Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-05-12 17:11:07    
Kiyaye hadin kai na Jam'iyyar ANC shi ne babban aikin da shugaba Zuma ke fuskanta, in ji masanin kasar Sin

cri
Cikin zaben da aka yi a kasar Afirka ta Kudu a ranar 22 ga watan Afrilu na shekarar bana domin zaben 'yan majalisun kasar, jam'iyyar ANC da Jacob Zuma ke shugabanta ta samu nasara bisa kuri'un da ta samu na kashi 65.9%, sa'an nan farin jinin shugaba Zuma a cikin bakar fatan kasar ya wuce jimillar sosai. Dangane da dalilin da ya sa shugaba Zuma ya samu irin wannan karbuwa a cikin jama'a, a ganin Zhang Yongpeng, wani masanin kasar Sin mai binciken batutuwan Afirka, shi ne domin asalinsa matalauci ne, kuma mayaki mai yin fama da akidar nuna wariyar launin fata.

'Dalilai da yawa sun sa Zuma ya samu farin jini sosai, da farko dai, ya kasance daya daga cikin manyan mutanen da suka kafa jam'iyyar ANC, ya taba zama gidan kurkuku a lokacin mulkin wariyar jinsi, amma duk da haka, ya tsaya kan aikin dakile akidar nuna wariyar launin fata. Sa'an nan dalili na biyu shi ne, ya samu asalinsa ne cikin al'ummar matalauta, shi ya sa ake sa ran cewa zai iya lura da moriyar bakar fata da matalauta sosai.'

A watan Satumba na shekarar 2008, Thabo Mbeki, shugaban kasar Afirka ta Kudu na lokacin, ya yi murabus. Batun ya janyo baraka ga jam'iyyar ANC, har ma wasu manyan kusoshin jam'iyyar sun bar matsayinsu, sun kafa wata jam'iyyar adawa. Shi ne ya sa Mista Zhang Yongpeng na ganin cewa, kiyaye hadin kai a cikin jam'iyyarsa ya zama wani babban aiki da ke gaban shugaba Zuma.

'Wani babban kalubalen da ake fuskanta shi ne, yaya za a kiyaye rinjaye a cikin majalisun kasar. Domin cikin zabe mai zuwa, jam'iyyun adawa ka iya kafa wani kawance don takara da jam'iyyar ANC. Shi ya sa ake bukatar daidaita manufa da ra'ayi a cikin jam'iyyar, ta yadda za a samu kiyaye hadin kai da karfin jam'iyyar.'

Zhang Yongpeng ya ce, manufa maras inganci da shugaba Mbeki ya dauka ta tsananta bambancin da ke tsakanin masu kudi da matalauta na al'ummar kasar, sa'an nan matakin dipolamasiyya da ya dauka shi ma ya haifar da rashin jin dadi a cikin jam'iyyar ANC da kuma tsakanin jama'ar kasar Afirka ta Kudu. Wadannan abubuwa, a ganin mista Zhang, sun sa Mbeki ya kasa samun goyon baya daga jama'a. Amma, yanzu wadannan matsaloli kan tattalin arziki da harkokin waje sun ci gaba da zaman kalubale ga shugaba Zuma. Zhang Yongpeng ya ce,

'Tattalin arziki shi ne fannin da aka fi samun kalubale, inda ta yaya za a sassanta bambancin da ke tsakanin mai kudi da matalauta ya zama matsala mafi daukar hankalin mutum. Bayan da Zuma ya hau karagar mulki, ba shi da damar yin kome, sai dai warware wannan matsalar, domin ya riga ya yi alkawarin sassanta matsalar, da kuma ware kudi don tallafa wa bakar fata. Sa'an nan ta fuskar harkar dipolamasiyya, ana bukatar kare karfin da kasar Afirka ta Kudu ke da shi na yin tasiri kan shiyyar da kasar ke ciki. Haka kuma ana tuhumar shugaba Zuma kan ko zai iya ciyar da aikin sulhuntawa da ake gudanar a kasar Zimbabwe gaba, da kuma daidaita rikicin da ake samu a sauran wurare na nahiyar Afirka ta hanyar lumana.' (Bello Wang)