Ran 12 ga watan Mayu na shekarar bana cika shekara guda da aukuwar bala'in girgizar kasa a lardin Sichuan a ran 12 ga watan Mayu na shekarar 2008. Wannan mummunar girgizar kasa ta girgiza mutanen Sin gami da na kasashen duniya matuka, ta kuma haddasa wa kasar Sin babbar asarar rayuka da dukiyoyi. Mutanen da bala'in ya shafa sun sha wahalhalu kwarai da gaske. Shi ya sa za mu gabatar muku da shirinmu na musamman dangane da lardin Sichuan a halin yanzu domin tunawa da cika shekara guda da aukuwar bala'in girgizar kasa ta Wenchuan.
A cikin shekara guda da ta gabata, mutanen da suke zaune a wuraren da bala'in ya shafa sun fuskanci kalubale mai tsanani. Suna samun waraka daga ciwon da bala'in ya kawo musu, tare kuma da sauke babban nauyin sake gina gidajensu. Sauran Sinawa kuwa suna nuna musu kulawa da ba su tallafi ta hanyoyi daban daban da zummar taimaka musu kawar da tsoron da bala'in ya kawo musu, ta haka za su iya farfado da zaman rayuwarsu yadda ya kamata cikin sauri. A cikin dukkan wadanda bala'in girgizar kasa ya shafa, yaran da suka zama marayu a sakamakon bala'in sun fi jawo hankalin mutane. Sun rasa iyayensu da iyalansu a lokacin da suke kanana. Dukkan bangarorin zaman al'ummar kasar Sin suna mai da hankali da kuma nuna musu kulawa sosai. A cikin shirinmu na yau, wakilinmu zai jagorance mu domin yin hira da wata yarinyar da ta zama marainiya a sakamakon bala'in.
"Sunana Suzi. Ina da shekaru 13 da haihuwa. Ina sha'awar wasan ninkaya kwarai da gaske. Sa'an nan kuma, ina kaunar yin wasa da fiyano. 'Ya'yan itatuwa da dabbar Panda su ma abubuwa ne da nake so."
Masu karatu, yarinyar da take gabatar da kanta a Turance a yanzu ita ce Qing Fangrui. Tana karatu a aji na bakwai a cikin makarantar Guangya da ke birnin Dujiangyan a lardin Sichuan. A ran 12 ga watan Mayu na shekarar bara, iyayenta sun je makarantar domin duba yadda take kasancewa a cikin awoyi da dama kafin aukuwar bala'in girgizar kasa. Amma ba su yi zaton cewa, ba za su iya sake saduwa bayan ran 12 ga watan Mayu na shekarar 2008 ba. A kan hanyar iyayen Qing Fangrui ta komawa gida cikin mota, a daidai lokacin da suke ratsa kusa da garin Yingxiu, mummunar girgizar kasar ta auku. Iyayenta sun bace, har yanzu ba a san inda suke ba tukuna.
A daidai lokacin aukuwar bala'in, Qing Fangrui tana karatu a cikin aji. Abubuwan da suka faru a wancan lokaci sun saka mata bakin ciki kwarai, sa'an nan kuma, ba ta son tun baya. Wu Xiaoxia, malamar da take koyar da Qing Fangrui tun daga ajinta na biyu zuwa na bakwai. Ya zuwa yanzu dai ta iya waiwayar abubuwan da suka faru a daidai lokacin aukuwar bala'in a waccan rana. Ta gaya mana cewa,"Girgizar kasar ta girgiza dakin karatunmu kwarai da gaske, har ma ba mu iya tsayawa ba. Wasu yara sun labe, shi ya sa ba tare da bata lokaci ba malamai suka ja su domin zuwa filin wasa. A wancan lokaci, girgizar kasar ba ta gama ba."
Qing Fangrui ta ji bakin ciki matuka a sakamakon gamuwa da girgizar kasa da kuma rasa iyayenta duka. Ta fara daina yin magana, ta rasa murna baki daya. Mutane da yawa sun nuna tausayinta kwarai bisa abubuwan da suka faru a kan wannan yarinya. Mutanen kirki sun ba ta taimako daya bayan daya domin taimaka mata jure wahala mafi tsanani a farkon lokaci na bayan aukuwar bala'in. Da zarar Qing Guangya, shugaban makarantar Guangya ya samu labarin Qing Fangrui, sai ya lashi takobin shigar da ita a cikin dakunan kwana a makarantarsa da kuma ba ta tallafi wajen gama karatu. Irin wannan alkawari ya mara wa Qing Fangrui baya sosai a zaman rayuwarta a nan gaba. Mr. Qing ya bayyana cewa,"Ba za ta iya biyan kudin karatu a makaranatar firamare, har ma zuwa jami'a ba. Sa'an nan kuma, makarantarmu za ta ba ta kudin kashewa na zaman yau da kullum. A ganina, na yi irin wannan alkawari da wuri-wuri, wannan yana da kyau matuka a gare ta."
