbi State
Nigeria
Olanrewaju Dauda
P.O.Box 75455
Victoria Island Lagos
Lagos State
Nigeria
Hadiza Hamisu
Moro River
P.O.Box 253
Titin Wanba Akwanga
Nasarawa State
Nigeria
Wadanda suka zo na biyu su ne:
Hamza hamza
BP 80
Ngaoundere
Cameroon
Namadina Yahaya
Ingenieur en Informatique
36,Fass Louveau
BP 12344 Dakar
Senegal
Shugaba.Yahaya Salihu
P.O.Box 114
Akwanga
Nasarawa State
Nigeria
Haruna Ibrahim
P.O.Box 249 G.P.O
Dugbe Ibadan
Oyo State
Nigeria
Salisu Muhammad Dawanau
Finance Department
NSPMC Limited
P.M.B. 144 Abuja
Nigeria
Mustapha Ndawashi
P.O.Box 763,
Bida
Niger State
Nigeria
Muh'd Sani Musa
C/o Auwalu Abba
P.O.Box 889 Jos
Plateau State
Nigeria
Mohammed Gaude
P.O.Box 1697 Sokoto
Sokoto State
Nigeria
Adamu Abubakar Dan Jarida
P.O.Box 181
Jalingo Muri
Taraba State
Nigeria
Shu'aibu Gandu
Unguwar Dangara Tsafe LGA
P.O.Box 13
Zamfara State
Nigeria
Wadanda suka zo na farko su ne
Shugaba Bello Abubakar Malam Gero
P.O.Box 4039 Sokoto
Sokoto State
Nigeria
Shugaba Ibrahim Z.Othman
P.O.Box 911 Zaria
Kaduna State
Nigeria
Mamane Ada
P.O.Box 420
Niamey
Niger
Shugaba Musa Adamu Abubakar
P.O.Box 564
Gombe
Gombe State
Nigeria
Yahaya Ahmadu
Centre of the study of Nig.Languages
Bayero University Kano
PMB 3011
Kano State
Nigeria
To, dukkan ma'aikatan sashen Hausa na gidan rediyon CRI muna taya wadannan masu sauraro namu murna, kuma za mu turo muku kyaututtuka bisa ga yadda muka alkawarta. Sa'an nan, wadanda ba su yi nasara ba, kada dai ku yi kasa a gwiwa, kun yi kokari, kuma muna fatan za ku rubanya kokarinku a gasar kacici-kacici da za mu shirya a nan gaba, ko ba dade ko ba jima, nasara ta Allah ce.
Bayan haka, masu sauraro, muna kuma farin cikin sanar da ku cewa, a wannan karo, mun sami wani mai sauraron da ya samu lambar yabo ta musamman, wato shi ne Mohammed Idi Gargajiga daga Gombe, tarayyar Nijeriya, wanda zai samu damar zuwa nan kasar Sin ziyara, kuma a kwanan baya, malam Mohammed ya turo mana sakon cewar, ya riga ya sami visa, kuma ya ce, "Yanzu zan iya cewa kasar sin salamu alaikum, domin na shiga sabon babi na Duniyarmu ta abokantaka na Sin da Afrika." Sa'an nan, bisa wani sabon labarin da muka samu, an ce, malam Mohammed zai iso nan birnin Beijing a ran Lahadi, wato ran 24 ga wata, sabo da haka, fatanmu shi ne ka iso lafiya, da hannu biyu biyu muke nan muke maraba da zuwanka kasar Sin!
Bayan haka, masu sauraro, muna kuma sanar da ku cewa, "shekarar da muke ciki shekara ce ta cika shekaru 60 da kafuwar Jamhuriyar Jama'ar Sin. Sabo da haka, CRI za ta shirya "gasar kacici-kacici ta murnar cika shekaru 60 da kafuwar sabuwar kasar Sin" tun daga ran 1 ga watan Yuni zuwa ran 1 ga watan Satumba na shekarar da ake ciki ta rediyo da kuma yanar gizo, domin kara wa masu sauraronmu fahimtar sauye-sauyen da kasar Sin ta samu a cikin wadannan shekaru 60 da suka gabata ta fannonin tattalin arziki da zaman al'umma da dai sauransu. Za mu gabatar muku da gasar ta shirye-shiryenmu na rediyo, haka kuma za mu sanya ta a kan shafinmu na yanar gizo, wato www. Hausa.cri.cn. Muna kuma kira gare ku da ku yi kokarin shiga gasar,da fatan Allah zai sa ku samu nasara. (Lubabatu)
|