Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-05-13 16:56:59    
Fadi albarkacin bakunanku game da yaki da bala'u daga indallah

cri

Masu sauraro, idan ba ku manta ba, a ran 12 ga watan Mayu na shekarar 2008 da ta gabata, girgizar kasa mai tsanani da karfinta ya kai digiri 8 ta afka wa lardin Sichuan da ke kudu maso yammacin kasar Sin, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane masu dimbin yawa. Bisa kokarin da bangarori daban daban suke yi, yanzu lardin Sichuan na farfadowa daga bala'in.

Hasali ma dai, 'yan Adam sun sha fama da bala'u daga indallah. A shekarar 2004, igiyar ruwa mai karfi da ake kira tsunami ta galabaitar da kasashen kudu maso gabashin Asiya, sa'an nan, a shekarar 2008, mahaukaciyar guguwa ta kawo wa kasar Myanmar manyan hasarorin rayuka da dukiyoyi. Kwanan baya ba da jimawa ba, wata girgizar kasa ta kuma yi sanadiyyar mutuwar daruruwan mutane a kasar Italiya. Kash, irin bala'u ba su lisaftuwa.

To, a zagayowar ranar 12 ga watan Mayu, wato ranar cika shekara daya da aukuwar girgizar kasa a lardin Sichuan na kasar Sin, shin kuna da abubuwan da kuke son fada mana, kuma a ganinku, me ya kamata dan Adam su yi don yaki da irin bala'u daga indallah? Muna fatan za ku aiko mana sakonni don fadi albarkacin bakunanku, don mu yi musanyar ra'ayoyi.

Kada kuma ku manta, adireshinmu na Email shi ne Hausa@cri.com.cn.

Sashen Hausa na CRI