Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-05-12 16:27:52    
Dabbobi Panda sun sami sabon gidan zama bayan girgizar kasa

cri
"ina so in sami labarai kan yadda dabbobi Panda masu daraja suke a halin yanzu? Ko suna da abinci gora da suke ci? Yaya zamansu ya ke a halin yanzu?"

Nan ba da dadewa ba wani karami yaro mai suna Jiang Xixi ya yi ban kwana da dabbobi Panda guda takwas da suka kasance na tsawon watanni tara a gidan dabbobi na birnin Beijing, suna cikin dabbobi panda 63 da aka tura su daga sansanin kiwon dabbobi na Wolong zuwa wurare daban daban na kasar Sin domin renonsu bayan da aka yi girgizar kasa a ranar 12 ga watan Mayu na shekarar bara. Cikin shekara kusan daya bayan da aka yi girgizar kasa,dabbobin panda da yawa sun koma sansanin kiwo ba kakkautawa. To yaya gidajensu na zama a yanzu? Yaya lafiyarsu da kuma suke zama a wurin? Wannan muhimmin batu ne da masu sauraronmu da kuma masu kishin dabbobi panda suke so su sami labari a wannan fanni. To ga shi yau wakilanmu Wei Lijun da Liu Dongwei sun kawo mana wani labari a kan cewa " a baiwa dabbobi panda wani sabon gidan zama".

" yayin da kasa ta girgiza,dabbobin panda suna fargabar yin tafiya suna tsoro kwarai da gaske har ma sun taru gu daya. Lallai girgizar kasa ta haddasa musu samun lahani sannu a hankali."

Sansanin kiwo dabbobi Panda na Wolong mai tazara kilomita 11 daga cibiyar girgizar kasa mai digiri takwas bisa maaunin Richter da tsattsagewar kasa mai tsanani digiri 11 ya gamu da mummunan lahani,haka kuma ya kawo cikas ga dabbobi Panda. Sa'ad da Mr Zhang Hemin wanda ya fara kiwo dabbobi Panda kuma darektan cibiyar nazarin dabbobi Panda ta kasar Sin a Wolong ya waiwayo firgita da dabbobi Panda suka yi a ran 12 ga watan Mayu na bara da girgizar kasa ta wakana,hankalinsa ba a kwance ya ke ba. Ya ce wasu duwatsun da suka gangaro daga saman dutse sun danne wasu dabbobi Panda,wasu dabbobi Panda sun tsorata har ma cikin da suka yi ya zube sabo da girgizar kasa, da ka ga mawuyancin hali da dabbobi Panda ke ciki,lalle za ka yi bakin ciki sosai. A cikin kusan shekara daya da ta gabata,suna kiwon dabbobi Panda tare da kauna har ma sun sami nasarori.

" Muna kiwo dabbobi Panda tare da kauna,mu kan shafa jikinsu da kusantar su ,da yin magana da su,bai kamata mu tsaya matsayin sama wajen kula da su ba,wani lokaci muna yin mu'amala da su ta yin rarrafe, bayan da muka yi kokari na tsawon kusan shekara daya,dabbobi panda sun koma zamansu kamar yadda suka yi a da kafin girgizar kasa."

Kwanakin baya wakilan gidan rediyo na kasar Sin sun kai ziyara a sansanin nazarin hayyafar dabbobi Panda dake a birnin Chengdu mai tazara kilomita sama da dari daga Wolong inda dabbobi Panda suka fi yawa a kasar Sin,bishiyoyin gora masu launin kore suna jejjere bisa layi,wasu dabbobi Panda suna wasa a kan katako da aka gitta musamman dominsu,suna da kamani mai ban sha'awa. Wani Baamurke mai suna Washington wanda ya zo daga birnin Seattle na kasar Amurka da ya ga wani Panda na cin gora,ya yi farin ciki da cewa

" a ganina Panda na da ban sha'awa. Wannan karo ne na farko da na ga Panda, musamman yayin da na ga karamin Panda yadda yake wasa a harabarsu. Fasalin gidan dabbobi Panda na da kyan gani sosai, ban taba ganin yawan gorar da aka tanada kamar a wannan wurin ba,dabbobi Panda suna wasa yadda suka ga dama."

Mai kiwon panda Mr Lao Tan da wani dalibin kasar Japan mai aikin sa kai suna nan suna shirya abinci mai dadi domin dabbobi Panda. Mr Lao Tan ya bayyana cewa bayan da girgizar kasa ta faru, an kawo dabbobi Panda guda hudu daga Wolong zuwa wannan sansanin domin renonsu, ga shi yanzu kusan babu bambanci tsakanin dabbobin Panda da ake da su a da da wadanda aka kawo. Kan batun wadanan dabbobi Panda, Mr Lao Tan ya yi bayani kamar ya ba da labari dangane da 'ya'yansa. Ya ce

" idan ka nuna wa Panda kirki,panda za ta nuna biyayya gareka. Idan panda ta nuna biyayya gare ka,za ka ji dadi. Idan panda ta hadu da rashin lafiya,na kan sanar da likitoci na dabbobi,su kan zo cikin lokaci domin yi mata jinya.duk da haka wani lokaci ma na kan kasa hakuri."

