Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-05-19 10:43:53    
An shirya bikin mika injunan noma da kasar Zimbabwe ta saya daga kasar Sin

cri
A ran 15 ga wata a birnin Harare, hedkwatar kasar Zimbabwe, gwamnatocin kasashen Sin da Zimbabwe sun shirya bikin mika injunan aikin gona da kayayyakinsu na gyara da kasar Zimbabwe ta saya daga kasar Sin. Mr. Yuan Nansheng, jakadan kasar Sin a kasar Zimbabwe da ministoci 3 na gwamnatin kasar Zimbabwe wadanda suka halarci wannan biki sun yaba wa sakamakon da kasashen biyu suka samu a fannin yin hadin gwiwar aikin gona.

A yayin bikin, Mr. Yuan Nansheng, jakadan kasar Sin a kasar Zimbabwe ya ce, "An isar da wadannan injunan aikin gona a kasar Zimbabwe ne a daidai lokaci kuma a kan kari. Sabo da kayayyaki ne da suka wajaba wajen farfado da aikin gona na kasar Zimbabwe wadda take kokarin daidaita rikicin karancin hatsi. Hakan kuma wani muhimmin mataki ne da gwamnatin kasar Sin ta dauka domin tabbatar da ruhun taron koli na Beijing na dandalin tattaunawa tsakanin kasashen Sin da Afirka."

Tun daga watan Mayu na shekarar da ta gabata, gwamnatocin kasashen Sin da Zimbabwe sun soma yin hadin gwiwa a fannin aikin gona a karo na biyu. Bisa shirin da aka tsara, bankin kula da harkokin shige da fice na kasar Sin ya samar da rancen kudin da yawansa ya kai kudin Sin yuan miliyan 280 ga bangaren kasar Zimbabwe. Kamfanin hannun jari na "duniyar manoma" na kasar Zimbabwe ya yi amfani da wadannan kudi wajen sayen injunan noma fiye da 2480 da injunan girbin hatsi da injunan daukar kaya da injunan hako tabo da wasu kayayyakinsu na gyara daga kasar Sin. Za a yi amfani da wadannan injuna kan aikin gona kai tsaye domin nuna goyon baya ga manoma da farfado da aikin gona na kasar.

A yayin bikin mika wadannan injuna, Mr. Joseph Made, ministan aikin gona na kasar Zimbabwe ya tabbatar da muhimmiyyar rawar da wadannan injunan aikin gona kirar kasar Sin za su taka wajen zamanintar da aikin gona na kasar Zimbabwe. Mr. Made ya ce, "Kasar Zimbabwe na daya daga cikin kasashen da suka fi samun ci gaban aikin gona a Afirka. Na kan gaya wa manomanmu cewa, ya kamata su yi amfani da wadannan injunan aikin gona masu inganci sosai kamar yadda ya kamata. Mun san ingancin injunan aikin gona na kasar Sin kwarai sabo da muna yin hadin gwiwa sosai da masana harkar fasahohi na kasar Sin a kullum, kuma mu kan gaya musu abubuwan da muke bukata. Bisa wannan shiri, za mu iya zamanintar da tsarin ban ruwa da aikin gona na kasarmu."

A cikin jawabin da ya yi a yayin bikin, Mr. Thomas Nherera, mataimakin shugaban kamfanin hannun jari na "duniyar Manoma" na kasar Zimbabwe, wato kamfanin "Farmers World Holdings" ya bayyana cewa, "Kasar Sin, wato aminiyarmu da jakadanta a nan kasar Zimbabwe sun tabbatar da ganin mun kammala wannan shiri lami lafiya. Amma wannan ba zango na karshe ne ba, huldar hadin gwiwa da ke tsakaninmu za ta ci gaba."

Mr. Patrick Chinamasa, ministan harkokin shari'a na kasar Zimbabwe, aminin jama'ar kasar Sin ne ya kuma halarci bikin shi da kansa. A ganinsa, kasar Sin za ta zama wani muhimmin jigo a cikin ayyukan farfado da kasar Zimbabwe. Mr. Chinamasa ya ce, "Nauyi mafi muhimmanci da ke kan hadaddiyar gwamnatin Zimbabwe shi ne farfado da tattalin arziki. Muna tsammanin cewa, kasar Sin za ta taka muhimmiyar rawa wajen farfado da kasarmu. Kasar Sin na daya daga cikin rukunonin tattalin arziki mafi muhimmanci a duk duniya. Muna da imani cewa, kasashen Sin da Zimbabwe za su kafa huldar abokantaka a fannin tattalin arziki."

Lokacin da yake yin hasashe kan makomar hadin gwiwa da za a yi a tsakanin kasashen biyu, Mr. Yuan Nansheng ya ce, kasashen biyu za su iya kara yin hadin gwiwa a fannonin aikin gona da na kere-kere da ayyukan yau da kullum da dai makamantansu. (Sanusi Chen)