Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-05-13 12:54:42    
Gwamnatin Mexico na daukar tsauraran matakai don farfado da tattalin arzikinta bisa babbar illar da cutar A H1N1 ke yi mata

cri

Aminai 'yan Afrika, ko kuna sane da cewa, an samu bullar annobar cutar A H1N1 a wassu kasashe da yankuna a karshen watan da ya gabata. Yanzu haka dai, irin wannan mummuwar cuta ta rigaya ta yadu zuwa kasashe 30 na duniya. Amma abin farin ciki shi ne kasar Mexico da cutar ta fi rutsa da ita tana kokarin maido da zamantakewar al'umma da na tattalin arzikinta sannu a hankali. Babu tantama, annobar cutarA H1N1 ta yi babbar illa ga bunkasar tattalin arzikin kasar Mexico. Kwanan baya dai, gwamnatin kasar ta Mexico ta fito da wasu jerin takamaiman shirye-shirye da zummar farfado da tattalin arzikinta.

Jama'a masu saurare, sanin kowa ne, tattalin arzikin kasar Mexico ta samu koma baya sosai sakamakon aukuwar rikicin hada-hadar kudi na duk duniya. Kwanan baya ba da dadewa ba, ministan kudi na kasar Mexico, Mista Agustin Carstens ya tabbatar da cewa, tattalin arzikin kasar ya rigaya ya tabarbare wato ken an ya samu koma baya sosai a watanni 3 na karshen shekarar bara da kuma watanni 3 na farkon shekarar bana. Annobar cutar AH1N1 ta kuma kara dakile tattalin arzikin kasar, wadda ta tafka mummunar asara da ta kai dolar Amurka biliyan biyu da miliyan dari uku. Ban da wannan kuma, ministan harkokin wajen kasar ta Mexico Mista Espinosa ya fadi cewa, kila asarar da kasarsa ta samu a sanadiyyar bullowar cutar AH1N1 za ta dauki kashi 1 cikin kashi 100 na GDP na kasar a shekarar da muke ciki; Dadin dadawa, ministan kudin kasar Mexico ta kiyasta cewa, bunkasar tattalin arzikin kasar za ta yi kasa da kashi 4.1 cikin kashi 100 a wannan shekara.

Sana'ar yawon shakatawa da kuma sana'ar zirga-zirgar jiragen sama su ne suka fi samun illa daga wannan mummunar cuta. Sana'ar yawon shakatawa ta kasance tamkar wani irin ginshiki na bunkasuwar tattalin arzikin kasar Mexico. Amma, kwanan baya, kasashe da dama sun haramta ziyarar bude da ido tsakaninsu da kasar ta Mexico bayan bullowar cutar AH1N1 a wannan kasa, hakan ya yi babbar illa ga sana'ar yawon shakatawa ta wannan kasa. Ministan yawon shakatawa na Mexico, Mista Rodolf Elizondo ya furta a shekaran-jiya cewa, da yake matafiya na kasashen ketare sun ragu sosai, shi ya sa sana'ar yawon shakatawa ta kasar za ta samu raguwa da kimanin dola biliyan hudu a wannan shekara. ' Bisa wannan hali dai', in ji shi, 'gwamnatin Mexico na cikin shirin kaddamar da wani shiri na ware kimanin dola miliyan casa'in don sa kaimi ga matafiya na cikin gidan kasar da su yi hutu a fadin duk kasar da kuma wajenta.

Jama'a masu saurare, kamar yadda kuka san cewa, sana'ar zirga-zirgar jiragen sama ta Mecixo ta rigaya ta shiga cikin mawuyacin hali a sanadiyyar hauhawar farashin mai da kuma faduwar ma'aunin musanye-musanyen kudin kasar wato Peso da dolar Amurka. An kiyasta cewa, masu yawon shekatawa daga ketare da hukumomin zirga-zirgar jiragen sama na Mexico za su dauka a wannan shekara zai yi kasa da kimanin kashi 28 cikin kashi 100. Domin warware wannan matsala, bankin yin cinikayya da ketare na kasar Mecixo zai tallafa wa sana'ar sufiri ta kasar don taimaka mata wajen aiwatar da shirin bunkasa sana'ar cikin dogon lokaci.

Aminai 'yan Afrika, yanzu haka, kasar Mexico ta samu kudin taimako daga kasa da kasa. Bankin duniya ya riga ya yi shelar bada rancen kudi daya ya kai dola miliyan dari biyu da wani abu ga Mexico; Ban da wannan kuma, asusun kudi na duniya IMF shi ma ya yi alkawarin samar wa wannan kasa rancen kudi.

Amma duk da haka, wassu manazarta sun yi hasashen cewa, zai yi wuya gwamnatin Mexico za ta iya shawo kan matsar tabarbarewar tattalin arzikin kasar cikin gajeren lokaci saboda mummunar annobar cutar AH1N1 da take rutsa da ita. ( Sani Wang)