Girgizar kasa da ta wakana a yankin Wenchuan ta haddasa mummunan lahani ga sansanin kiwon dabbobi Panda na Wolong inda dabbobin Panda ke rayuwa, an lalata sama da kashi sabain bisa kashi dari na wuraren da dabbobi panda ke zaune,musamman dabbobi Panda da ke zama a wurare masu gora tsakanin tsayin mita dubu biyu zuwa dubu biyu da dari biyar daga bisa teku,wani lokaci ma dabbobi Panda su kan fuskanci barazanar rashin abinci. Sansanin nazarin hayayyafar dabbobi Panda na birnin Chengdu ya ba da tallafin agaji,ya samar musu da abinci. Darektan sansanin nazarin hayayyafar dabbobi panda na birnin Chengdu Mr Zhang Hemin ya bayyana cewa

"da akwai fili mai kadada sama da dari a sansaninmu inda aka dasa bishiyoyin gora,wannan abinci ne da muka tanada domin magance bala'i. idan bala'in ya zo ba zata, mun bayar da gorar da muke dasawa a wannan fili domin ceton dabbobi Panda da muke kiwo."

Ga shi a yau, mun tsungunar da dabbobi Panda da aka kawo daga Wolong yadda ya kamata,amma sake gina wurin ba da kariyar halitattu na Wolong ta yadda dabbobi Panda za su koma wuraren zamansu na da sun kasance babban burinmu ne, Mr Zhang Hemin,darektan cibiyar nazarin hayayyafar dabbobi Panda na kasar Sin ya fadi haka

" mun gaggauta gina dakunan wucin gadi domin dabbobi Panda,haka kuma mun shimfida ayyukan wucin gadi da dama ta yadda su za su iya kwana yadda ya kamata. Wolong wuri ne na asalin zaman dabbobi Panda,suna iya zaman jin dadi a wannan wurin."

Sabon gida na cibiyar nazarin hayayyafar dabbobi Panda na kasar Sin yana wurin Huang Caopin na yankin Genda mai tazarar kilomita 10 daga gidansu na da. Yayin da aka tsara fasalin sabon gidan dabbobi Panda,an yi la'akari da abubuwa da dama ciki har da tsaro,halayen zama na panda, sabon ginin yana wani fili mai fadi dake cikin kyakkyawan muhalli da kuma yanayi mai dadi da saukin samun ruwa, an zubar da kudin Sin Yuan biliyan daya da miliyan dari huku,za a fara aikin sake gina gidan dabbobi panda daga watan Yuli na wannan shekara da muke ciki.

Bisa labarin da aka samu, an ce aikin sake gina gidan dabbobin panda ya samu cikakken goyon baya daga mutane da kungiyoyi masu abuta da kasar Sin na bangarori daban daban na duniya. A jikin wata takardar ba da taimako daga cibiyar nazarin hayayyafar dabbobi Panda ta birnin Chengdu an rubuta kudin Sin Renminbi Yuan miliyan 12 da gwamnatoci da kungiyoyi da ba na gwamnati ba da kamfanoni na kasa da kasa suka bayar. Wannan ya karfafa kwarin gwiwar Mr Zhang Hemin na sake gina sabon gidan dabbobi Panda.

" gwamnatin yankin mulki na musamman na Hongkong ta mika hannunta na ba da taimako,mun yi farin ciki da ganin haka,wannan ya karfafa gwiwarmu, za mu gaggauta kammala aikin sake gina sabon gidan cikin gajeren lokaci."

Mr Zhang Hemin ya ce yana fatan a maido horaswar dabbobi Pandan da aka hayayyafa ta hanyar taimakon dan Adam a fili mai fadi da bar su zauna a dausayin da aka killace su saboda girgizar kasa da ta faru, wannan zai amfana wajen warware matsalolin da ake fama da su kan dabbobi panda da aka samu ta taimakon dan Adam, ta yadda dabbobi panda na iya girma kamar yadda suka yi a waje. Domin kammala wadannan ayyukan cikin shekaru biyu ko uku cikin nasara, ana nan ana gaggauta daddasa bishiyoyi da ciyayi a wuraren da ake bukata. Ya ci gaba da bayyana da cewa hayayyafar dabbobi panda ba aiki ne mai sauki ba daga wurare marasa tsayi zuwa wurare masu tsayi. Dalili kuwa shi ne gora ta sha bamban da juna a wurare masu tsayi da marasa tsayi, bayan da dabbobi panda suka yi barbara a watan Maris ko watan Afrila na kowace shekara,dabbobi panda mata su kan yi kaura daga wurare marasa tsayi zuwa wuarare masu tsayi suna neman abinci domin tanadar abinci har zuwa watan Augusta ko September bayan da suka haifar da jariransu. Domin kare wuraren zama na dabbobi Panda da wurarensu na hayayyafa, ya bayyana cewa ana nan ana shirin kauratar da gidajen manoma sama da 870 daga yankin ba da kariya zuwa wani kwarin tuddai za a tsungunar da su yadda ya kamata. Zhang Hemin ya ce

"kamata ya yi mu gaggauta kammala wannan aiki,mun tsungunar da manoma, mun samo filaye a kan tuddai, mun noma bishiyoyin gora,mun samar da wani gidan tsugunar da dabbobi panda ta yadda za su iya zama cikin lumana da hayayyafa a ciki. Wannan aikinmu ne na gaggawa,za mu kaddamar da wannan aiki cikin sauri,kuma za mu yi kokarin kammala shi cikin shekaru biyu ko uku masu zuwa."