Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-05-20 14:18:48    
Sichuan za ta sami damar karbar bakuncin gasar wasa kwakwalwa ta kasar Sin a karo na farko

cri
A watan Nuwamba na shekarar da muke ciki, za a yi gasar wasa kwakwalwa ta kasar Sin a karo na farko a birnin Chengdu, babban birnin lardin Sichuan a kudu maso yammacin kasar Sin. A wancan lokaci, 'yan wasan dara da masu kada kati da suka fi yin fice a kasar Sin za su kara da juna a cikin wasannin. A halin yanzu dai, mazauna birnin Chengdu da suke himmantuwa wajen sake gina gidajensu bayan mummunar girgizar kasa ta Wenchuan suna yin marhabin da wannan kasaitacciyar gasa da hannu biyu biyu.

Da zummar sa kaimi kan bunkasa gasar wasa kwakwalwa, kamar wasan dara da kada kati, da ingantuwar matsayin 'yan wasa, da kuma kara kyautata zaman rayuwar jama'a ta fuskar al'adu a lokacin hutu, Sinawan da suke sha'awar wasan dara da kada kati sun yi aniyar shirya wata gasa da ta hada da dukkan wasannin dara da kada kati a duk fadin kasar Sin a karo na farko. Saboda haka, sun fitar da gasar wasannin kwakwalwa ta duk kasar a karo na farko da za a yi a birnin Chengdu na lardin Sichuan a ran 13 zuwa 23 ga watan Nuwamba na shekarar bana. Nan gaba za a ci gaba da shirya wannan gasa sau daya a ko wadanne shekaru 4. An samar da manyan wasanni guda 6 tare kuma da kananan wasanni guda 43 a yayin gasar wasa kwakwalwa ta kasar Sin a karo na farko. An kiyasta cewa, mutane fiye da 2500 daga sassa daban daban na kasar Sin za su shiga gasar. Fan Guangsheng, mataimakin darektan cibiyar kula da wasannin dara da kada kati ta babbar hukumar wasannin motsa jiki ta kasar Sin ya yi karin bayani da cewa,"Mun samar da manyan wasanni guda 6, wato darar Weiqi da ake yi da 'ya'yan dara masu launin fari da baki a kasashen Sin da Japan da Korea ta Kudu, da dara irin ta gargajiya ta kasar Sin da ta kasashen waje da darar kwado da darar jera 'ya'yan dara 5 a layi guda da kuma kada kati. Sa'an nan kuma, mun fitar da kananan wasanni ne da zummar samar wa 'yan wasa masu karfi damar karawa da juna da kuma karfafa gwiwar sabbin jini da masu sha'awar wasan."

Sanin kowa ne, a shekarar bara, lardin Sichuan ta gamu da mummunar girgizar kasa. Yanzu mazauna wurin suna dukufa wajen sake gina gidajensu, to, yaya za su iya shirya irin wannan kasaitacciyar gasa? Kuma mene ne gasar za ta samar musu? A lokacin da take yin magana kan ainihin nufin lardin Sichuan game da shirya gasar, Zhu Ling, shugabar hukumar wasannin motsa jiki ta lardin Sichuan ta bayyana cewa, lardin Sichuan tana fatan shirya gasar wasa kwakwalwa ta kasar Sin a karo na farko za ta iya ba da taimako wajen nuna wa jama'a yadda mazauna Sichuan suke himmantuwa wajen sake gina gidajensu a yanzu bayan aukuwar girgizar kasa ta Wenchuan, tare kuma da ruhunsu na neman samun ci gaba.

Ana mayar da birnin Chengdu tamkar birni ne na wasan dara a kasar Sin. A wannan birni, akwai dimbin mutanen da suka yi fice wajen yin wasan dara na Weiqi da irin na gargajiya na kasar Sin gami da masu sha'awar wasan dara da kada kati masu tarin yawa da ba a iya kidaya yawansu ba. Rahoton da hukumar kididdiga ta kasar Sin ta bayar ya shaida cewa, tsawon lokacin da ko wane mazauni lardin Sichuan ya kan kashe domin yin wasan dara da kada kati a ko wace rana ya fi matsakaicin tsawon lokacin na kasar Sin sosai. Haka kuma, ya fi tsawon lokacin da ake dauka wajen karanta littattafai da mujalloli, da yin amfani da yanar gizo ta internet, da motsa jiki da sauran harkokin hutawa. Musamman ma bayan aukuwar bala'in,an kasa gudanar da manyan harkokin nishadi da nuna fasaha da wasannin motsa jiki a Sichuan, shi ya sa yin wasan dara da kada kati suka fi dacewa ga mazauna Sichuan masu aiki tukuru a lokacin hutawa. Fan Guangsheng, mataimakin darektan cibiyar kula da wasan dara da kada kati yana mai cewar,"A shekarar bara, lardin Sichuan ya gamu da mummunan bala'in girgizar kasa. Yanzu mazauna wurin suna dukufa wajen sake gina gidajensu. A daidai wannan lokaci, lardin Sichuan ya nemi shirya gasar wasa kwakwalwa ta kasar Sin a karo na farko. Wannan ya nuna mana karfin zuciyar jama'ar da ke zaune a lardin Sichuan."

