Jama'a masu karatu, shekarar da ake ciki shekara ce ta cika shekaru 60 da kafuwar Jamhuriyar Jama'ar kasar Sin. A cikin shekaru 60 da suka gabata, gwamnati da jama'ar kasar Sin sun dukufa ka'in da na'in wajen raya kasar. Sabo da haka, karfin kasar Sin ya samu dagawa sosai. Ingancin zaman rayuwar jama'a ma ya samu kyautatuwa a kai a kai. An kuma samu babban ci gaba a fannoni daban daban, kamar su fannonin masana'antu da aikin gona da kuma kimiyya da fasaha da dai sauransu. Tashar CRI za ta shirya "gasar kacici-kacici ta murnar cika shekaru 60 da kafuwar sabuwar kasar Sin" tun daga ran 1 ga watan Yuni zuwa ran 1 ga watan Satumba na shekarar da ake ciki ta rediyo da yanar gizo domin kara wa masu sauraronmu sanin sauye-sauyen da kasar Sin ta samu a cikin wadannan shekaru 60 da suka gabata a fannonin tattalin arziki da zaman al'umma da dai sauransu. Sabo da haka, sashen Hausa na gidan rediyon kasar Sin zai karanta muku bayanai 5 game da ci gaban da kasar Sin ta samu a cikin wadannan shekaru 60 da suka gabata tun daga ran 1 zuwa ran 5 ga watan Yuni. Sannan za mu maimaita su tun daga ran 6 zuwa ran 10 ga watan Yuli, sai kuma tun daga ran 3 zuwa ran 7 ga watan Agusta na shekarar da ake ciki. Muna fatan za ku gyara zama ku saurari wadannan bayanai biyar kuma za ku aiko mana amsoshinku game da tambayoyin da za mu yi a cikin wadannan bayanai biyar. Ba ma kawai za mu karanta muku wadannan bayanai biyar ta gidan rediyo ba, har ma za mu shigar da su a kan shafinmu na yanar gizo.
Idan kuna son shiga gasar ta yanar gizo, sai ku duba kan shafinmu na yanar gizo, wato http://hausa.cri.cn, sannan za ku iya aiko mana amsa ta e-mail na hausa@cri.com.cn. Muna fatan ku samu nasara a cikin gasar idan Allah ya yarda.
|