Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-05-14 16:57:03    
Wakilin WHO a nan kasar Sin ya nuna imani ga kasar Sin wajen shawo kan cutar murar A (H1N1)

cri

A ran 13 ga wata, an tabbatar da wani mutum na daban da ya kai shekaru 19 da haihuwa, kuma ya dawo daga kasar Canada ya kamu da cutar mura mai nau'in A (H1N1). Sakamakon haka, yawan mutanen da suka shigo da cutar a babban yankin kasar Sin ya kai guda 2. Kuma an riga an karya lagon kokarin hana shigowar cutar a kasar Sin da aka tsara.

Ko kasar Sin wadda ta taba fama da cutar SARS da murar tsuntsaye za ta iya hana barkewar cutar mura mai nau'in A (H1N1)? A wannan rana da yamma, lokacin da yake ganawa da wakilinmu, Dokta Hans Troedsson, wakilin kungiyar kiwon lafiya ta kasa da kasa, wato WHO da ke nan kasar Sin ya bayyana cewa, yana da imani ga kasar Sin wajen shawo kan cutar. Amma a waje daya ya nuna cewa, kasar Sin tana fuskantar kalubale mai tsanani wajen shawo kan cutar. Dokta Hans Troedsson ya ce, "Ina tsammani cewa, kasar Sin ta riga ta yi share fagen shawo kan cutar. Lokacin da muke hira da musayar ra'ayoyi da jami'an hukumar kiwon lafiya ta kasar Sin, matakan share fagen shawo kan cutar da gwamnatin kasar Sin ta dauka sun jawo hankulanmu sosai. Na fahimci matakan da gwamnatin kasar Sin ta dauka yanzu sabo da matakai ne da ke dacewa da dokoki da ka'idoji na tabbatar da kiwon lafiyar jama'a."

A cikin ofishinsa da ke nan birnin Beijing, Dokta Hans Troedsson ya jaddada ra'ayinsa da cewa, ko da yake yanzu an tabbatar da mutane biyu da suka kamu da cutar mura mai nau'in A (H1N1), amma idan ana ganin cewa cutar ta soma barkewa a kasar Sin, lokacin haka bai yi ba. A ganin Dokta Hans Troedsson, kasar Sin tana da dimbin fasahohin shawo kan irin wannan cutar. "A kwanan baya, na kai ziyara ga wasu wuraren kasar Sin. Dole ne na fadi cewa, kasar Sin tana da cikakkun hukumomin kiwon lafiya na matakin larduna da isassun ma'aikata da na'urori. A waje daya, yau da shekara 1 da ta gabata, lokacin da aka samu barkewar cutar baki da kafa, mun gano cewa, ma'aikatan kiwon lafiya na kasar Sin sun iya daidaita matsalar cikin sauri. A cikin gajeren lokaci ne suka yada bayanan shawo kan cutar a dukkan fadin kasar. Bugu da kari kuma, ba a cikin hukumomin kiwon lafiya kawai ba, a cikin makarantun midil da na firamare, dalibai sun samu ilmin yin rigakafin cutar. Idan kasar Sin ta yi amfani da wadannan hanyoyi domin shawo kan cutar mura mai nau'in A (H1N1), ko shakka babu, za su zama wani muhimmin karfi."

Amma yanzu an riga an shiga lokacin neman ci gaba na bai daya a duk duniya, cututtuka suna kuma yaduwa ba a cikin wata kasa kadai ba. Bayan da aka tabbatar da mutum daya da ya kamu da cutar mura mai nau'in A (H1N1), ba tare da bata lokaci ba gwamnatin kasar Sin ta sanar wa kungiyar WHO da sauran jama'a nan da nan. Game da matakan da gwamnatin kasar Sin ta dauka, Dokta Hans Troedsson ya ce, "Mun yaba wa gwamnatin kasar Sin sosai sabo da ta sanar mana da wannan labari cikin sauri. Yanzu a kowace rana, ana musayar bayanai a tsakaninmu da ma'aikatar kiwon lafiya ta kasar Sin. Kuma mu kan tattauna hanyoyin da ya kamata mu dauka domin yin rigakafi da kuma shawo kan cutar cikin hadin gwiwa. Muna samar wa ma'aikatar kiwon lafiya ta kasar Sin bayanai game da sauran kasashen duniya, tana kuma samar mana da labaru masu dumi-dumi game da yadda take shawo kan cutar."

Amma a matsayin babbar kasar da ke da mutane fiye da biliyan 1.3, kasar Sin tana da nauyi mai tsanani wajen shawo kan cutar mura mai nau'in A (H1N1). Dokta Hans Troedsson ya nuna cewa, yanzu kasar Sin tana fuskantar kalubale a fannoni 3. "Idan cutar ta barke a cikin dimbin mutanen da yawansu ya kai biliyan 1.3, wani kalubale ne mai tsanani sosai. A waje daya, bambancin da ke kasancewa a tsakanin yankuna daban daban na kasar Sin. Bugu da kari kuma, mutanen da su kan wuce a wurare daban daban sun yi yawa a kasar Sin. Sabo da haka, ana da wuyan sa ido kan yadda cutar take yaduwa." (Sanusi Chen)