A ko wace rana da yamma, dattijo Dong Zhenji ya kan yi yawo a kauyensu da aka sake ginawa. Dattijo Dong Zhenji yana cike da farin ciki sosai a lokacin da yake ganin sabbin gine-gine masu kyan gani. Gidan Gong Zhenji ya ruguje a cikin bala'in girgizar kasa da ta auku a ranar 12 ga watan Mayu na shekarar da ta wuce, ko da yake babu mutanen da suka ji rauni ko rasa rayuka a iyalinsa, amma dukkan dukiyoyinsu sun salwanta. Gidajen kwana na sauran iyalan da ke kauyen duk girgizar ta ragargaza su. Bayan aukuwar girgizar kasa, dattijo Dong Zhenji da iyalinsa sun yi zama a rumfuna na wucin gadi a karkashin taimako daga wajen gwamnatin wurin. Bayan rabin shekara da ta wuce kuma, sun shiga sabon gidansu. Tsoho Dong Zhenji ya gaya wa wakilinmu cewa, 'Ban taba yin tunanin cewa, zan iya zama a gidan kwana mai kyau kamar na yanzu ba. Ana samar da ruwa, da wutar lantarki, da kuma gas a babban ginin da muke zama a yanzu.'
Tsoho Dong Zhenji ya gaya wa wakilinmu cewa, ba su kashe kudi kan sabon gidansu ba. Gwamnatin wurin ce ta warware matsalar kudin sake gina gidaje ta hanyoyin ba da kudi da kasar ta yi, da samun taimakon kudi daga wajen bangarori daban daban na zaman takewar al'umma, da dai sauransu.
Tsoho Zhao Rude da ke zama a garin Luoshui na birnin Shifang ya kaura zuwa sabon gida a 'yan watannin da suka wuce. Zhao Rude ya ce, ko da yake a kan samu tartsatsin girgizar kasa tun shekara daya da ta wuce, amma ya kwantar da hankalinsa a cikin sabon gidansu. Ya ce, 'An tsara tsarin gidanmu ne bisa ma'aunin yaki da bala'in girgizar kasa, sabo da haka, yana da inganci mai kyau.'
Ba kawai ayyukan sake raya yankunan da ke fama da bala'in girgizar kasa sun gabatar da sabbin gidaje ga jama'ar wurin ba, har ma sun samar da damar samun aikin yi da dama. Fang Xu yana daya daga cikin mutanen da suka samu aikin yi a karkashin kokarin da gwamnatin wurin ta yi bayan aukuwar girgizar kasa. Ya ce, 'Yawan kudin da muka samu a yanzu ya karu sosai bisa na kafin aukuwar girgizar kasa. Gaskiya ne gwamnatinmu ta ba mu taimako sosai kan wannan.'
Babbar girgizar kasa ta kawo tasiri mai tsanani ga hankulan mutane masu fama da bala'in, musamman ma ga yara. Domin taimakawa yara kwantar da hankulansu, an kafa dakin ba da shawara kan halin 'dan Adam a dukkan makarantun da aka sake ginawa a yankuna masu fama da bala'in, a waje daya kuma, wasu makarantu sun kafa kwasa-kwasai na kide-kide da raye-raye, da dai sauransu, ta yadda dalibai suke iya mayar da hankulansu kan abubuwan da suke sha'awa, da kuma manta da girgizar kasar. Bayan haka kuma, bangarori daban daban na zaman takewar al'umma su ma sun bayar da taimako ga yara, abin da yara suka fi nuna sha'awa a kai shi ne, samun warkewa a kasashen ketare.
A makarantar sakandare ta Leigu, akwai dalibai 15 da suka je kasar Philipines don samun jiyya bisa gayyatar da aka yi musu. Fu Zhengyun, wata malama ta makarantar ta gayawa wakilinmu cewa, 'Wadannan yara sun kwantar da hankulansu sosai bayan da suka komawa daga Philipines. Dukkansu sun tsaida kudurin cewa, za su mayar da hankulansu kan karatu, domin karfafa karfinsu a fannoni daban daban, ta yadda za su iya saka wa dukkan zaman al'umma.'
|