A gaskiya, bayan da wakilanmu da suka taba tattara labaru a makarantar Guangya suka san labarin Qing Fangrui na bakin ciki, sun ba ta kyautar kudi daya bayan baya. Ban da wannan kuma, a farkon lokaci na bayan aukuwar bala'in, sun taimakawa wannan yarinya neman iyayenta ta hanyar gidan rediyonmu da internet da fatan dai yin namijin kokarin nuna mata jaje.
Ko da yake an sha yin kokari, amma a karshe dai, ba a sami iyayen Qing Fangrui ba, ba a san inda suke ba. Qing Fangrui ta zama marainiya.
Bisa ka'idojin da ma'aikatar kula da harkokin jama'a ta kasar Sin ta fitar, an ce, yaran da suka zama marayu a sakamakon bala'in girgizar kasa suna iya samun kudin alawus na yuan dari 6 daga gwamnatin kasar a ko wane wata domin ci gaba da zaman rayuwarsu. Kazalika kuma, hukumomin wuraren kasar sun ba da karin taimakon kudi. Masana'antu da mutanen kirki su ma su kan ba da tallafin kudi a kullum, ta haka yanzu matsalar kudi ba ta addabi Qing Fangrui ba.
Ko da yake wannan yarinya ba za ta damu zaman rayuwarta ba, amma ba ta iya shawo kan ciwon da ta gamu da shi a tunaninta cikin gajeren lokaci ba. A sakamakon haka ne malamanta da abokan karatunta da dangoginta suka samar mata yanayi mai karfafa zuciya, su fitar da ita daga kadaici. Madam Wu da take koyar da Qing Fangrui ta gaya mana cewa,"Ta kan yi zama da karatu tare da abokan karatunta kamar yadda 'yan uwa suke kasancewa tun daga ran Lahadi zuwa ran Jumma'a. A karshen mako kuwa, ta kan yi zama tare da abokan karatunta. A wani lokaci ma, iyayen sauran abokan karatunta su kan gayyace ta zuwa gidajensu. Wani kawunta ya kan gayyace ta zuwa wajensa sau daya a ko wane wata. Shi ya sa a wannan lokacin karatu ta fara bude zuciyarta tare da yin hira da mu."
Qing Fangrui da ta soma bude zuciyarta ta fara samun jaruntakar kaddamar da sabon zaman rayuwarta. Ta kuma fara nuna gwanintarta a fannoni daban daban. A kwanan baya, a yayin gasar rubuta makala a Turance ta duk fadin kasar Sin, wannan yarinya ta zama ta farko. Ta rubuta makala dangane da bala'in girgizar kasa da ya auku a ran 12 ga watan Mayu na shekarar 2008, inda ta ce, "Zan yi dariya, zan sami karfin zuciya, zan kara imani, zan yi dogaro da kaina."
Yanzu darussan koyon Turanci da Faransanci da yanayin kasa da kidan fiyano da dai sauransu sun cika ajandar Qing Fangrui baki daya. Tana sha'awar ko wace darasin da ake koyarwa a makaranta. Wanann yarinya da ta riga ta kawar da tsoron da bala'in girgizar kasa ya taba kawo mata, tana yin kokarinta domin cimma burinta, inda ta ce,"Burina ya hada da fannoni daban daban. Ina fatan zan iya zama wata likita, amma ina son in yi nazari kan girgizar kasa. Ina son in san lokacin aukuwar bala'in."
An labarta cewa, bala'in girgizar kasa da ya auku a lardin Sichuan a shekarar bara ya sanya yara 650 su zama marayu. Yanzu wasu 630 ko fiye daga cikinsu suna zaune a gidajen marayu ko kuma makarantu cikin farin ciki. Sun ci gaba da sabon zaman rayuwarsu kamar yadda Qing Fangrui take yi a sakamakon kulawa da hankalin da bangarori daban daban na zaman al'ummar kasar Sin suke maidawa a kanta.(Tasallah)
|