Duk da haka, mutane da yawa suna nuna damuwar cewa, ko da yake mazauna lardin Sichuan na da kyakkyawan burin shirya gasar, amma ko suna da isasshen karfin shirya irin wannan kasaitacciyar gasa ta babban mataki? Ko da yake shirya irin wannan gagarumar gasa na da matukar wahala a fannoni daban daban. Amma bayan da hukumar wasannin motsa jiki ta kasar Sin ta sha yin nazari, tana ganin cewa, lardin Sichuan yana iya biyan bukatun shirya gasar wasannin kwakwalwa ta kasar Sin, haka kuma, karfinsa na gudanar da ayyuka da kuma fasahohinsa na shirya gasanni sun samu babban yabo. Xiao Min, mai ba da taimako ga shugaban hukumar wasannin motsa jiki ta kasar Sin ta yi bayani da cewa,"Yankin Chengdu na da kyakkyawan sharadi na shirya gasanni da kuma isassun fasahohin shirya manyan gasanni. Tabbas ne zai iya yin amfani da ruhun wasannin Olympic da na yaki da bala'in girgizar kasa, mazauna wurin za su hada kansu domin samun cikakkiyar nasarar shirya gasar wasa kwakwalwa ta kasar Sin a karo na farko."

Yanzu ya rage rabin shekara daya kawai a bude gasar wasa kwakwalwa ta kasar Sin a karo na farko. Birnin Chengdu, babban birnin lardin Sichuan yana share fagen gasar cikin himma. Masu shirya gasar suna fatan za su iya bayyana karin halayen musamman ta fuskar al'adu a yayin gasar. Liu Siming, darektan cibiyar kula da wasan dara da kada kati ta hukumar wasannin motsa jiki ta kasar Sin ya yi nuni da cewa,"Bambanci mafi girma da ke akwai a tsakanin wasan dara da kada kati da kuma sauran wasannin motsa jiki shi ne wasan dara da kada kati na da dogon tarihi tare kuma da nuna halin musamman na al'adu. Shi ya sa dole ne mu mayar da shirya gasa ta babban mataki a gaba da kome. Za mu yi amfani da damar shirya taron baje-koli na al'adun wasan dara da kada kati domin shirya makala da kiran taron nune-nunen rubuce-rubuce da zane-zane da bidiyo da kayan wasan dara na gargajiya da littattafan bayani kan wasan dara da taron dandalin tattaunawa kan al'adun wasan dara da kada kati. Za mu kuma kara yin nazari kan al'adun wasan dara da kada kati da sake farfado da su, ta haka, za mu iya inganta halin musamman na wasan dara da kada kati ta fuskar al'adu da kuma kara tasirinsu a zaman al'ummar kasarmu."

Kamar yadda Mr. Liu ya fada, a yayin gasar wasa kwakwalwa ta kasar Sin a karo na farko da za a yi, masu shirya gasar za su gudanar da harkoki da dama, ciki har da shigar da wasan dara da kada kati a unguwanni da kuma jami'o'i, da taron baje-koli kan al'adun wasan dara da kada kati da dai sauransu. Mr. Liu Siming ya kuma kara da cewa, ma'aikatansa za su hada gasar da kuma aikin yaki da bala'in girgizar kasa da lardin Sichuan ke gudanarwa tare, don haka, ko wane dan wasan dara da mai kada kati zai iya ba da gudummawarsa wajen sake gina lardin Sichuan bayan bala'in. Kazalika kuma, a wannan lokaci, masu sha'awar wasan dara da kada kati da suka zo daga sassa daban daban na kasar Sin za su taru a birnin Chengdu, za su sami zarafin yin karawa da zakaru. Gasar da za a yi a watan Satumba na wannan shekara za ta zama dandamali mafi dacewa wajen nuna kyakkyawar surar lardin Sichuan da ake farfado da shi bayan aukuwar bala'in girgizar kasa.(Tasallah)